Annabcin Uba a kan Babila
Daular da ta kwashe Yahuda ita kanta an yanke mata hukunci: an kunyata Bel, an rushe garunta, an bar ƙasar ga diloli. A halin yanzu Isra'ila da Yahuda suna dawowa suna kuka, suna tambayar hanyar zuwa Sihiyona da wurin Ubansu, an nemi laifinsu ba a same shi ba, Mai Fansarsu kuwa mai ƙarfi ne.
50 1Maganar da Ubanmu ya yi game da Babila, ƙasar Babiloniyawa, ta wurin annabi Irmiya:
2Ku yi shela a cikin al'ummai, ku kuma sanar da shi; ku ɗaga tuta, ku sanar da shi; kada ku ɓoye kome. Ku ce, An kama Babila; Bel ya sha kunya, Marduk ya ragargaje. Siffofinta sun sha kunya, an farfashe gumakanta. a a v2 Bel da Marduk manyan allolin Babila ne. 3Gama wata al'umma daga arewa tana auka mata; za ta mai da ƙasarta kango, ba kuma wanda zai zauna a cikinta. Mutane da dabbobi duk sun gudu; sun tafi.
4A kwanakin nan da kuma a lokacin nan, in ji Ubanmu, 'ya'yan Isra'ila za su zo, su da 'ya'yan Yahuda tare; za su yi tafiya suna kuka, su kuma nemi Ubansu. 5Za su tambayi hanyar zuwa Sihiyona, fuskokinsu sun koma wajenta, suna cewa, “Ku zo, mu haɗa kanmu da Ubanmu cikin madawwamin alkawari wanda ba za a taɓa mantawa da shi ba.” 6Mutanena sun zama ɓatattun tumaki; makiyayansu sun ɓatar da su, suka sake su a kan duwatsu. Sun yi ta yawo daga dutse zuwa tudu; sun manta da wurin hutunsu. 7Duk waɗanda suka same su sun cinye su, maƙiyansu kuma suka ce, “Ba mu da laifi, domin sun yi wa Ubangiji zunubi, wato makiyayarsu ta gaskiya, Ubangiji, begen kakanninsu.” 8Ku gudu daga cikin Babila; ku fita daga ƙasar Babiloniyawa, ku zama kamar bunsurai masu jagorancin garke. 9Gama ga shi, ina tada ina kuma kawo wa Babila ƙungiyar manyan al'ummai daga ƙasar arewa. Za su yi sahu gāba da ita, daga can kuma za a kama ta. Kibiyoyinsu suna kama da na ƙwararren jarumi wanda ba ya komawa hannu wofi. 10Za a washe Babiloniya; duk masu washe ta za su ƙoshi, in ji Ubanmu.
11Saboda kuna murna, saboda kuna shagali, ku masu washe gādona, saboda kuna tsalle kamar karsana mai sussukar hatsi, kuna kuma haniniya kamar ingarmu, 12mahaifiyarku za ta sha kunya ƙwarai; wadda ta haife ku za ta ji kunya. Ga shi, za ta zama ta ƙarshe cikin al'ummai — jeji, busasshiyar ƙasa, da hamada. 13Saboda fushin Ubanmu ba za a zauna a cikinta ba; za ta zama kango sarai. Duk mai wucewa ta Babila zai firgita, zai kuma yi tsaki saboda dukan raunukanta. 14Ku ja dāgā gāba da Babila daga kowane gefe, dukanku masu harbin baka. Ku harbe ta; kada ku yi rowar kibiyoyi, gama ta yi wa Ubanmu zunubi. 15Ku yi ihu gāba da ita daga kowane gefe; ta miƙa wuya. Hasumiyoyinta sun faɗi; an rushe garunta. Tun da yake wannan ramuwar Ubanmu ne, ku rama mata; ku yi mata kamar yadda ta yi. 16Ku datse mai shuki da mai girbi daga Babila. A gaban takobin azzalumi kowa zai juyo zuwa ga mutanensa, kowa kuma zai gudu zuwa ƙasarsa.
17Isra'ila garke ne da ya warwatse, wanda zakoki suka kora. Da farko sarkin Assuriya ya cinye shi, yanzu kuma a ƙarshe Nebukadnezzar sarkin Babila ya tauna ƙasusuwansa.
18Ga abin da Uban rundunonin Sama, Ubanmu na Isra'ila, yake cewa, Zan hukunta sarkin Babila da ƙasarsa yadda na hukunta sarkin Assuriya. 19Zan dawo da Isra'ila zuwa wurin kiwonsa, zai kuma yi kiwo a Karmel da Bashan; a kan tuddan Ifra'im da Gileyad ransa zai ƙoshi. 20A waɗancan kwanaki da a wannan lokaci, in ji Ubanmu, za a nemi laifin Isra'ila amma babu; za a nemi zunuban Yahuda amma ba za a same su ba, gama zan gafarta wa raguwar da zan bar da rai.
21Ku haura ku yaƙi ƙasar Meratayim, da waɗanda suke zama a Fekod. Ku kashe su ku hallaka su ƙaƙaf, in ji Ubanmu; ku yi duk abin da na umarce ku. 22Akwai amon yaƙi a ƙasar, da hallaka mai girma. 23Yadda aka datse guduma ta dukan duniya aka kuma karya ta! Yadda Babila ta zama abin tsoro a cikin al'ummai! 24Na kafa miki tarko, ya Babila, aka kuma kama ki kafin ki sani. An same ki aka kama ki domin kin yi gāba da Ubanmu.
25Ubanmu ya buɗe ma'ajin makamansa ya fitar da makaman fushinsa, gama Uban rundunonin Sama yana da aiki da zai yi a ƙasar Babiliyawa. 26Ku zo ku yaƙe ta daga kowane gefe; ku buɗe rumbunanta; ku tsibe ta kamar tsibin hatsi. Ku hallaka ta ƙaƙaf; kada a bar mata kome. 27Ku kashe dukan 'yan bijiminta; bari su gangara zuwa mayanka. Kaitonsu, gama ranarsu ta zo, lokacin hukuncinsu. 28Ku ji—waɗanda suka tsere da masu neman mafaka daga ƙasar Babila, suna zuwa Sihiyona domin su yi shelar adalcin Ubanmu, adalcinsa saboda haikalinsa. 29Ku kira maharba su yaƙi Babila, dukan masu tanƙwara baka. Ku kafa sansani kewaye da ita a kowane gefe; kada wani ya tsere. Ku sāka mata gwargwadon ayyukanta; ku yi mata duk abin da ta aikata. Gama ta yi girman kai a kan Ubanmu, a kan Mai Tsarki na Isra'ila.
30Saboda haka samarinta za su fāɗi a titunanta, dukan sojojinta kuma za a yi musu shiru a wannan rana, in ji Ubanmu. 31Ga shi, ina gāba da kai, kai mai girman kai, in ji Uban rundunonin Sama, gama ranarka ta zo, lokacin da zan hukunta ka. 32Mai girman kai zai yi tuntuɓe ya fāɗi, babu wanda zai tā da shi. Zan hura wuta a cikin biranensa, za ta kuwa cinye duk abin da yake kewaye da shi. 33Ga abin da Uba na rundunonin Sama ya ce: An danne 'ya'yan Isra'ila, da 'ya'yan Yahuda tare da su. Duk waɗanda suka kama su suna riƙe da su kam; sun ƙi su saki su.
34Mai Fansarsu yana da ƙarfi; Uba na rundunonin Sama shi ne sunansa. Lalle zai kāre ƙararsu, domin yă kawo hutu ga duniya amma tashin hankali ga mazaunan Babila.
35Takobi a kan Babiloniyawa, in ji Ubanmu, da a kan mazaunan Babila, da a kan shugabanninta da masu hikimarta! 36Takobi a kan annabawan ƙarya, za su kuma zama wawaye! Takobi a kan jarumanta, za su kuma farfashe! 37Takobi a kan dawakanta da karusanta, da a kan dukan baƙin sojojin da ke cikinta, za su kuma zama kamar mata! Takobi a kan dukiyoyinta, za a kuma washe su! 38Fari a kan ruwanta, za su kuma ƙafe! Gama ƙasa ce ta gumaka, suna kuma hauka a kan gumakansu masu ban tsoro. 39Saboda haka namun jeji da kuraye za su zauna a can, jiminai kuma za su yi zama a cikinta. Ba za a ƙara zama a cikinta ba, ba kuwa za a yi zama a cikinta ba dukan zamanai. 40Kamar lokacin da Ubanmu ya birkice Saɗom da Gwamora da garuruwan maƙwabtansu, in ji Ubanmu, saboda haka ba wanda zai zauna a can; ba wani mutum da zai zauna a cikinta. 41Ga shi, mayaƙa suna zuwa daga arewa; babbar al'umma da sarakuna masu yawa suna tashi daga iyakar duniya. 42Suna riƙe da baka da māshi; mugaye ne, ba sa jin ƙai. Ƙararsu na ruri kamar teku suna hawan dawakai, a shirye kamar mutum domin yaƙi da ke, Diyar Babila. 43Sarkin Babila ya ji labarinsu, hannuwansa kuma suka raunana. Azaba ta kama shi, zafi kamar na mace mai naƙuda. 44Ga shi, kamar zaki mai hawowa daga kurmin Urdun zuwa makiyaya mai kyau, nan take zan kori Babila daga ƙasarta, zan kuma naɗa a kanta duk wanda na zaɓa. Gama wane ne kamar ni? Wa zai kira ni? Wane makiyayi zai iya tsayawa a gabana?
45Saboda haka ku ji shirin da Ubanmu ya yi a kan Babila da nufe-nufen da ya ƙulla a kan ƙasar Babiloniyawa: Lalle za a ja ƙananan garkensu; lalle makiyayarsu za ta razana saboda ƙaddararsu. 46Da jin ƙarar kamuwar Babila duniya za ta girgiza, kukanta kuma za a ji shi a cikin al'ummai.