Ben-Hadad ya Kewaye Samariya
Ben-Hadad ya nemi azurfar Ahab, da matansa, da 'ya'yansa, Isra'ila kuma ta fatattake shi sau biyu kamar yadda Ubanmu ya yi alkawari ta bakin wani annabi. Amma Ahab ya kira sarkin da aka ci ɗan'uwansa ya kuma sake shi, wani annabi a ɓoye kuma ya kama Ahab har ya yanke wa kansa hukunci.
20 1Ben-Hadad sarkin Aram ya tara dukan sojojinsa — sarakuna talatin da biyu suna tare da shi, da dawakai da kekunan yaƙi. Ya haura, ya kewaye Samariya, ya kuma kai mata hari. 2Ya aiki manzanni cikin birnin wurin Ahab sarkin Isra'ila, yana cewa, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce: 3‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne, haka ma zaɓaɓɓun matanka da 'ya'yanka nawa ne.’”
4Sarkin Isra'ila ya amsa ya ce, “Kamar yadda ka faɗa, ubangijina sarki: ni naka ne, da dukan abin da nake da shi.”
5Manzannin suka komo suka ce, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce: ‘Na aika maka da saƙo ina neman azurfarka da zinariyarka, da matanka da 'ya'yanka. 6Amma wajen wannan lokaci gobe zan aiki bayina su bincika fadarka da gidajen barorinka, za su kuma kwashe duk abin da yake da daraja a wurinka.’”
7Sarkin Isra'ila ya kirawo dukan dattawan ƙasar ya ce, “Ku lura sosai mutumin nan yana neman faɗa ne. Ya aika yana neman matana, da 'ya'yana, da azurfata, da zinariyata, ban kuwa hana shi ba.”
8Dukan dattawa da dukan jama'a suka ce masa, “Kada ka saurare shi, kada kuma ka yarda masa.”
9Sai ya ce wa manzannin Ben-Hadad, “Ku gaya wa ubangijina sarki, ‘Duk abin da ka fara nema daga bawanka zan yi, amma wannan abin da kake nema ba zan iya ba.’” Manzannin suka tafi suka kai masa amsarsa.
10Sai Ben-Hadad ya aika saƙo ya ce, “Bari alloli su hukunta ni munin hukunci, in har ƙurar Samariya za ta ishi kowane mai bina ya ɗauki tafin hannu guda.”
11Sarkin Isra'ila ya amsa ya ce, “Ku gaya masa, ‘Kada mai ɗaura kayan yaƙi yă yi fahariya kamar wanda ya tuɓe su.’”
12Yayinda Ben-Hadad da sarakunan suke shan giya a tentunansu, sai ya ji wannan, ya umarci mutanensa ya ce, “Ku kama matsayanku.” Sai suka kama matsayansu gāba da birnin.
Uba ya Ba Ahab Nasara
13Sai wani annabi ya zo wurin Ahab sarkin Isra'ila ya ce, “Ga abin da Ubanmu ya ce: Ka ga wannan babban rundunar soja? Yau zan bashe ta a hannunka, za ka kuwa sani ni ne Ubanka.”
14Ahab ya ce, “Ta wurin wa?” Annabin ya amsa ya ce, “Ga abin da Ubanmu ya ce: Ta wurin matasan hafsoshin shugabannin lardunan ne.” Ahab ya ce, “Wa zai fara yaƙin?” Ya ce, “Kai za ka fara.”
15Sai Ahab ya tara matasan hafsoshin shugabannin lardunan — mutum 232. Sa'an nan ya tara sauran, dukan Isra'ilawa — jimla 7,000. 16Suka fita da tsakar rana, yayinda Ben-Hadad da sarakuna talatin da biyu ƙawayensa suke ta shan giya suka bugu a tentunansu. 17Matasan hafsoshin shugabannin lardunan ne suka fara fita. Ben-Hadad ya riga ya aiki 'yan leƙen asiri, suka kawo masa labari suka ce, “Ga mutane suna fitowa daga Samariya.”
18Ya ce, “In sun fito don salama, ku kama su da rai; in kuma sun fito don yaƙi, ku kama su da rai.”
19Matasan hafsoshin shugabannin lardunan suka fito daga birnin, rundunar soja kuma na binsu daga baya. 20Kowane mutum ya kashe abokin gābansa. Arameyawa suka gudu, Isra'ila kuma na runtuminsu, amma Ben-Hadad sarkin Aram ya tsere a kan doki tare da waɗansu mahaya dawakai. 21Sarkin Isra'ila ya nausa gaba ya ƙwace dawakai da kekunan yaƙi, ya kuma kashe Arameyawa da yawa ƙwarai. 22Daga baya annabin ya zo wurin sarkin Isra'ila ya ce, “Ka ƙarfafa matsayinka, ka kuma yi tunani sosai a kan abin da ya kamata ka yi, gama bazara mai zuwa sarkin Aram zai sāke kai maka hari.”
23A halin yanzu fadawan sarkin Aram suka ce masa, “Allolinsu alloli ne na duwatsu, shi ya sa suka ci mu da yaƙi. Mu yaƙe su a fili, lalle za mu rinjaye su. 24Ka yi haka: ka cire dukan sarakunan daga matsayinsu na shugabanci, ka sa waɗansu hafsoshi a maimakonsu. 25Ka tara runduna kamar wadda ka rasa — doki a bakin doki, keken yaƙi a bakin keken yaƙi — ka yaƙi Isra'ila a fili. Sa'an nan lalle za mu fi su ƙarfi.” Ya saurare su, ya kuma yi haka.
26Bazara mai zuwa Ben-Hadad ya tara Arameyawa, ya haura zuwa Afek domin yă yaƙi Isra'ila. 27Da aka tara Isra'ilawa aka kuma ba su kayan yaƙi, sai suka fita don su gamu da su. Isra'ila suka kafa sansani gāba da su kamar ƙananan garkunan awaki biyu, Arameyawa kuwa suka cika ƙasar.
28Mutumin Allah ya zo wurin sarkin Isra'ila ya ce, “Ga abin da Ubanmu ya ce: Tun da yake Arameyawa suna tsammani Ubangiji allah ne na tuddai, ba na kwaruruka ba, zan bashe wannan dukan babban runduna a hannunka, za ka kuwa sani ni ne Ubanka.”
29Kwana bakwai suka kafa sansani gāba da juna; a rana ta bakwai kuwa yaƙin ya ɓarke. A rana guda Isra'ilawa suka karkashe sojojin ƙasa na Arameyawa dubu ɗari. 30Sauran suka gudu zuwa cikin Afek, inda katangar ta fāɗo a kan mutum dubu ashirin da bakwai daga cikinsu. Ben-Hadad kuwa ya gudu zuwa cikin birnin, ya ɓoye a cikin wani ɗaki na ciki.
31Barorinsa suka ce masa, “Mun ji cewa sarakunan gidan sarautar Isra'ila masu jinƙai ne. Bari mu tafi wurin sarkin Isra'ila da rigunan makoki kewaye da gindayenmu, da igiyoyi a kawunanmu; wataƙila zai bar ka da ranka.”
32Sai suka naɗe tsummoki kewaye da gindayensu, suka sa igiyoyi a kawunansu, suka zo wurin sarkin Isra'ila, suka roƙa suka ce, “Bawanka Ben-Hadad ya ce, ‘Ina roƙo, ka bar ni da rai.’” Ya amsa ya ce, “Yana da rai har yanzu? Ɗan'uwana ne.”
33Mutanen suka ɗauki wannan a matsayin alama mai kyau, suka yi saurin kama maganarsa. Suka ce, “I, ɗan'uwanka Ben-Hadad!” Sarkin ya ce, “Ku tafi, ku kawo shi.” Sai Ben-Hadad ya fito, Ahab kuwa ya sa shi ya hau keken yaƙi.
34“Zan mayar da biranen da mahaifina ya ƙwace daga mahaifinka,” Ben-Hadad ya ce, “za ka kuma kafa wuraren kasuwancinka a Dimashƙu, yadda mahaifina ya yi a Samariya.” Ahab ya ce, “A kan waɗannan sharuɗɗa zan sake ka.” Sai ya ƙulla yarjejeniya da shi, ya kuma sake shi.
Wani Annabi ya Fuskanci Sarki
35Bisa ga maganar Ubanmu sai wani daga cikin 'ya'yan annabawa ya ce wa abokinsa, “Ina roƙonka, ka buge ni.” Amma mutumin ya ƙi ya buge shi.
36Annabin ya ce, “Tun da yake ba ka yi biyayya ga muryar Ubanmu ba, da zarar ka rabu da ni zaki zai kashe ka.” Da mutumin ya tafi, sai zaki ya same shi ya kashe shi.
37Annabin ya sami wani mutum ya ce, “Ina roƙonka, ka buge ni.” Sai mutumin ya buge shi ya kuma ji masa rauni.
38Sa'an nan annabin ya tsaya a bakin hanya yana jiran sarki, ya ɓad da kamanninsa da ɗaure ido da bandeji. 39Sa'ad da sarki yake wucewa, sai annabin ya tā da murya ya ce, “Bawanka ya shiga tsakiyar yaƙi, sai ga wani mutum ya ratse, ya kawo mini wani ɗan kama, ya ce, ‘Ka tsare mutumin nan. In ya ɓace, ranka a bakin ransa ne, ko kuwa ka biya azurfa mai nauyin fam saba'in da biyar.’ 40Yayinda bawanka yake shagaltu a nan da can, sai mutumin ya ɓace.” Sarkin Isra'ila ya ce, “Hukuncinka ke nan; kai da kanka ka yanke shi.”
41Nan da nan annabin ya cire bandeji daga idanunsa, sai sarkin Isra'ila ya gane shi ɗaya ne daga cikin annabawa.
42Ya ce wa sarki, “Ga abin da Ubanmu ya ce: Tun da yake ka saki mutumin da na ware domin hallaka, ranka zai zama a bakin ransa, mutanenka kuma a bakin mutanensa.”
43Da fushi da ɓacin rai, sarkin Isra'ila ya kama hanyarsa zuwa gida, ya komo Samariya.