Ku Fasa Ƙasar da ba a Nome ba
An busa ƙaho: runduna tana saukowa daga arewa, an kuma faɗa wa Yahuza su gudu zuwa birane masu garu. Irmiya ya ga ƙasar ta koma kufai marar siffa, ya kasa daina rawar jiki. Hukunci gaskiya ne, amma Uba ya ce halakar ba za ta zama cikakkiya ba.
4 1“Idan za ki komo, ya Isra'ila,” in ji Ubanmu, “to, ki komo wurina. Idan kin kawar da abubuwanki na ƙyama daga gabana, in kuwa ba ki yi kaɗawa ba, 2in kuma kika rantse, ‘Muddin Ubanmu yana a raye,’ cikin gaskiya, da adalci, da aikin adalci, to, al'ummai za su sami albarka ta wurinsa, a cikinsa kuma za su yi fahariya.”
3Gama ga abin da Ubanmu yake faɗa wa mutanen Yahuda da na Urushalima, Ku fasa ƙasarku da ba a nome ba, kada kuwa ku yi shuka a cikin ƙayayyuwa. 4Ku yi wa kanku kaciya ga Ubanmu, ku cire loɓar zukatanku, ku mutanen Yahuda da mazaunan Urushalima, in ba haka ba fushina zai ɓarke kamar wuta ya kuma yi ta ci ba mai iya kashe shi ba, saboda muguntar ayyukanku.
Masifa Tana Zuwa daga Arewa
5“Ku yi shela a Yahuda, ku yaɗa labari a Urushalima, ku ce, ‘Ku busa ƙaho ko'ina a ƙasar!’ Ku yi ihu ku ce, ‘Ku tattaru, mu kuwa gudu zuwa birane masu katanga!’ 6Ku ɗaga tuta wajen Sihiyona! Ku gudu domin tsira, kada ku yi jinkiri! Gama ina kawo masifa daga arewa, hallaka mai girma.”
7Zaki ya fito daga kurminsa, mai hallaka al'ummai yana kan tafiya. Ya bar wurinsa domin yă mai da ƙasarki kango; biranenki za su rushe su zama kufai, babu kuma wani da ya rage yana zama a cikinsu. 8Saboda haka ku sa tufafin makoki, ku yi kuka da baƙin ciki, gama zafin fushin Ubanmu bai juya daga gare mu ba.
9“A ranan nan,” in ji Ubanmu, “sarki da fadawansa za su karaya; firistoci za su firgita, annabawa kuma za su yi mamaki.”
10Sai na ce, “Kash, ya Uba Mabuwayi! Lalle ka yaudari wannan jama'a da Urushalima ƙwarai, wai, ‘Za ku sami salama,’ alhali kuwa takobi ya kai ga maƙogwaronmu.”
11“A lokacin, za a gaya wa wannan jama'a da Urushalima, Iska mai zafi daga tuddan hamada wofi tana busawa wajen 'yar mutanena, ba domin shiƙa ba, ba kuma domin tankaɗewa ba. 12Iska mai ƙarfi fiye da haka za ta zo bisa umarnina. Yanzu kuwa zan furta hukuncina a kansu.”
13Duba! Abokin gāba yana zuwa kamar gizagizai, kekunan yaƙinsa kamar guguwa; dawakansa sun fi gaggafa sauri. Kaitonmu—mun hallaka! 14Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki, domin ki sami ceto. Har yaushe mugayen tunaninki za su kasance a cikinki? 15Gama wata murya tana yin shela daga Dan, tana sanar da masifa daga tuddan Ifraimu.
16Ku gargaɗi al'ummai, ku sanar wa Urushalima, “Masu kewaye suna zuwa daga ƙasa mai nisa; suna tā da ihun yaƙi a kan biranen Yahuda. 17Suna kewaye da ita kamar masu gadin gona, domin ta yi mini tawaye,” in ji Ubanmu. 18Hanyoyinki da ayyukanki sun jawo wannan a kan ki. Wannan ce masifarki, kaico da ɗaci yake, domin ya soka har zuciyarki.
Annabi Ya Yi Kuka domin Mutanensa
19Azabata, azabata! Ina murɗewa cikin zafi. Kaico, bangwayen zuciyata! Zuciyata tana bugawa a cikina; ba zan iya yin shiru ba, gama na ji karar ƙaho, da kiran yaƙi. 20Ana shelar masifa bisa masifa, gama an mayar da dukan ƙasar kango. Nan take an rushe tentunana, labulen tentina cikin ƙyiftawar ido. 21Har yaushe zan dinga ganin tutar yaƙi in kuma dinga jin karar ƙaho?
22“Gama mutanena wawaye ne; ba su san ni ba. Yara marasa azanci ne, ba su da fahimta. Gwanaye ne a yin mugunta, amma ba su san yadda za su aikata nagarta ba.”
23Na dubi duniya, ga ta kuwa ba siffa babu kome; na dubi sammai kuma, haskensu kuwa ya ƙare. 24Na dubi duwatsu, ga su kuwa suna girgiza; dukan tuddai suna lilo. 25Na duba, ga shi babu kowa ko kaɗan; dukan tsuntsayen sama kuwa sun gudu. 26Na duba, ga shi ƙasa mai albarka ta zama hamada; dukan biranenta kufai suke a gaban Ubanmu, a gaban zafin fushinsa.
27Gama ga abin da Ubanmu yake cewa, Dukan ƙasar za ta zama kango, duk da haka ba zan hallaka ta ƙaƙaf ba. 28Saboda wannan duniya za ta yi makoki sammai kuma a bisa za su yi duhu, gama na faɗa, na kuduri niyya; ba zan sassauta ba, ba kuwa zan janye ba.
29Da jin ƙarar mahaya dawakai da maharba kowane birni yana gudu. Suna gudu su shiga kurmi suna kuma hawa cikin duwatsu; an yashe kowane birni, babu kuma kowa da yake zama a cikinsu. 30Ke kuwa, wadda aka hallaka, me kike yi, kina sa jar tufa, kina yin ado da kayan zinariya, kina shafa kwalli a idanunki? A banza kike ƙawata kanki. Masoyanki sun rena ki; suna neman su kashe ki. 31Gama na ji kuka kamar na mace mai naƙuda, azaba kamar ta mace mai haihuwar ɗan fari—kukan 'yar Sihiyona, tana shaƙar numfashi, tana miƙa hannuwanta, “Kaitona! Ina mutuwa a gaban masu kisa.” a a v31 'Yar Sihiyona' wani suna ne na waƙa domin Urushalima.