Li'azaru na Betani
Yesu ya jira kwana biyu, ya iso a makare da kwana huɗu, ya kuma yi kuka a kabarin abokinsa. Ya gaya wa Marta cewa shi ne tashin matattu da rai, ya gode wa Ubansa a fili saboda ya ji shi, ya kuma kira Li'azaru ya fito. A sa'an nan ne majalisa ta yanke shawarar kashe shi.
11 1Wani mutum mai suna Li'azaru yana fama da rashin lafiya, mutumin Betani ne, ƙauyen Maryamu da 'yar'uwarta Marta. 2Maryamu — wadda ɗan'uwanta Li'azaru yake fama da rashin lafiya — ita ce ta shafa wa Ubangiji turare mai ƙamshi, ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta. 3Sai 'yan'uwan mata suka aika masa saƙo, suna cewa, “Ubangiji, wanda kake ƙauna yana fama da rashin lafiya.”
4Da Yesu ya ji haka, sai ya ce, “Wannan ciwo ba zai ƙare da mutuwa ba, sai dai domin ɗaukakar Ubanmu ne, domin a ɗaukaka Ɗan Ubanmu ta wurinsa.”
5Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da 'yar'uwarta da Li'azaru. 6Saboda haka da ya ji Li'azaru yana fama da rashin lafiya, sai ya ƙara kwana biyu a inda yake.
7Sa'an nan bayan haka ya ce wa almajiran, “Mu koma Yahudiya.”
8Almajiran suka ce masa, “Mallam, ba jima ba Yahudawa suka yi ƙoƙarin su jajjefe ka da duwatsu, yanzu kuma za ka sāke komawa can?”
9Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa'o'i goma sha biyu ne a rana ba? Duk wanda yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba, domin yana ganin hasken wannan duniya. 10Amma in wani yana tafiya da dare, sai ya yi tuntuɓe, domin babu haske a cikinsa.” 11Bayan haka, ya ce musu, “Abokinmu Li'azaru ya yi barci, amma zan je in tashe shi.”
12Sai almajiran suka ce masa, “Ubangiji, in barci ya yi, to, zai sami sauƙi.” 13Yesu dai yana magana ne a kan mutuwarsa, amma su suna tsammani barci na hutawa yake nufi.
14Saboda haka sai Yesu ya gaya musu a fili, “Li'azaru ya mutu, 15ina kuma murna saboda ku da ban kasance a can ba, domin ku gaskata. Amma mu je wurinsa.”
16Sai Toma, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ya ce wa sauran almajiran, “Mu ma mu je, mu mutu tare da shi.”
17Saboda haka da Yesu ya iso, sai ya tarar Li'azaru ya riga ya yi kwana huɗu a kabari. 18Betani kuwa tana kusa da Urushalima, wajen mil biyu, a a v18 Istadiya goma sha biyar wajen mil biyu ne (kusan kilomita uku). 19Yahudawa da yawa kuwa suka zo wurin Marta da Maryamu domin su yi musu ta'aziyya a kan ɗan'uwansu. 20Da Marta ta ji Yesu yana zuwa, sai ta fito ta tarye shi, amma Maryamu ta zauna a gida. 21Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan, da ɗan'uwana bai mutu ba. 22Amma har yanzu ma na san duk abin da ka roƙi Ubanmu, zai ba ka.”
23Yesu ya ce mata, “Ɗan'uwanki zai tashi.”
24Marta ta ce masa, “Na san zai tashi a tashin matattu a rana ta ƙarshe.”
25Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko da ya mutu, 26kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata da wannan?”
27Ta ce masa, “I, Ubangiji; na gaskata kai ne Almasihu, Ɗan Ubanmu, wanda yake zuwa duniya.”
28Bayan ta faɗi haka, sai ta tafi ta kira 'yar'uwarta Maryamu a asirce, ta ce, “Mallam ya zo, yana kuma kiranki.” 29Da Maryamu ta ji haka, sai ta tashi da sauri ta tafi wurinsa. 30Yesu bai riga ya shiga ƙauyen ba tukuna, yana nan inda Marta ta tarye shi. 31Yahudawan da suke tare da ita a gida, suna yi mata ta'aziyya, da suka ga Maryamu ta tashi da sauri ta fita, sai suka bi ta, suna tsammani za ta kabari ne domin ta yi kuka a can. 32Da Maryamu ta zo wurin Yesu, ta gan shi, sai ta fāɗi a ƙafafunsa, ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗan'uwana bai mutu ba.”
33Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita kuma suna kuka, sai ya yi nishi a ruhunsa, ya kuma damu ƙwarai.
34Ya ce, “Ina kuka kwantar da shi?” Suka ce masa, “Ubangiji, zo ka gani.”
35Yesu ya yi kuka.
36Sai Yahudawa suka ce, “Ku dubi yadda yake ƙaunarsa!” 37Amma waɗansunsu suka ce, “Wannan mutum da ya buɗe idanun makahon, bai iya ya kāre wannan daga mutuwa ba?”
38Sai Yesu, yana cike da baƙin ciki a ransa, ya zo kabarin — wani kogo ne da aka rufe da dutse.
39Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Marta, 'yar'uwar wanda ya mutun, ta ce masa, “Ubangiji, yanzu ya riga ya yi wari, ai ya yi kwana huɗu da mutuwa.”
40Yesu ya ce mata, “Ban gaya miki ba cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Ubanmu?”
41Sai suka kawar da dutsen. Yesu kuwa ya daga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka ji ni. 42Na san kullum kana jina, amma na faɗi haka ne saboda taron da suke tsaye a nan, domin su gaskata kai ka aiko ni.” 43Da ya faɗi haka, sai ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Li'azaru, fito waje!”
44Sai wanda ya mutun ya fito, ƙafafunsa da hannuwansa a ɗaure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuma a naɗe da zane. Yesu ya ce musu, “Ku kunce shi, ku bar shi yă tafi.”
Majalisa Ta Taru
45Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo wurin Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka gaskata da shi. 46Amma waɗansunsu suka tafi wurin Farisiyawa, suka gaya musu abin da Yesu ya yi. 47Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira majalisa, suka ce, “Mene ne za mu yi? Gama wannan mutum yana aikata alamu masu yawa. 48In muka ƙyale shi haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma su zo su ƙwace wurinmu da al'ummarmu.”
49Amma ɗayansu, Kayafas, babban firist na wannan shekara, ya ce musu, “Ba ku san kome ba ko kaɗan. 50Ba ku gane ba cewa ya fi muku kyau mutum ɗaya yă mutu saboda jama'a, da dukan al'umma ta hallaka?” 51Bai faɗi haka daga kansa ba, sai dai tun da yake shi ne babban firist na wannan shekara, ya yi annabci cewa Yesu zai mutu saboda al'ummar, 52ba don al'ummar kaɗai ba, har ma domin yă tara 'ya'yan Ubanmu da suka watse su zama ɗaya. b b v52 Kayafas ya yi magana mafi zurfi fiye da yadda ya sani. Yesu zai mutu ba don al'ummar Yahudawa kaɗai ba, har ma domin yă tara kowane ɗan Ubanmu da ya watse cikin iyali ɗaya. 53Saboda haka tun daga wannan rana suka ƙulla shawara domin su kashe shi. 54Saboda haka Yesu bai ƙara zagawa a fili a cikin Yahudawa ba, sai dai ya janye zuwa wani gari mai suna Ifraimu kusa da jeji, ya kuma zauna a can tare da almajiransa.
55Idin Ƙetarewa na Yahudawa kuwa ya kusa, mutane da yawa kuma suka haura daga ƙauyuka zuwa Urushalima kafin idin domin su tsarkake kansu. 56Suka yi ta neman Yesu, suna tambayar juna yayinda suke tsaye a cikin haikali, suna cewa, “Me kuke tsammani? Lalle ba zai zo idin ba, ko?” 57Manyan firistoci da Farisiyawa kuwa sun riga sun ba da umarni cewa duk wanda ya san inda yake, dole yă bayar da labari, domin su kama shi.