Abokan Ayuba Suka Yi Shiru
Abokan nan uku suka daina, sai wani saurayi mai suna Elihu, wanda yake sauraro tun farko, ya tafasa: yana fushi da Ayuba saboda ya baratar da kansa, yana fushi da abokan saboda sun hukunta shi ba tare da amsa ba. Hikima daga numfashin Mai Iko Duka take, in ji shi, ba daga furfura ba.
32 1Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin shi mai adalci ne a idanunsa. 2Sai fushin Elihu ɗan Barakel mutumin Buz, na iyalin Ram, ya ƙuna ƙwarai. Fushinsa ya ƙuna a kan Ayuba domin ya nuna kansa mai adalci ne maimakon Allah. 3Fushinsa ya kuma ƙuna a kan abokan Ayuba uku, domin ba su sami amsa ba, amma duk da haka suka yanke wa Ayuba hukunci. 4Elihu kuwa ya jira kafin yă yi magana da Ayuba, domin sauran sun girme shi. 5Amma da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da abin cewa, sai fushinsa ya ƙuna. 6Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ɗauki magana ya ce, “Ni ƙarami ne a shekaru, ku kuma tsofaffi ne; shi ya sa na janye, ina tsoron gaya muku abin da na sani. 7Na yi tunani, ‘Bari shekaru su yi magana, yawan shekaru kuma su koyar da hikima.’ 8Amma ruhu ne da yake cikin mutum, numfashin Maɗaukaki, shi ne yake ba da ganewa. 9Ba tsofaffi ba ne masu hikima, ba kuma dattawa ba ne suke fahimtar abin da yake daidai. 10Saboda haka ina cewa, ku saurare ni; ni ma zan faɗi abin da na sani. 11Ga shi, na jira maganarku; na saurari gardamarku yayin da kuke neman abin da za ku ce. 12Na mai da hankalina sosai gare ku; amma babu ko ɗayanku da ya nuna Ayuba ya yi kuskure, ko ya amsa gardamarsa. 13Saboda haka kada ku ce, ‘Mun sami hikima; bari Allah yă ƙaryata shi, ba mutum ba.’ 14Ayuba bai jero maganarsa gāba da ni ba, ni kuwa ba zan amsa masa da gardamarku ba. 15Sun firgita, ba su da sauran abin cewa; magana ta kāsa musu. 16Ya kamata in jira, yanzu da suka yi shiru, yanzu da suke tsaye babu wata amsa? 17Ni ma zan faɗi nawa; ni ma zan faɗi abin da na sani. 18Gama na cika da magana; ruhun da yake cikina yana matsa mini. 19A ciki, ina kama da ruwan inabi marar hanyar fita, kamar sababbin salkuna masu shirin fashewa. 20Dole in yi magana in sami sauƙi; dole in buɗe leɓunana in ba da amsa. 21Ba zan nuna sonkai ga kowa ba, ba kuma zan yi wa kowa zaƙin baki ba; 22gama ban san yadda ake zaƙin baki ba—in na yi, da Mahaliccina ya kawar da ni nan da nan.”