Rantsuwar Ayuba ta Zuciya Mai Tsabta
Ayuba ya ƙare da rantsuwa, yana buɗe rayuwarsa abu bayan abu: babu sha'awa, babu ƙarya, babu hana bawa adalci, babu cin abinci shi kaɗai alhali maraya yana jin yunwa, babu dogara ga zinariya. Ya sa hannu a kai ya nemi a kawo takardar tuhuma. Sa'an nan maganarsa ta tsaya kawai.
31 1“Na yi alkawari da idanuna; to yaya zan dinga kallon budurwa? 2Gama wane rabo zan samu daga Allah da yake bisa, wane gādo daga Maɗaukaki a can sama? 3Ashe, ba masifa ba ce ga marasa adalci, da bala'i ga masu aikata mugunta? 4Ashe, ba ya ganin hanyoyina, ba ya kuma ƙidaya kowane sawuna?
5“In na yi rayuwa cikin ƙarya, ƙafata kuma ta ruga cikin ha'inci, 6to, bari yă auna ni a kan ma'auni mai adalci, bari kuma Allah yă san gaskiyata, 7in sawayena sun kauce daga hanya, zuciyata kuma ta bi idanuna, wani ƙazanta kuma ya manne a hannuwana, 8to, bari in shuka wani kuma yă ci, bari kuma a tumɓuke abin da ya tsiro mini.
9“In mace ta rinjayi zuciyata, na kuma yi fako a bakin ƙofar maƙwabcina, 10to, bari matata tă yi wa wani mutum hidima, bari kuma waɗansu su kwana da ita. 11Gama wannan laifi ne mai kunya, zunubi ne da ya cancanci hukunci; 12gama wuta ce da take cinyewa har zuwa Hallaka, tă kuma ƙone dukan girbina.
13“In na hana wa bawana ko baiwata adalci sa'ad da suka kawo ƙara a kaina, 14to me zan yi sa'ad da Allah ya tashi? Sa'ad da ya kira ni ga lissafi, me zan amsa masa? 15Ashe, wanda ya yi ni a cikin mahaifa bai yi bawana ma ba? Ashe, ba shi ɗaya ne ya halicce mu biyu a cikin mahaifa ba?
16“In na hana wa matalauta abin da suke bukata, ko na sa idanun gwauruwa su gaji, 17ko na ci abincina ni kaɗai yayinda maraya bai sami kome ba, 18ko da yake tun ƙuruciyata na yi renonsa kamar yadda uba yake yi, tun daga cikin mahaifiyata kuma na shiryar da gwauruwa, 19in na ga wani yana mutuwa don rashin tufafi, ko matalauci da ba shi da abin rufuwa, 20in dukan ransa bai albarkace ni ba saboda na yi masa ɗumi da gashin tumakina, 21in na ɗaga hannuna a kan maraya domin na ga goyon bayana a wurin shari'a, 22to, bari kafaɗata tă fito daga mazauninta, bari kuma hannuna yă karye a gaɓarsa. 23Gama masifa daga Allah abin tsoro ce a gare ni, a gaban ɗaukakarsa kuma ban iya yin kome ba.
24“In na mai da zinariya abin dogarona, ko na ce wa zallan zinariya, ‘Kai ne tabbacina,’ 25in na yi fahariya cewa dukiyata mai yawa ce, cewa hannuna ya samu abu mai yawa ƙwarai, 26in na dubi rana sa'ad da take haskakawa, ko wata yana tafiya cikin ɗaukaka, 27har aka rinjayi zuciyata a ɓoye, hannuna kuma ya yi musu sumba ta sujada, 28wannan ma zunubi ne da ya cancanci hukunci, gama dā na yi wa Allah da yake bisa rashin aminci.
29“In na yi murna da hallakar wanda yake ƙina, ko na yi farin ciki sa'ad da masifa ta same shi. 30ban taɓa barin bakina yă yi zunubi ba ta wurin kiran la'ana a kan ransa, 31in mutanen gidana ba su taɓa cewa ba, ‘Wane ne bai ƙoshi daga teburinsa ba?’, 32babu baƙon da ya taɓa kwana a titi, gama na buɗe ƙofofina ga matafiyi. 33In na rufe zunubaina kamar yadda waɗansu suke yi, ina ɓoye laifina a cikin zuciyata, 34domin na ji tsoron taron jama'a ƙwarai, reni na kabilu kuma ya razana ni, har na yi shiru ban kuma fita waje ba.
35“Kash, da a ce wani zai saurare ni! Ga sa hannuna—bari Maɗaukaki yă amsa mini! Bari mai tuhumata yă rubuta ƙararsa! 36Lalle zan ɗauke shi a kafaɗata, zan ɗaura shi a kaina kamar kambi. 37Zan ba shi lissafin kowane sawuna; kamar yarima zan matso kusa da shi.
38“In ƙasata ta yi kuka a kaina, kwarukanta kuma sun yi kuka tare, 39in na ci amfaninta ba tare da biya ba, ko na murƙushe ran masu ita, 40to, bari ƙaya tă tsiro a maimakon alkama, da ciyawa mai wari a maimakon sha'ir.” Maganganun Ayuba sun ƙare.