Yanzu a bugun takarda

Ayuba 14 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Akwai Bege ga Mutum?

Itacen da aka sare yakan sake tohowa da jin ƙanshin ruwa, amma mutum yakan kwanta ba ya tashi. Ayuba yana tunani ko matattu za su iya rayuwa, yana hasashen a ɓoye shi har fushin ya wuce sa'an nan a sake kiransa, ya kuma ce Allah yana zaizaye bege kamar ruwa a kan dutse.

Babi na 14.

“Mutum, wanda mace ta haifa, kwanakinsa kaɗan ne, cike kuma yake da wahala. Yakan hudo kamar fure ya kuma bushe; yana gudu kamar inuwa, ba ya dawwama. A kan irin wannan ne kake kafa idanunka? Kana kuma kawo ni cikin shari'a tare da kai? Wa zai iya fitar da abu mai tsabta daga marar tsabta? Babu ko ɗaya. Da yake an ƙaddara kwanakinsa, yawan watanninsa yana hannunka, ka kuma kafa iyaka da ba zai iya ƙetarewa ba, ka kawar da kallo daga gare shi, domin ya huta, sai ya cika ranarsa kamar ɗan kwadago.

“Gama akwai bege ga itace: in an sare shi, zai sāke tsira, tohonsa kuma ba zai gaza ba. Ko da saiwarsa ta tsufa cikin ƙasa, gindinsa kuma ya mutu a turɓaya, da ƙanshin ruwa zai tohe ya kuma fid da rassa kamar sabuwar shuka. Amma mutum yakan mutu a kuma kwantar da shi; mutum ya ja numfashinsa na ƙarshe, ina kuwa yake? Kamar yadda ruwa yakan ƙafe daga tafki, kogi kuma ya raɓe ya bushe, haka mutum yakan kwanta ba ya kuwa tashi; sai sammai sun shuɗe, ba zai farka ba, ba kuwa za a tashe shi daga barci ba.

“Kash, da za ka ɓoye ni cikin kabari, ka ɓoye ni har sai fushinka ya wuce, ka kafa mini ƙayyadadden lokaci, ka kuma tuna da ni! In mutum ya mutu, zai sāke rayuwa? Dukan kwanakin wahalata zan yi jira, sai sabuntawata ta zo. Za ka kira, ni kuma in amsa maka; za ka yi marmarin aikin hannuwanka. Gama a lokacin za ka ƙidaya takawata; ba za ka kula da zunubina ba. Za a rufe tawayena a cikin jaka, za ka kuma rufe laifina.

“Amma kamar yadda tsauni yakan fāɗi ya kuma ragargaje, a kuma gusar da dutse daga wurinsa, kamar yadda ruwa yakan goge duwatsu, ambaliyarsa kuma ta kwashe ƙasar duniya, haka kake hallaka begen mutum. Kana rinjayarsa har abada, sai ya rabu da rai; kana ɓata masa fuska ka kuma kore shi. 'Ya'yansa maza sukan sami girma, shi kuwa bai sani ba; a kuma ƙasƙantar da su, shi kuwa bai lura ba. Yana jin zafin jikin kansa kaɗai, yana kuma yin makoki domin kansa kaɗai.”