Ayuba Ya Amsa wa Abokansa
Ayuba ya kira abokansa likitoci marasa amfani masu shafe gaskiya da ƙarya, ya kuma gargaɗe su cewa Allah ba zai gode musu ba don sun goyi bayansa da rashin gaskiya. Yana so ya kai ƙararsa gaban Allah da kansa: ko ya kashe ni, zan sa zuciya gare shi. Sa'an nan, don me kake ɓoye fuskarka?
13 1“Ga shi, idona ya ga dukan wannan; kunnena ya ji ya kuma gane shi. 2Abin da kuka sani, ni ma na sani; ban kasa ku ba. 3Amma zan yi magana da Maɗaukaki, ina kuma marmarin in kai ƙarata ga Allah. 4Amma kuna lulluɓe gaskiya da ƙarairayi; dukanku likitoci ne marasa amfani. 5Da ma za ku yi shiru ƙaƙaf—wannan zai zama hikimarku ke nan! 6Yanzu ku ji gardamata, ku kuma saurari roƙon leɓunana. 7Za ku yi magana ta ƙarya saboda Allah, ku kuma yi magana ta yaudara dominsa? 8Za ku nuna masa sonkai ne? Za ku yi gardama a madadin Allah? 9Zai zama da lafiya a gare ku sa'ad da ya bincike ku? Ko za ku iya yaudararsa yadda kuke yaudarar mutum? 10Lalle zai tsauta muku in kuka nuna sonkai a ɓoye. 11Darajarsa ba za ta razana ku ba, tsoronsa kuma yă sauko muku? 12Karin maganarku karin magana ne na toka; garkuwoyinku na laka ne.
13“Ku yi shiru a gabana, ku bar ni in yi magana; bari kome ya zo yă auko mini. 14Don me zan sa naman jikina cikin hatsari, in kuma ɗauki raina a hannuwana? 15Ko da ya kashe ni, zan sa begena gare shi; duk da haka zan kāre hanyoyina a gabansa. a a v15 Ko a cikin korafinsa, dogaron Ayuba yana nufin Allah. Cikakkiyar budaddiyar dangantakar tana zuwa daga baya — Ayuba ya ga Ubanmu fuska da fuska a ƙarshen littafin. 16Wannan ma zai zama ceto na, gama babu maras tsoron Allah da zai yi ƙarfin halin zuwa gabansa. 17Ku saurari maganata da kyau; bari furcina yă kai kunnuwanku. 18Ga shi, na shirya ƙarata; na san za a wanke ni. 19Wa zai yi gardama da ni? Gama a lokacin zan yi shiru in mutu.
20“Ka yi mini abu biyu kaɗai, sa'an nan ba zan ɓoye kaina daga fuskarka ba: 21Ka janye hannunka nesa da ni, kada kuma ka bar tsoronka yă razana ni. 22Sa'an nan ka kira, ni kuwa in amsa; ko kuwa in yi magana, kai kuma ka amsa mini. 23Laifofina da zunubaina nawa ne? Ka nuna mini tawayena da zunubina. 24Don me kake ɓoye fuskarka, kana kuma ɗaukana a matsayin maƙiyinka? 25Za ka razana ganyen da iska take korarsa, ka kuma bi busasshen yayi? 26Gama kana rubuta abubuwa masu ɗaci a kaina, kana kuma sa in gāji zunuban ƙuruciyata. 27Ka sa ƙafafuna cikin turu, kana kuma lura da dukan hanyoyina; ka sa iyaka ga tafin ƙafafuna.
28“Saboda haka mutum yana lalacewa kamar ruɓaɓɓen itace, kamar tufafin da asu ya cinye.”