Ayuba Ya Amsa
Ayuba ya mayar da ba'a da ba'a, hikima za ta mutu tare da ku, sa'an nan ya ce har dabbobi da tsuntsaye sun san cewa hannun Ubanmu ne ya yi wannan. Waƙarsa ba ta ta'azantarwa: Allah yakan tuɓe mashawarta, alƙalai, firistoci da sarakuna, ya bar shugabannin duniya suna lalube cikin duhu.
12 1Sai Ayuba ya amsa ya ce, 2“Babu shakka ku ne mutane, hikima kuma za ta mutu tare da ku. 3Amma ni ma ina da hankali kamar ku; ban gaza ku ba. Wane ne bai san irin waɗannan abubuwa ba? 4Na zama abin dariya ga abokaina—ni, wanda na kira ga Allah ya kuma amsa mini; mutum mai adalci marar aibu, yanzu na zama abin dariya. 5Masu jin daɗi sukan rena masifa—bugu a shirye ga waɗanda ƙafafunsu ke santsi. 6Tentunan 'yan fashi suna zaman lafiya, waɗanda suke tsokanar Allah kuma suna cikin aminci—waɗanda suke ɗauke da allahnsu a hannunsu. a a v6 Waɗanda suke ɗauke da allahnsu a hannunsu: mutanen da suka dogara gaba ɗaya ga ƙarfinsu maimakon Allah. 7Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka; tsuntsayen sama, za su kuma gaya maka; 8ko ka yi magana da ƙasa, za ta kuma koya maka; kifayen teku kuma za su bayyana maka. 9Wane ne a cikin dukan waɗannan bai sani ba cewa hannun Ubanmu ne ya yi wannan? b b v9 Cikin dogon muhawararsa da abokansa uku, wannan shi ne wuri ɗaya tak da Ayuba ya ambaci Ubanmu da suna — sunan dangantaka da abokansa ba za su taɓa amfani da shi ba. Zuciyarsa, ko a cikin kukansa, tana nema ta kai ga Uban da ya taɓa sani. 10A hannunsa ne ran kowane mai rai da numfashin dukan 'yan adam yake. 11Ashe, kunne ba ya gwada kalmomi kamar yadda baki yake ɗanɗana abincinsa? 12Ana samun hikima wurin tsofaffi, ana kuma samun ganewa a tsawon kwanaki. 13A wurinsa ne hikima da iko suke; shawara da ganewa nasa ne. 14Abin da ya rushe ba za a iya sāke gina shi ba; wanda ya tsare ba za a iya saki ba. 15In ya riƙe ruwaye, sai su ƙafe; in ya sake su, sai su mamaye ƙasa. 16A wurinsa ne ƙarfi da hikima ta gaskiya suke; wanda aka ruɗe da mai ruɗi duka nasa ne. 17Yakan tafi da mashawarta a tube, yă kuma wofintar da alƙalai. 18Yakan kunce ɗaurin da sarakuna suka sa yă kuma ɗaura bante a kugunsu. 19Yakan tafi da firistoci a tube yă kuma tumɓuke waɗanda suka daɗe da kafuwa. 20Yakan rufe bakunan amintattu yă kuma ƙwace wa dattawa hikimar ganewa. 21Yakan zubar da kunya a kan fadawa yă kuma ƙwace wa masu ƙarfi ƙarfinsu. 22Yakan bayyana abubuwa masu zurfi daga duhu yă kuma fito da inuwa mai zurfi zuwa cikin haske. 23Yakan sa al'ummai su yi girma, sa'an nan yă hallaka su; yakan faɗaɗa al'ummai, sa'an nan yă bi da su. 24Yakan ƙwace wa shugabannin duniya hankali yă kuma sa su yi ta yawo a jeji marar hanya. 25Suna lalubo a cikin duhu babu haske, yă kuma sa su yi tangaɗi kamar bugagge.”