Yanzu a bugun takarda

Ayuba 11 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Zofar Ya Amsa

Zofar ya fi kowa tsanani: Ayuba yana yawan magana, kuma Allah ya hukunta shi ƙasa da yadda laifinsa ya cancanta. Ka kawar da zunubi daga alfarwarka, in ji shi, rai kuma zai fi tsakar rana haske. Yana da cikakken tabbaci, kuma ga marar laifi yake faɗar haka.

Babi na 11.

Sai Zofar mutumin Na'ama ya amsa ya ce, “Ba za a amsa wannan ambaliyar kalmomi ba? Za a nuna mai yawan surutu yana da gaskiya? Surutunka na banza zai sa waɗansu su yi shiru? Za ka yi ba'a babu wanda zai kunyata ka? Gama ka ce, ‘Koyarwata tsarkakakkiya ce, kuma ni mai tsabta ne a gabanka.’ Amma kash, da a ce Allah zai yi magana ya buɗe leɓunansa game da kai, ya kuma bayyana maka asiran hikima— gama hikima ta gaskiya tana da gefe biyu. Ka sani fa cewa Allah bai nemi lissafi gare ka gwargwadon laifinka ba. Ko za ka iya gane zurfafan abubuwan Allah? Ko za ka iya kai ga iyakar Maɗaukaki? Sun fi sammai tsayi—me za ka iya yi? Sun fi kabari zurfi—me za ka iya sani? Awonsu ya fi duniya tsawo, ya kuma fi teku faɗi. In ya ratsa ya kuma kulle mutum ya kira shi zuwa hukunci, wa zai iya mayar da shi baya? Gama ya san mutane masu banza; sa'ad da ya ga mugunta, ba zai lura da ita ba? Amma marar hankali zai zama mai hikima sa'ad da aka haifi ɗan jakin jeji mutum. In ka shirya zuciyarka ka miƙa hannuwanka gare shi, in zunubi yana a hannunka, ka yar da shi, kada kuma ka bar rashin adalci yă zauna a tentunanka, to lalle za ka ɗaga fuskarka, babu kunya; za ka tsaya daram ba za ka ji tsoro ba. Za ka manta da wahalarka, ka tuna da ita kamar ruwan da ya kwararo ya wuce. Rayuwarka za ta fi tsakar rana haske; duhunta zai zama kamar safiya. Za ka ji kwanciyar hankali, domin akwai bege; za ka waiwaya ka kwanta lafiya. Za ka kwanta babu wanda zai tsoratar da kai, mutane da yawa kuma za su nemi tagomashinka. Amma idanun mugaye za su gaza; kowace hanyar tsira za ta rasu musu, begensu kaɗai kuwa shi ne su ja numfashinsu na ƙarshe.”