Sarki Ya Ji Tsoro, Aka Kira Annabi
Da abin da Isra'ila suka yi wa Amoriyawa ya tsoratar da su, Mowab suka yi hayar Bala'am ya la'anta su. Ba zai iya faɗar kome ba sai abin da Ubanmu ya faɗa masa, kuma jaka ce ta bayyana wannan, wadda ta ga takobin da aka zare yana tsaye a hanya alhali sanannen mai gani bai gani ba.
22 1Sai Isra'ilawa suka kama hanya, suka yi sansani a filayen Mowab, a ƙetaren Urdun, ɗaura da Yeriko. 2Balak ɗan Zippor ya ga duk abin da Isra'ila ya yi wa Amoriyawa. 3Mowab ya ji tsoron mutanen ƙwarai, gama suna da yawa; Mowab ya firgita saboda Isra'ilawa. 4Mowab ya ce wa dattawan Midiyan, “Wannan taron mutane za su lashe duk abin da yake kewaye da mu, kamar yadda sa yakan lashe ciyawar jeji.” Balak ɗan Zippor shi ne sarkin Mowab a lokacin.
5Ya aiki manzanni wurin Bala'am ɗan Be'or a Fetor, kusa da Kogin Yuferatis a ƙasar mutanensa, domin su kira shi. Ya ce, “Duba, ga wasu mutane sun fito daga Masar. Duba, sun rufe fuskar ƙasa, kuma sun zauna ɗaura da ni. 6Ka zo, ina roƙonka ka la'anta mini mutanen nan—sun fi ni ƙarfi. Watakila sa'an nan in iya bugansu in kuma kore su daga ƙasar, gama na sani, duk wanda ka sa masa albarka, mai albarka ne, duk wanda kuma ka la'anta, la'ananne ne.”
7Dattawan Mowab da dattawan Midiyan suka tafi, da kuɗin duba a hannunsu, suka zo wurin Bala'am suka faɗa masa maganar Balak.
8Ya ce musu, “Ku kwana a nan daren nan, zan kuwa komo muku da amsa yadda Allah zai faɗa mini.” Sai shugabannin Mowab suka zauna tare da Bala'am.
9Sai Ubanmu ya zo wurin Bala'am ya ce, “Su wane ne mutanen nan da suke tare da kai?”
10Bala'am ya ce wa Ubanmu, “Balak ɗan Zippor, sarkin Mowab, ya aiko mini da saƙo, 11Duba, mutanen da suka fito daga Masar sun rufe fuskar ƙasa. Ka zo yanzu, ka la'anta mini su—watakila in iya yaƙe su in kuma kore su.”
12Amma Ubanmu ya ce wa Bala'am, “Kada ka tafi tare da su. Kada ka la'anta mutanen, gama masu albarka ne.”
13Bala'am ya tashi da safiyar nan ya ce wa shugabannin Balak, “Ku koma ƙasarku—Allah ya ƙi ya bar ni in tafi tare da ku.”
14Shugabannin Mowab suka tashi, suka tafi wurin Balak, suka ce, “Bala'am ya ƙi ya zo tare da mu.”
15Sai Balak ya sāke aikan shugabanni—masu yawa da kuma martaba fiye da na farko. 16Suka zo wurin Bala'am suka ce, “Ga abin da Balak ɗan Zippor ya ce, kada ka bar wani abu yă hana ka zuwa wurina, 17gama zan ɗaukaka ka ƙwarai, in kuma yi duk abin da ka faɗa mini. Saboda haka ina roƙonka ka zo ka la'anta mini mutanen nan.”
18Bala'am ya amsa wa bayin Balak ya ce, “Ko da Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan iya ƙetare umarnin Allah ba, in yi ƙarami ko babba. 19To yanzu, ina roƙonku, ku ma ku kwana a nan daren nan, domin in san abin da Ubanmu zai ƙara faɗa mini.”
20Sai Ubanmu ya zo wurin Bala'am da dare ya ce masa, “Da yake mutanen nan sun zo su kira ka, ka tashi ka tafi tare da su, amma sai dai abin da na faɗa maka kaɗai za ka yi.”
21Sai Bala'am ya tashi da safe, ya ɗora wa jakinsa sirdi, ya tafi tare da shugabannin Mowab.
Ubanmu Ya Yi Magana ta Bakin Jaki
22Amma fushin Ubanmu ya ƙuna domin ya tafi, sai mala'ikan Ubanmu ya tsaya a kan hanya domin yă yi gāba da Bala'am. Bala'am yana a kan jakinsa, tare da bayinsa biyu. 23Jakar ta ga mala'ikan Ubanmu tsaye a kan hanya, da takobinsa zārarre a hannunsa, sai ta kauce daga hanya ta shiga jeji. Sai Bala'am ya bugi jakar domin yă mayar da ita kan hanya. 24Sa'an nan mala'ikan Ubanmu ya tsaya a wata matsattsiyar hanya tsakanin gonakin inabi, da katanga a kowane gefe. 25Jakar ta ga mala'ikan Ubanmu, sai ta matsa ga katangar, ta kuma matsa ƙafar Bala'am a jikinta, sai ya sāke bugunta.
26Mala'ikan Ubanmu ya ƙara gaba ya tsaya a wani wuri matsattse inda babu wurin juyawa dama ko hagu. 27Da jakar ta ga mala'ikan Ubanmu, sai ta kwanta ƙarƙashin Bala'am; sai fushinsa ya ƙuna, ya bugi jakar da sandansa.
28Sai Ubanmu ya buɗe bakin jakar, sai ta ce wa Bala'am, “Me na yi maka, da ka buge ni sau uku yanzu?”
29Bala'am ya ce wa jakar, “Kin yi mini ba'a! Da a ce ina da takobi a hannuna, da na kashe ki yanzu.”
30Jakar ta ce wa Bala'am, “Ba jakarka ba ce ni, wadda ka riƙa hawa dukan kwanakin ranka har yă zuwa yau? Na taɓa yin maka haka a dā?” Ya ce, “A'a.”
31Sai Ubanmu ya buɗe idanun Bala'am, sai ya ga mala'ikan Ubanmu tsaye a kan hanya, da takobi zārarre a hannu, sai ya sunkuya ya fāɗi rubda ciki.
32Mala'ikan Ubanmu ya ce masa, “Me ya sa ka bugi jakarka sau uku? Ga ni na fito domin in yi gāba da kai, domin hanyarka karkatacciya ce a gabana. 33Jakar ta gan ni ta kuma kauce mini sau uku. Da ba ta kauce ba, da na kashe ka yanzu da na bar ta da rai.”
34Bala'am ya ce wa mala'ikan Ubanmu, “Na yi zunubi—ban san kana tsaye a kan hanya domin ka tare ni ba. To yanzu in wannan bai gamshe ka ba, zan koma.”
35Mala'ikan Ubanmu ya ce wa Bala'am, “Ka tafi tare da mutanen, amma sai dai abin da na faɗa maka kaɗai za ka faɗa.” Sai Bala'am ya ci gaba tare da shugabannin Balak.
36Da Balak ya ji Bala'am yana zuwa, sai ya fito domin yă tarye shi a birnin Mowab, a kan iyakar Arnon, a iyakar ƙarshen ƙasar. 37Balak ya ce wa Bala'am, “Ban aika da gaggawa domin a kira ka ba? Me ya sa ba ka zo wurina ba? Da gaske ne ba zan iya ɗaukaka ka ba?”
38Bala'am ya ce wa Balak, “Duba, ga ni na zo wurinka yanzu—amma ina iya faɗin kowane irin abu ne? Sai dai abin da Allah ya sa a bakina kaɗai zan iya faɗa.”
39Sai Bala'am ya tafi tare da Balak, suka kuma zo Kiriyat-huzot. 40Balak ya yanka shanu da tumaki, ya kuma aika rabo ga Bala'am da shugabannin da suke tare da shi. 41Da safe Balak ya ɗauki Bala'am ya haura da shi zuwa Bamot-ba'al, daga can kuwa ya ga ƙarshen jama'ar.