Isra'ila Ya Yi Kuka, Ubanmu kuma Ya Amsa
Da suka gaji da hanya, mutanen suka yi magana gāba da Ubansu da gāba da Musa, macizai kuma suka sare su; maganin shi ne macijin tagulla da aka ɗaga a kan sanda domin su dube shi. Sa'an nan sai waƙa a bakin rijiya da nasarori a kan Sihon da Og.
21 1Da Bakan'ane, sarkin Arad, wanda yake zama a Negeb, ya ji Isra'ila na zuwa ta hanyar Atharim, sai ya yaƙi Isra'ila, ya kuma kame waɗansu. 2Isra'ila ya yi wa Ubanmu alkawari ya ce, “In har ka ba da mutanen nan a hannuna, zan hallaka biranensu ƙaƙaf.” 3Ubanmu ya ji muryar Isra'ila, ya kuma ba da Kan'aniyawa a hannunsu. Suka hallaka su da biranensu ƙaƙaf. Saboda haka aka sa wa wurin suna Horma.
Macijin Tagulla
4Suka tashi daga Dutsen Hor suka nufi Jar Teku domin su kewaye ƙasar Edom, amma mutanen suka karai a kan hanya. 5Mutanen suka yi magana gāba da Ubanmu da kuma gāba da Musa suka ce, “Me ya sa kuka fisshe mu daga Masar domin mu mutu a jeji? Babu gurasa, babu ruwa, kuma mun ƙyamaci wannan abinci maras amfani.”
6Sai Ubanmu ya aiko da macizai masu dafi cikin mutanen; suka sari mutanen, Isra'ilawa da yawa kuwa suka mutu. 7Mutanen suka zo wurin Musa suka ce, “Mun yi zunubi domin mun yi magana gāba da Ubanmu da kuma gāba da kai. Ka yi addu'a gare shi domin yă kawar da macizan daga gare mu.” Sai Musa ya yi wa mutanen addu'a.
8Ubanmu ya ce wa Musa, “Ka ƙera maciji mai dafi, ka sa shi a kan sanda; duk wanda aka sare shi, in ya dubi macijin, zai rayu.”
9Sai Musa ya yi macijin tagulla ya sa shi a kan sanda; duk sa'ad da maciji ya sari wani, sai ya dubi macijin tagullan, ya rayu. a a v9 Yesu ya nuna wannan lokaci a matsayin siffar kansa: kamar yadda aka ɗaga macijin tagulla sama domin masu mutuwa su duba su rayu, haka aka ɗaga Ɗa sama domin duk wanda ya dubi shi da bangaskiya yă rayu (Yohanna 3:14-15).
Tafiya zuwa Mowab
10Isra'ilawa suka tashi suka yi sansani a Obot. 11Suka tashi daga Obot suka yi sansani a Iye-abarim, a cikin jeji wanda yake fuskantar Mowab, wajen gabas. 12Daga nan suka tashi suka yi sansani a Kwarin Zered. 13Daga nan suka ƙaura suka yi sansani a hayin Arnon, a cikin jeji wanda yake miƙe daga yankin Amoriyawa; gama Arnon shi ne iyakar Mowab da Amoriyawa. 14Saboda haka Littafin Yaƙe-yaƙe na Ubanmu ya ce, “Waheb a Sufa, da kwazazzabai na Arnon, 15da gangaren kwazazzabai da yake karkata wajen wurin Ar yă kuma kai ga iyakar Mowab.”
16Daga nan suka tafi Beyer, rijiyar da Ubanmu ya ce wa Musa, “Ka tara mutanen—zan ba su ruwa.”
17Sa'an nan Isra'ila ya rera wannan waƙa, “Ɓuɓɓugo, ya rijiya! Ku rera mata! 18Rijiyar da sarakuna suka haƙa, wadda manyan mutane suka haƙo da sandunan mulkinsu da sandunansu.” Sa'an nan daga jeji suka tafi Mattana, 19daga Mattana zuwa Nahaliyel, daga Nahaliyel zuwa Bamot, 20daga Bamot kuma zuwa kwari a filin Mowab, zuwa ƙwanƙolin Fisga wanda yake kallon jeji.
Ubanmu Ya Ba da Sihon a Hannunsu
21Sa'an nan Isra'ila ya aiki manzanni wurin Sihon sarkin Amoriyawa, yana cewa, 22“Bari in bi ta ƙasarka. Ba za mu kauce zuwa gona ko gonar inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiya ba. Za mu bi Babbar Hanyar Sarki har sai mun ƙetare iyakarka.”
23Amma Sihon ya ƙi barin Isra'ila yă ƙetare yankinsa. Ya tara dukan mutanensa, ya fita jeji don yă yaƙi Isra'ila, ya kai Yahaz, ya kuma yaƙi Isra'ila. 24Isra'ila ya buge shi da takobi, ya kuma ƙwace ƙasarsa daga Arnon zuwa Yabbok—har zuwa Ammonawa, waɗanda iyakarsu take da kāriya. 25Isra'ila ya kame dukan biranen nan ya kuma zauna cikin kowane birnin Amoriyawa—Heshbon da dukan ƙauyukan da suke kewaye da ita. 26Gama Heshbon ita ce birnin Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yaƙi tsohon sarkin Mowab ya kuma ƙwace dukan ƙasarsa daga gare shi, har zuwa Arnon. 27Saboda haka mawaƙa su ce, “Ku zo Heshbon—a sāke gina ta, a maido da birnin Sihon. 28Gama wuta ta fito daga Heshbon, harshen wuta daga birnin Sihon. Ta cinye Ar ta Mowab, iyayengijin tuddan Arnon. 29Kaiton ki, Mowab! Kin hallaka, ya mutanen Kemosh! Ya mai da 'ya'yansa maza 'yan gudun hijira, 'ya'yansa mata kuma kamammu ga Sihon sarkin Amoriyawa. 30Amma mun buge su; Heshbon ta hallaka har zuwa Dibon. Mun lalatar har zuwa Nofa, wadda take kaiwa ga Medeba.”
31Saboda haka Isra'ila ya zauna a ƙasar Amoriyawa. 32Musa ya aiki mutane su leƙi asirin Yazer; suka kame ƙauyukanta suka kuma kori Amoriyawa da suke can. 33Sa'an nan suka juya suka hau ta hanyar Bashan, sai Og sarkin Bashan ya fito don yă yaƙe su, shi da dukan mutanensa, domin yă yi yaƙi a Edireyi.
34Amma Ubanmu ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa—na ba da shi, da dukan mutanensa, da ƙasarsa a hannunka. Ka yi masa yadda ka yi wa Sihon sarkin Amoriyawa, wanda yake zama a Heshbon.”
35Suka buge shi, da 'ya'yansa, da dukan mutanensa, har ba a bar wani mai rai ba, suka kuma mallaki ƙasarsa.