Matan da Suka Yi Tafiya tare da Yesu
An ambaci sunayen matan da suke ɗaukar nauyin aikin. Misali game da ƙasa iri-iri ya bayyana dalilin da ya sa maganar Ubanmu ba ta yin amfani a wasu. Ya kwantar da hadari, ya 'yanta wani mutum da ake kira Tuli wanda maƙwabtansa suka roƙe shi ya tafi, sa'an nan ya warkar da wata mace mai zubar jini ya kuma ta da 'yar Yayirus.
8 1Ba a daɗe ba, sai ya yi tafiya ta cikin birane da ƙauyuka, yana wa'azi yana kuma shelar bisharar Mulkin Ubanmu. Sha biyun nan suna tare da shi, 2da waɗansu mata da aka warkar daga mugayen ruhohi da cututtuka: Maryamu, wadda ake kira Magadaliya, wadda aljanu bakwai suka rabu da ita, 3da Yuwanna, matar Kuza, wakilin Hirudus, da Suzanna, da waɗansu da yawa, waɗanda suke taimakonsu daga abin da suke da shi.
4Da wani babban taro ya taru, mutane daga kowane birni kuma suna zuwa wurinsa, sai ya yi musu magana da misali, ya ce,
5“Wani manomi ya fita don shuka. Yayinda yake shuka, sai waɗansu iri suka fāɗi a kan hanya, aka tattake su, tsuntsayen sama kuma suka cinye su. 6Waɗansu iri suka fāɗi a kan dutse; da suka tsira, sai suka yanƙwane domin rashin ruwa. 7Waɗansu suka fāɗi cikin ƙayayuwa, ƙayayuwan kuma suka yi girma tare da su, suka shaƙe su. 8Waɗansu iri kuma suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka yi girma, suka ba da amfani riɓi ɗari.” Da ya faɗi haka, sai ya ɗaga murya ya ce, “Duk mai kunnuwan ji, to, yă ji.”
9Almajiransa suka tambaye shi ma'anar misalin nan.
10Sai ya ce, “An ba ku ikon sanin asiran Mulkin Ubanmu; amma ga sauran, da misalai ake musu, domin ‘ko da suna kallo, ba za su gani ba, ko da suna ji kuma, ba za su gane ba.’”
11“To, ga ma'anar misalin: Irin shi ne maganar Ubanmu. 12Waɗanda suke a kan hanya su ne waɗanda suke ji; sa'an nan Iblis yă zo yă ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata su sami ceto. 13Waɗanda suke a kan dutse su ne waɗanda sukan ji maganar su karɓe ta da farin ciki, amma ba su da saiwa; sukan gaskata na ɗan lokaci, sa'an nan su fāɗi a lokacin jarabawa. 14Abin da ya fāɗi cikin ƙayayuwa kuwa: waɗannan su ne waɗanda suke ji, amma yayinda suke tafiya, sai damuwoyin rayuwa, da wadata, da jin daɗi, su shaƙe su, 'ya'yansu kuma ba sa nunawa. 15Amma wanda yake a ƙasa mai kyau: waɗannan sukan ji maganar da zuciya ta gaskiya mai kyau, su riƙe ta sosai, su ba da 'ya'ya ta wurin jimiri.”
Hasken da ba za a Iya Ɓoye shi ba
16“Ba wanda yakan ƙuna fitila yă rufe ta da tulu, ko yă sa ta a ƙarƙashin gado; a maimako, yakan ajiye ta a kan madauri, domin masu shiga su ga hasken. 17Gama babu wani abin da yake a ɓoye da ba za a bayyana shi ba, babu kuma wani abin da yake a asirce da ba za a sani ba a kuma kawo shi cikin haske. 18Saboda haka ku kula da yadda kuke saurara, gama duk mai shi, za a ƙara masa; duk wanda ba shi da shi kuma, har ma abin da yake tsammani yana da shi za a karɓe masa.”
Iyalin Ubanmu
19Mahaifiyarsa da 'yan'uwansa suka zo wurinsa, amma ba su iya kaiwa gare shi ba saboda taron. 20Sai aka gaya masa, “Mahaifiyarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna son su gan ka.”
21Amma ya amsa musu ya ce, “Mahaifiyata da 'yan'uwana su ne waɗanda suke jin maganar Ubanmu suke kuma aikata ta.”
Yesu ya Umarci Hadari
22Wata rana, shi da almajiransa suka shiga jirgin ruwa. Ya ce musu, “Mu haye zuwa ƙetaren tafkin.” Sai suka tashi.
23Yayinda suke tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata guguwa ta sauko a kan tafkin; jirgin ruwan ya cika da ruwa, suka kuma shiga hatsari. 24Suka tashe shi, suna cewa, “Mallam, Mallam, za mu nutse!” Sai ya tashi, ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan; suka tsaya, aka kuma yi tsit. 25Ya tambaye su, “Ina bangaskiyarku?” Da tsoro da kuma mamaki, suka ce wa juna, “Wane ne wannan ne? Yana umartar har iskoki da ruwa, suna kuma yin masa biyayya.”
Mutumin da aka Kuɓutar daga Runduna
26Sai suka tuƙa zuwa yankin Garasinawa, wanda yake ƙetaren Galili. 27Da Yesu ya sauka a ƙasa, sai wani mutum mai aljanu daga birnin ya taras da shi. Tun dā can bai sa tufafi ba, bai kuma zauna a gida ba sai dai a cikin kaburbura. 28Da ya ga Yesu, sai ya yi ihu, ya fāɗi a gabansa, ya ce da babbar murya, “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Maɗaukaki? Ina roƙonka, kada ka ba ni azaba!” 29Domin Yesu ya umarci ƙazamin ruhun yă fita daga mutumin, gama ya sha kama shi; ko da yake ana tsaronsa a kuma daure shi da sarƙoƙi da ƙarafa a ƙafafunsa, yakan tsintsinke su, aljanin kuma yă kore shi zuwa jeji.
30Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Ya ce, “Runduna,” gama aljanu da yawa sun shige shi.
31Suka kuma roƙe shi kada yă umarce su su shiga cikin ramin marar iyaka.
32A can kuwa akwai wani babban garken aladu suna kiwo a gefen tudu. Sai aljanun suka roƙe shi yă bar su su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu. 33Sai aljanun suka fita daga mutumin suka shiga cikin aladun; garken kuma ya runtume daga kan tudu zuwa cikin tafkin, suka nutse.
34Da masu kiwon suka ga abin da ya faru, sai suka gudu, suka ba da labari a cikin birni da kuma a ƙauyuka. 35Mutane suka fito domin su ga abin da ya faru. Da suka kai wurin Yesu, sai suka tarar da mutumin da aljanu suka rabu da shi yana zaune a gaban Yesu, saye da tufafi, hankalinsa kuma a kwance—sai tsoro ya kama su. 36Waɗanda suka ga abin kuwa suka gaya musu yadda aka warkar da mutumin nan mai aljanu. 37Sai dukan mutanen yankin Garasinawa suka roƙe shi yă rabu da su, gama tsoro mai girma ya kama su. Sai ya shiga jirgin ruwa, ya koma. 38Mutumin da aljanu suka rabu da shi ya roƙe shi yă tafi tare da shi, amma Yesu ya salame shi, yana cewa,
39“Koma gida; ka faɗa yadda Ubanmu ya yi maka abubuwa masu girma.” Sai ya tafi, yana shelar ko'ina a cikin dukan birnin yadda Yesu ya yi masa abubuwa masu girma.
Warkarwa da Tashi ta Wurin Bangaskiya
40To, da Yesu ya dawo, sai taron suka marabce shi, gama dukansu suna jiransa. 41Sai wani mutum mai suna Yayirus, shugaban majami'a, ya zo ya fāɗi a gaban ƙafafun Yesu, yana roƙonsa yă zo gidansa, 42gama yana da makaɗaiciyar 'ya mace, wadda ta kai kamar shekara goma sha biyu, tana kuma bakin mutuwa. Yayinda Yesu yake tafiya, sai taron suka matsa masa. 43Sai ga wata mace wadda ta sha zuban jini shekara goma sha biyu; ta kashe dukan dukiyarta a kan likitoci, amma babu wanda ya iya warkar da ita. 44Ta zo ta bayansa, ta taɓa gefen rigarsa, nan da nan kuwa zuban jininta ya tsaya.
45Yesu ya ce, “Wa ya taɓa ni?” Da dukansu suka ƙaryata, sai Bitrus ya ce, “Mallam, taron suna cincika suna kuma matsa maka.”
46Amma Yesu ya ce, “Wani ya taɓa ni, gama na ji iko ya fita daga gare ni.”
47Da macen ta ga ba za ta iya ɓoyewa ba, sai ta zo da rawan jiki, ta fāɗi a gabansa, ta kuma bayyana a gaban kowa dalilin da ya sa ta taɓa shi da kuma yadda ta warke nan take.
48Sai ya ce mata, “'Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke; ki tafi lafiya.”
49Tun yana cikin magana, sai wani daga gidan shugaban majami'a ya zo ya ce, “'Yarka ta mutu; kada ka ƙara dami Malam.”
50Amma Yesu ya ji, ya amsa masa ya ce, “Kada ka ji tsoro; ka gaskata kawai, za kuwa a cece ta.”
51Da ya isa gidan, bai bar kowa yă shiga tare da shi ba sai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma uban yarinyar da mahaifiyarta.
52Kowa yana kuka yana kuma makokinta, amma ya ce, “Kada ku yi kuka, gama ba ta mutu ba, barci take yi kawai.”
53Sai suka yi masa dariya, domin sun san ta mutu.
54Amma ya kama hannunta, ya ɗaga murya ya ce, “Yarinya, ki tashi.”
55Sai ruhunta ya dawo, ta kuma tashi nan take. Ya umarce su su ba ta wani abu ta ci. 56Iyayenta suka yi mamaki, amma ya umarce su kada su gaya wa kowa abin da ya faru.