Matattun Ƙudaje a cikin Mai
Karin magana game da yadda ƙaramin abu yakan ɓata abu mai yawa: matattun ƙudaje cikin turare, bayi a kan dawakai, sarakuna kuma a ƙasa, wawa wanda yake hallaka kansa da maganarsa. Natsuwa takan kwantar da fushin mai mulki; rufin da yake lanƙwasa da maganar rashin hankali a ɗakin kwana, dukansu sukan fara kaɗan.
10 1Matattun ƙudaje sukan sa man mai turare ya yi wari ya kuma ruɓe; haka ma ɗan wauta kaɗan ya fi hikima da daraja nauyi. 2Zuciyar mai hikima takan karkata ga damansa, amma zuciyar wawa ga hagunsa. 3Ko sa'ad da wawa yake tafiya a kan hanya, ba shi da hankali, yana kuma nuna wa kowa cewa shi wawa ne. 4Idan fushin mai mulki ya tashi gāba da kai, kada ka bar matsayinka, gama natsuwa takan kwantar da manyan laifuffuka.
5Akwai wata mugunta da na gani a ƙarƙashin rana, irin kuskuren da yakan fito daga wurin mai mulki: 6an sa wauta a manyan muƙamai masu yawa, yayin da masu arziki suke zaune a ƙananan muƙamai. 7Na ga bayi a kan dawakai, da sarakuna suna tafiya da ƙafa kamar bayi. 8Duk wanda ya haƙa rami yana iya fāɗuwa a cikinsa, kuma duk wanda ya rushe katanga maciji yana iya sāre shi. 9Duk wanda yake farfasa duwatsu yana iya jin ciwo daga gare su, kuma duk wanda yake tsattsaga katakai yana cikin hatsari daga gare su. 10Idan gatari ya yi ƙauri kuma ba a wasa bakinsa ba, dole ka yi amfani da ƙarfi mai yawa; amma hikima takan kawo nasara.
11Idan maciji ya sāra kafin a yi masa gardi, mai gardi ba zai sami wata riba ba. 12Kalmomin mai hikima suna jawo masa alheri, amma leɓunan wawa sukan hallaka shi. 13Farkon kalmominsa wauta ne, ƙarshen maganarsa kuwa mugun hauka ne. 14Duk da haka wawa yakan ci gaba da magana. Babu wanda ya san abin da yake zuwa, kuma wa zai iya gaya wa kowa abin da zai faru bayansa?
15Wawaye sukan gajiyar da kansu da aikinsu, gama ba su ma san hanyar zuwa gari ba. 16Kaitonki, ya ƙasa, sa'ad da sarkinki yaro ne, sarakunanki kuma suke liyafa da safe. 17Albarka tā tabbata gare ki, ya ƙasa, sa'ad da sarkinki ɗan manya ne, sarakunanki kuma suke liyafa a daidai lokaci— domin ƙarfi, ba domin buguwa ba. 18Saboda ƙyuya katakan rufi sukan lankwashe, saboda hannuwan kasala kuma gida yakan yi ɗigo. 19Ana shirya abinci domin dariya, ruwan inabi kuma yakan faranta rai, kuɗi kuwa yakan amsa kome. 20Kada ka la'anci sarki ko a cikin tunaninka, kada kuma ka la'anci mai arziki ko a cikin ɗakin kwananka, gama tsuntsun sama yana iya ɗaukar maganarka, kuma mai fikafikai yana iya ba da labarin abin da ka faɗa.