Gurasa a Kan Ruwaye
Ka watsa abincinka a kan ruwa, ka raba rabonka ko'ina, gama ba ka san wace masifa take zuwa ba. Duk wanda yake lura da iska ba zai taɓa yin shuka ba. Ka yi shuka safe da yamma, ka ji daɗin haske, ka tuna da kwanakin duhu masu zuwa, ka kuma sani Allah zai kawo ƙuruciya cikin shari'a.
11 1Ka jefa gurasarka a kan ruwaye, gama bayan kwanaki masu yawa za ka sāke samunta. 2Ka ba da rabo ga bakwai, ko ma ga takwas, gama ba ka san irin masifar da za ta auko wa ƙasa ba. 3Idan gizagizai suka cika, sai su zubo ruwan sama a kan ƙasa; in kuwa itace ya faɗi wajen kudu ko wajen arewa, inda ya faɗi, nan zai kwanta. 4Duk wanda yake kallon iska ba zai taɓa shuka ba, kuma duk wanda yake nazarin gizagizai ba zai taɓa girbi ba.
5Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba, ko yadda ake yin ƙasusuwa a cikin mahaifa ta mace mai ciki, haka ma ba za ka iya sanin aikin Allah ba, wanda yake yin kome.
6Ka shuka irinka da safe, da yamma kuma kada ka bar hannunka yă huta, gama ba ka san wanne zai yi nasara ba—wannan ko wancan—ko kuwa dukansu biyu za su yi kyau daidai.
Haske Yana da Daɗi
7Haske yana da daɗi, kuma yana da kyau ga idanu su ga rana.
8Saboda haka in mutum ya yi shekaru masu yawa, sai yă yi farin ciki a cikinsu duka; amma yă tuna da kwanakin duhu, gama za su yi yawa. Dukan abin da yake zuwa na wucewa ne.
9Ka yi farin ciki, kai saurayi, a cikin ƙuruciyarka, bari zuciyarka tă faranta maka rai a kwanakin ƙuruciyarka. Ka yi tafiya a hanyoyin zuciyarka da kuma a gaban idanunka; amma ka sani cewa saboda dukan waɗannan abubuwa Allah zai kawo ka ga hukunci.
10Saboda haka ka kawar da baƙin ciki daga zuciyarka, ka kau da zafi daga jikinka, gama ƙuruciya da farkon rayuwa na wucewa ne.