Yanzu a bugun takarda

Markus 4 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Mulkin Ubanmu Yana da Kunnuwan Ji

Yana koyarwa daga cikin jirgin ruwa, Yesu ya faɗi yadda mulkin Ubanmu yake zuwa: irin da ya faɗi a hanya, a kan dutse, cikin ƙaya da kuma ƙasa mai kyau; fitila; hatsin da yake girma sa'ad da manomi yake barci; ƙwayar mastad. Sa'an nan ya kwantar da hadirin da almajiransa suka tabbata zai nutsar da su.

Babi na 4.

Yesu ya sāke yin koyarwa a bakin teku. Taro mai girma ya taru kewaye da shi har ya shiga cikin jirgin ruwa da ke kan ruwa ya zauna, taron duka kuwa suna a gaɓar teku a kan tudu. Ya koya musu abubuwa masu yawa ta wurin misalai, a cikin koyarwarsa kuma ya ce musu,

“Ku saurara! Wani mai shuka ya fita don yă yi shuka. Yayinda yake shuka, sai waɗansu iri suka fāɗi a gefen hanya, tsuntsaye kuma suka zo suka cinye su. Waɗansu iri suka fāɗi a wurin dutse, inda ba ƙasa sosai, nan da nan kuwa suka tsira domin ƙasar ba ta da zurfi. Da rana ta fito, sai tsire-tsiren suka ƙone, kuma domin ba su da saiwa, sai suka yanƙwane. Waɗansu iri suka fāɗi cikin ƙayayuwa, sai ƙayayuwan suka yi girma suka shaƙe su, ba su kuwa ba da hatsi ba. Waɗansu iri kuwa suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka ba da hatsi da ya tsira, ya yi girma, ya kuma ba da riɓi talatin, da sittin, da ɗari na abin da aka shuka.” Sai ya ce, “Duk mai kunnuwan ji, yă ji.”

Sa'ad da yake shi kaɗai, sai waɗanda suke kewaye da shi, tare da Sha Biyun nan, suka tambaye shi game da misalan.

Ya ce musu, “An ba ku asirin Mulkin Ubanmu, amma ga waɗanda suke waje kuwa, kome yana zuwa ta wurin misalai, domin ‘su yi ta kallo amma kada su gane, su yi ta ji amma kada su fahimta, don kada su juyo a kuwa gafarta musu.’”

Ya ce musu, “Ashe, ba ku fahimci wannan misali ba? To, yaya za ku fahimci dukan misalan? Mai shuka yana shuka maganar. Waɗannan su ne waɗanda suke a gefen hanya inda aka shuka maganar: da zarar sun ji, sai Shaiɗan ya zo nan da nan ya ɗauke maganar da aka shuka a cikinsu. Haka ma waɗanda aka shuka a wurin dutse su ne waɗanda sukan ji maganar, nan da nan kuma su karɓe ta da farin ciki. Amma ba su da saiwa a cikinsu, suna dawwama na ɗan lokaci kaɗan ne; sa'ad da wahala ko tsanani ya zo saboda maganar, nan da nan sai su yi tuntuɓe su fāɗi. Waɗansu kuma su ne waɗanda aka shuka cikin ƙayayuwa. Waɗannan su ne waɗanda sukan ji maganar, amma damuwoyin wannan zamani, da ruɗin dukiya, da sha'awace-sha'awacen waɗansu abubuwa sukan shiga su shaƙe maganar, ta kuma kāsa ba da 'ya'ya. Waɗannan kuwa su ne waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau: sukan ji maganar, su karɓe ta, su kuma ba da 'ya'ya — riɓi talatin, da sittin, da ɗari.”

An Sa Haske domin yă Haskaka

Ya ce musu, “Ko akwai wanda yakan kawo fitila don yă sa ta a ƙarƙashin kwando ko gado — ba a kan madaurin fitila ba? Gama babu abin da yake a ɓoye sai dai a bayyana shi; babu kuma abin da yake a asirce sai dai yă fito fili. In wani yana da kunnuwan ji, yă ji.”

Ya ce musu, “Ku lura da abin da kuke ji. Mudun da kuke awo da shi, da shi za a awo muku — a kuma ƙara muku. Gama duk mai abu za a ƙara masa; wanda kuwa ba shi da shi, har ma abin da yake da shi za a karɓe masa.”

Iri Yana Girma da Kansa

Ya ce, “Mulkin Ubanmu yana kama da wani mutum da ya watsa iri a ƙasa. Dare da rana, barci ko farkawa, sai irin yă tsiro yă yi girma, ko da yake bai san yadda haka yake faruwa ba. Ƙasa takan ba da hatsi da kanta — da farko toho, sa'an nan kai, sa'an nan cikakkiyar ƙwaya a cikin kai. Amma sa'ad da hatsin ya nuna, nan da nan sai yă kai lauje, domin lokacin girbi ya yi.”

Ƙwayar Mustad

Ya ce, “Da me za mu kwatanta Mulkin Ubanmu, ko kuwa da wane misali za mu misalta shi? Yana kama da ƙwayar mustad, wadda ita ce mafi ƙanƙanta cikin dukan iri sa'ad da aka shuka ta a ƙasa. Amma da aka shuka ta, sai ta yi girma ta zama mafi girma cikin dukan tsire-tsiren lambu, ta kuma fitar da manyan rassa har tsuntsayen sama su iya yin sheƙunansu a inuwarta.”

Da misalai masu yawa irin waɗannan ya yi musu maganar, gwargwadon iyawarsu ta ji. Bai yi musu magana sai da misalai ba, amma a kaɗaice yakan bayyana wa almajiransa kome.

Yesu Ya Kwantar da Hadari

A ranar nan, da yamma ta yi, sai ya ce musu, “Mu haye zuwa gaɓar gaba.”

Suka bar taron, suka tafi da shi yadda yake, a cikin jirgin ruwa, waɗansu jiragen ruwa kuma suna tare da shi. Sai babban hadari mai ƙarfi ya tāso. Raƙuman ruwa suka dinga bugun jirgin, har jirgin ya kusa cika da ruwa. Amma Yesu yana barci a bayan jirgin a kan matashin kai. Suka tashe shi suka ce, “Malam, ba ka kula da cewa muna mutuwa ba?”

Sai ya tashi, ya tsawata wa iskar, ya ce wa tekun, “Ka natsu! Ka yi tsit!” Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit gaba ɗaya. Ya ce musu, “Don me kuke tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya?”

Suka tsorata ƙwarai, suka ce wa juna, “Wane ne wannan har iska da teku suna masa biyayya?”