Shirin Ubanmu domin Aure
Game da kisan aure Yesu ya koma ga halitta da abin da Ubanmu ya haɗa. Ya marabci yara, wani attajiri da ya ƙaunace shi kuma ya tafi yana baƙin ciki. Yakubu da Yahaya suka roƙi kujerun mulki, suka ji magana game da hidima da fansa. Bartimawus makaho ya yi ihu ya fi taron murya, ya kuma sami ganin gari.
10 1Ya bar wurin ya tafi yankin Yahudiya da ƙetaren Urdun; taron jama'a suka sāke taruwa gare shi, kuma kamar yadda ya saba, ya sāke koya musu.
2Waɗansu Farisiyawa suka zo don su gwada shi, suka tambaye shi, “Ya halatta mutum ya saki matarsa?”
3Ya amsa musu ya ce, “Mene ne Musa ya umarce ku?”
4Suka ce, “Musa ya ba da izini mutum ya rubuta takardar saki ya kore ta.”
5Yesu ya ce musu, “Saboda taurin zuciyarku ne ya rubuta muku wannan umarni. 6Amma tun farkon halitta, Ubanmu ya yi su namiji da mace. 7‘Saboda wannan dalili mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya manne wa matarsa, 8su biyun kuma su zama jiki ɗaya.’ Saboda haka ba sa ƙara zama biyu, sai dai jiki ɗaya. 9Saboda haka abin da Ubanmu ya haɗa, kada wani ya raba.”
10Da suka koma cikin gida, almajiran suka sāke tambayarsa game da wannan.
11Ya ce musu, “Duk wanda ya saki matarsa ya auri wata, ya yi mata zina, 12in kuwa ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina.”
Uba Ya Karɓi Yara
13Mutane suna kawo masa yara domin ya taɓa su, amma almajiran suka tsawata musu.
14Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi ya ce, “Ku bar yara su zo wurina; kada ku hana su, gama Mulkin Ubanmu na irin waɗannan ne. 15Lalle hakika, ina gaya muku, duk wanda bai karɓi Mulkin Ubanmu kamar yaro ba, ba zai taɓa shiga shi ba.”
16Sai ya rungume su, ya sa musu hannuwansa, ya albarkace su.
Mutumin da Yake da Yawa amma Ya Rasa Abu Ɗaya
17Yayinda yake kama hanya, sai wani mutum ya runtuma, ya durƙusa a gabansa, ya tambaye shi, “Malam managiyi, me zan yi domin in gaji rai madawwami?”
18Yesu ya ce masa, “Me ya sa kake ce da ni managiyi? Babu wani managiyi sai Ubanmu kaɗai. 19Ka san umarnai, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaidar ƙarya; kada ka yi zamba; ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’”
20Ya ce masa, “Malam, dukan waɗannan na kiyaye tun ƙuruciyata.”
21Yesu ya dube shi, ya kuma ƙaunace shi, ya ce, “Abu guda ka rasa, ka tafi, ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa talakawa—za ka kuwa sami dukiya a Sama—sa'an nan ka zo ka bi ni.”
22Da jin wannan magana, sai fuskarsa ta ɓaci, ya tafi yana baƙin ciki, gama yana da dukiya mai yawa.
23Yesu ya dudduba kewaye, ya ce wa almajiransa, “Yana da wuya ƙwarai mawadata su shiga Mulkin Ubanmu!”
24Almajiran suka yi mamakin maganarsa. Yesu ya sāke ce musu, “'Ya'yana, yana da wuya ƙwarai a shiga Mulkin Ubanmu! 25Raƙumi ya fi sauƙin shiga ta kafar allura da mai arziki ya shiga Mulkin Ubanmu.”
26Suka ƙara mamaki ƙwarai, suka ce wa juna, “To, wa zai iya samun ceto?”
27Yesu ya dube su ya ce, “Ga mutum, ba ya yiwuwa; amma ga Ubanmu ba haka ba ne, gama ga Ubanmu kome yana yiwuwa.”
28Bitrus ya fara ce masa, “Ga shi, mun bar kome mun bi ka.”
29Yesu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, babu wanda ya bar gida, ko 'yan'uwa maza, ko 'yan'uwa mata, ko uwa, ko uba, ko 'ya'ya, ko gonaki saboda ni da kuma saboda bishara,
30“wanda ba zai sami riɓi ɗari a yanzu ba, a wannan lokaci—gidaje, 'yan'uwa maza, 'yan'uwa mata, uwaye, 'ya'ya, gonaki, tare da tsanani—a kuma lokaci mai zuwa, rai madawwami. 31Amma da yawa na farko za su zama na ƙarshe, na ƙarshe kuma su zama na farko.”
Yesu Ya Sāke Yin Annabcin Mutuwarsa Sau na Uku
32A kan hanya zuwa Urushalima, Yesu yana tafiya a gabansu. Suka yi mamaki, waɗanda suke biyowa kuwa suka ji tsoro. Ya sāke ja da sha biyun gefe, ya fara gaya musu abin da yake shirin faruwa da shi,
33“Ga shi, muna haurawa zuwa Urushalima. Za a bashe Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman Attaura, za su yanke masa hukuncin kisa, su kuma bashe shi ga al'ummai. 34Za su yi masa ba'a, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi; bayan kwana uku kuma zai tashi.”
Girma ta Wurin Hidima
35Yakubu da Yahaya, 'ya'yan Zabadi, suka zo wurinsa suka ce, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙa.”
36Ya ce musu, “Me kuke so in yi muku?”
37Suka ce masa, “Ka bar mu mu zauna cikin ɗaukakarka, ɗaya a damanka, ɗaya kuma a hagunka.”
38Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Ko za ku iya shan kwaf da nake sha, ko a yi muku baftisma da baftismar da ake yi mini?”
39“Za mu iya,” suka ce. Yesu ya ce musu, “Kwaf da nake sha, za ku sha; baftismar da ake yi mini, za a yi muku, 40amma zama a damana ko a haguna ba nawa ba ne in bayar - na waɗanda aka shirya wa ne.”
41Da sauran goman suka ji haka, sai suka yi fushi da Yakubu da Yahaya.
42Yesu ya kira su wuri ɗaya ya ce, “Kun san cewa waɗanda ake ɗauka shugabannin al'ummai suna mulkinsu da ƙarfi, manyansu kuma suna nuna musu iko. 43Amma a cikinku ba haka ba ne. A maimakon haka, duk wanda yake so ya zama babba a cikinku, dole ne ya zama mai hidimarku, 44duk wanda kuma yake so ya zama na farko a cikinku, dole ne ya zama bawan kowa. 45Gama ko Ɗan Mutum ma bai zo domin a yi masa hidima ba, sai dai domin ya yi hidima, ya kuma ba da ransa fansar mutane da yawa.”
Bartimawus Ya Sami Ganin Gari
46Suka zo Yariko. Yayinda Yesu da almajiransa suke fita tare da taron jama'a mai yawa, sai ga wani makaho, Bartimawus ɗan Timawus, zaune yana bara a gefen hanya. 47Da ya ji cewa Yesu Banazare ne, sai ya fara ihu yana cewa, “Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” 48Mutane da yawa suka tsawata masa ya yi shiru, amma ya ƙara ta da murya yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”
49Yesu ya tsaya ya ce, “Ku kira shi.” Sai suka kira makahon, suka ce, “Ka yi ƙarfin hali! Ka tashi—yana kiranka.”
50Sai ya watsar da mayafinsa, ya yi wuf ya tashi, ya zo wurin Yesu.
51Yesu ya ce masa, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce masa, “Rabboni, ka sa in sāke gani.” a a v51 “Rabboni” hanya ce ta kiran Yesu daga zuciya kuma ta kashin kai — “malamina,” da ake faɗa cikin cikakken amana.
52Yesu ya ce masa, “Tafi; bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu a kan hanya.