Yanzu a bugun takarda

2 Sama'ila 12 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Uba Ya Aiki Natan wurin Dawuda

Natan ya ba da labarin wani mai arziki da ya saci ɗan ragon da matalauci yake ƙauna, kuma Dawuda ya hukunta kansa kafin ya ji kai ne mutumin. Takobi ba zai taɓa rabuwa da gidansa ba. Ya yi azumi saboda yaron da ke mutuwa, sa'an nan ya tashi ya yi sujada. Aka haifi Sulemanu, kuma Ubanmu yana ƙaunarsa.

Babi na 12.

Ubanmu ya aiki Natan wurin Dawuda. Sai ya zo ya ce, “Waɗansu mutum biyu suna zama a wani gari, ɗaya mai arziki ne, ɗaya kuma matalauci. Mai arzikin yana da garken tumaki da na shanu da yawan gaske, amma matalaucin ba shi da kome sai ƙaramar 'yar tunkiya guda ɗaya da ya saya. Ya yi renonta, ta kuma girma tare da shi da 'ya'yansa. Tana ci daga farantinsa, tana sha daga ƙoƙonsa, tana kwana a ƙirjinsa; ta zama kamar 'ya a gare shi. Sai wani matafiyi ya zo wurin mai arzikin, amma bai yarda ya ɗauko daga garkensa ko daga shanunsa don yă shirya wa baƙon da ya zo ba. Sai ya ɗauki 'yar tunkiyar matalaucin, ya shirya ta wa mutumin da ya zo wurinsa.”

Dawuda ya husata ƙwarai da mutumin, sai ya ce wa Natan, “Muddin Ubanmu yana raye, mutumin da ya yi haka ya cancanci a kashe shi! Dole yă biya diyyar tunkiyar har sau huɗu, domin ya yi haka bai kuwa ji tausayi ba.”

Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin! Ga abin da Ubanmu, Allah na Isra'ila, yake cewa: Na shafe ka ka zama sarki a bisa Isra'ila, na kuma cece ka daga hannun Sawulu.

“Na ba ka gidan maigidanka da matansa a hannunka, da gidan Isra'ila da na Yahuda. Da a ce wannan bai ishe ka ba, da na ƙara maka abubuwa masu yawa. Me ya sa ka rena maganata, kana aikata mugunta a gabana? Ka kashe Uriya mutumin Hitti da takobi, ka ƙwace matarsa ta zama taka, ka kuma kashe shi da takobin Ammonawa. Saboda haka yanzu takobi ba zai taɓa rabuwa da gidanka ba, domin ka rena ni, ka kuma ƙwace matar Uriya mutumin Hitti ta zama taka.

Ga abin da Ubanmu yake cewa: Zan jawo maka masifa daga cikin gidanka. A idanunka zan ɗauki matanka, in ba su ga wani da yake kusa da kai, shi kuwa zai kwana da su da rana tsaka. Ka yi wannan a ɓoye, amma ni zan yi wannan abu a gaban dukan Isra'ila, da rana tsaka.”

Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubanmu zunubi.” Sai Natan ya amsa ya ce, “Ubanmu kuma ya kawar da zunubinka; ba za ka mutu ba.”

Amma domin ka nuna wa Ubanmu reni ƙwarai ta wurin wannan aiki, ɗan da aka haifa maka zai mutu. Sa'an nan Natan ya tafi gida. Ubanmu kuwa ya bugi yaron da matar Uriya ta haifa wa Dawuda, sai ya kamu da ciwo mai tsanani. Dawuda ya roƙi Ubanmu saboda yaron. Ya yi azumi, ya shiga ɗaki, ya kwana a ƙasa dukan dare. Dattawan gidansa suka tsaya kusa da shi domin su tashe shi daga ƙasa, amma ya ƙi, bai kuwa ci abinci tare da su ba. A rana ta bakwai yaron ya mutu. Bayin Dawuda suka ji tsoron gaya masa cewa yaron ya mutu, gama suka ce, “Tun yaron yana da rai, mun yi masa magana bai kuwa saurare mu ba. Yaya za mu ce masa yaron ya mutu? Watakila yă cuci kansa.”

Amma Dawuda ya ga bayinsa suna raɗa, sai ya gane cewa yaron ya mutu. Sai ya tambaya, “Yaron ya mutu ne?” Suka ce, “Ya mutu.”

Dawuda ya tashi daga ƙasa, ya yi wanka, ya shafa mai, ya canja tufafinsa. Ya shiga gidan Ubanmu ya yi sujada, sa'an nan ya koma gida, bisa ga roƙonsa suka kawo masa abinci, ya kuwa ci. Bayinsa suka ce masa, “Mene ne wannan da ka yi? Tun yaron yana da rai, ka yi azumi kana kuka; yanzu da ya mutu, sai ka tashi kana ci.”

Ya ce, “Tun yaron yana da rai, na yi azumi na yi kuka, ina cewa a raina, ‘Wa ya sani? Watakila Ubanmu yă yi mini alheri yă bar yaron yă rayu.’ Amma yanzu ya mutu. Don me zan yi azumi? Zan iya mayar da shi kuma? Zan tafi wurinsa, amma shi ba zai komo wurina ba.”

Sa'an nan Dawuda ya ta'azantar da matarsa Batsheba. Ya tafi wurinta ya kwana da ita, sai ta haifi ɗa. Ya raɗa masa suna Sulemanu. Ubanmu kuwa ya ƙaunace shi, sai ya aika da saƙo ta hannun annabi Natan, shi kuwa ya raɗa masa suna Yedidiya, saboda Ubanmu. a a v25 Yedidiya yana nufin “ƙaunataccen Ubanmu” — sunan yana nuna ƙaunar da Ubanmu ya riga ya sa a kan yaron.

Dawuda Ya Kame Rabba

A lokacin kuwa Yowab yana yaƙi da Rabba ta Ammonawa, sai ya kame birnin sarauta. Yowab ya aiki manzanni wurin Dawuda ya ce, “Na yi yaƙi da Rabba, na kuma kame magudanar ruwanta. Yanzu ka tara sauran sojoji, ka kewaye birnin, ka kuma kame shi. In ba haka ba, ni zan kame shi, a kuma raɗa masa sunana.”

Dawuda ya tara dukan sojoji, ya tafi Rabba, ya fāɗa mata, ya kuma kame ta. Ya ɗauki kambi daga kan sarkinsu—wajen fam saba'in da biyar na zinariya saye da dutse mai daraja—aka kuwa sa shi a kan Dawuda. Ya kwashe ganima mai yawa daga birnin. Ya fitar da mutanen da suke can, ya sa su aiki da zarto, da sungumin ƙarfe, da gatarin ƙarfe, ya kuma sa su yin aiki a tanderun tubali. Haka kuwa ya yi wa dukan biranen Ammonawa. Sa'an nan Dawuda da dukan sojoji suka koma Urushalima.