Yanzu a bugun takarda

Karin Magana 26 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Wawa Yakan Sāke Wautarsa

Kusan jerin irin mutane uku ne. Wawa, wanda ba za a iya girmama shi ko ɗaukarsa aiki ko warkar da shi ba; malalaci, mai jujjuyawa a gadonsa kamar ƙofa a kan madogararta; da mayaudari, wanda yakan yi wa mutum rauni sa'an nan ya ce wasa kawai yake yi. Duk wanda ya haƙa rami zai fāɗa ciki.

Babi na 26.

Kamar ƙanƙara a lokacin rani da kuma ruwan sama a lokacin girbi, haka girmamawa ba ta dace da wawa ba. Kamar gwara mai firfita fikafikai ko alallaka mai sheƙawa, haka la'anar da ba ta cancanta ba, ba ta sauka. Bulala domin doki, linzami domin jaki, sanda kuma domin bayan wawaye. Kada ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, don kada kai ma ka zama kamarsa. Ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, don kada yă zama mai hikima a idanunsa. Duk wanda ya aika da saƙo ta hannun wawa, yana yanke ƙafafunsa ne, yana kuma shan ta'adi. Kamar ƙafafun gurgu da suke rataye a banza, haka karin magana yake a bakin wawaye. Kamar daure dutse a majajjawa, haka yake ga wanda yake ba wawa girma. Kamar ƙayar da take hannun mashayi, haka karin magana yake a bakin wawaye. Kamar maharbi da yake jiyar da kowa ciwo, haka yake ga wanda yake ɗaukar wawa ko kuwa ya ɗauki duk mai wucewa aiki. Kamar yadda kare yake komawa ga amansa, haka wawa yakan sāke wautarsa. Ka ga wani mai hikima a idanunsa? Akwai sauran bege ga wawa fiye da shi.

Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya! Zaki a cikin titi!” Kamar yadda ƙofa take juyawa a ƙyaurenta, haka rago yake juyawa a kan gadonsa. Rago yakan sa hannunsa a cikin kwano; yakan gaji da mayar da shi bakinsa. Rago yana ganin kansa mai hikima fiye da mutum bakwai masu amsa cikin hikima.

Kamar kama kare a kunnuwa, haka yake ga mai wucewa da yake tsoma baki a faɗar da ba tasa ba.

Kamar mahaukaci da yake harbin cinnuka, da kibau, da mutuwa, haka yake ga wanda yake ruɗin maƙwabcinsa yana cewa, “Wasa nake yi kawai!”

In ba itace, wuta takan mutu, in kuma ba mai gulma, faɗa takan kwanta. Kamar gawayi ga garwashi da itace ga wuta, haka mai neman faɗa yake kunna husuma. Kalmomin mai gulma suna kamar zaƙaƙƙun loma; sukan nutse har cikin zuciya.

Kamar sheƙi mai walƙiya a jikin tukunyar ƙasa, haka leɓɓa masu zaƙi suke tare da mugunyar zuciya. Maƙiyi yakan ɓad da kansa da leɓɓansa, amma a zuciyarsa yana riƙe da ruɗu. Ko da yana magana da daɗi, kada ka gaskata shi, gama abubuwan ƙyama bakwai sun cika zuciyarsa. Ko da yake an ɓoye ƙiyayyarsa da ruɗu, za a tone muguntarsa a cikin taro. Duk wanda ya haƙa rami zai fāɗa a ciki, dutse kuma yakan birkice ya koma kan wanda ya mirgine shi. Harshe mai ƙarya yana ƙin waɗanda yake murƙushewa, baki mai daɗin zaƙi kuma yakan kawo hallaka.