Yanzu a bugun takarda

Ayuba 21 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Ayuba Ya Amsa: Me Ya Sa Mugaye Suke Wadata?

Ayuba ya amsa da shaidar da abokansa suka ƙi kula da ita: mugaye sukan tsufa su yi ƙarfi, 'ya'yansu suna rawa, sukan kuma mutu cikin salama bayan sun ce wa Allah ya rabu da su. Mai wadata da mai baƙin ciki duka suna kwanciya cikin ƙura. Ta'aziyyarsu, in ji shi, ƙarya ce.

Babi na 21.

Sai Ayuba ya amsa ya ce, “Ku saurari maganata da kyau, kuma bari wannan yă zama ta'aziyyar da kuke ba ni. Ku haƙura da ni yayin da nake magana, bayan na gama magana kuma, sai ku ci gaba da yin ba'a. Ni dai, ina kai ƙarata ga mutum ne kawai? Me zai hana haƙurina yă ƙare? Ku dube ni, ku kuma yi mamaki, ku sa hannunku a bakinku. Sa'ad da na tuna da wannan, sai tsoro ya kama ni, jijjiga kuma ta kama jikina. Me ya sa mugaye suke ci gaba da rayuwa, suna tsufa suna kuma ƙaruwa da iko? 'Ya'yansu suna zaune lafiya tare da su a gabansu, zuriyarsu kuma a gaban idanunsu. Gidajensu suna cikin aminci, babu tsoro, kuma sandar Allah ba ta fāɗuwa a kansu. Bijiminsu yakan yi barbara ba ya kāsawa ba; saniyarsu takan haifa ba tā zubar da ciki ba. Suna sakin ƙananan 'ya'yansu su yi ta yawo kamar garke, 'ya'yansu kuma suna ta tsalle-tsalle. Suna rera waƙa da ganga da molo, suna kuma shagali da amon sarewa. Suna ƙarasa kwanakinsu cikin wadata, da salama kuma suke gangarawa zuwa kabari. Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu! Ba mu da sha'awar sanin hanyoyinka. Wane ne Maɗaukaki, da za mu bauta masa? Wace riba kuma za mu samu in muka yi masa addu'a?’ Amma wadatarsu ba ta hannunsu take ba; shawarar mugaye kam, ba na so in sa hannu a cikinta. Sau nawa ake kashe fitilar mugaye? Sau nawa masifa take aukawa a kansu? Sau nawa Allah yake rabon azaba cikin fushinsa? Sau nawa suke kamar ciyawar da iska take kaɗawa, kamar yayin da hadari yake share shi? Kuna cewa, ‘Allah yana ajiye hukuncin mutum wa 'ya'yansa.’ Bari yă sāka wa mutumin kansa, domin yă san haka. Bari idanunsa su ga hallakarsa, bari kuma yă sha fushin Maɗaukaki. Gama me ya dama shi game da iyalinsa a bayansa, sa'ad da aka datse watanninsa? Ko wani zai iya koya wa Allah sani, tun da shi ne yake shari'anta waɗanda suke can sama? Wani yakan mutu cikin cikakken ƙarfi, cikin natsuwa da aminci gaba ɗaya, jikinsa cike da ƙoshin lafiya, ɓargon ƙasusuwansa kuma yana da danshi. Wani kuma yakan mutu da ran ɗaci, bai taɓa ɗanɗana wani abu mai kyau ba. Tare suke kwanciya cikin ƙura, tsutsotsi kuma su rufe su biyu. Ga shi, na san tunaninku, da makircin da kuke yi domin ku cuce ni. Gama kuna cewa, ‘Ina gidan mai girma yanzu? Ina tentin da mugu yake zama?’ Ba ku taɓa tambayar masu tafiya a kan hanya ba? Ba za ku yarda da shaidar da suke bayarwa ba, wato akan tsira da mugu a ranar masifa, akan kuɓutar da shi a ranar fushi? Wane ne yake tunkararsa gaba da gaba saboda halinsa, wane ne kuma yake sāka masa saboda abin da ya aikata? Akan kai shi kabari, a kuma yi tsaron kabarinsa. Turɓayar kwari tana da daɗi a gare shi; kowa yana binsa, waɗanda suka riga shi kuma ba su ƙidayuwa. To yaya za ku iya ta'azantar da ni da maganganun banza? Amsoshinku ba kome ba ne illa ƙarya.”