Hawaye Babu Mai Ta'aziyya
Mai Hadishi ya ga zalunci ba mai ta'aziyya, ya ce matattu sun fi masu rai jin daɗi. Kishi ne yake motsa yawancin aiki. Duk da haka biyu sun fi ɗaya: wani da zai ɗaga ka sa'ad da ka fāɗi, ya ji maka ɗumi, ya tsaya tare da kai. Ko sarkin da aka fi so ba da daɗewa ba ba a bukatarsa.
4 1Na sāke dubawa na ga dukan zalunci da ake yi a duniya: waɗanda ake zaluntarsu suna kuka, babu mai ta'aziyyarsu; masu zaluntarsu suna riƙe da iko, duk da haka babu mai ta'aziyya. 2Saboda haka na ce matattu, waɗanda suka riga suka mutu, sun fi masu rai, waɗanda suke da rai har yanzu, farin ciki. 3Wanda bai riga ya zo duniya ba, wanda bai ga muguntar da ake yi a duniya ba, ya fi su biyu. 4Na ga dukan aiki da gwaninta sun fito ne daga kishin da mutum yake yi wa maƙwabcinsa. Wannan ma abin wucewa ne, kamar bin iska. 5Wawa yakan naɗe hannuwansa, yă kuma lalatar da kansa. 6Tafin hannu ɗaya da kwanciyar rai ya fi tafin hannu biyu da wahala da bin iska.
7Na sāke ganin wani abu mai wucewa a duniya:
8Akwai mutum shi kaɗai, babu abokinsa, babu ɗa ko ɗan'uwa; aikinsa ba shi da iyaka, duk da haka idanunsa ba sa ƙoshi da wadata. Yana tambaya, “Wa nake yi wa aiki, ina hana kaina jin daɗi?” Wannan ma iska ce kawai — mugun aiki ne.
9Biyu sun fi ɗaya, domin suna da sakamako mai kyau don aikinsu: 10In ɗaya ya faɗi, ɗayan yă ɗaga shi. Amma kaiton wanda ya faɗi shi kaɗai, babu mai ɗaga shi. 11Haka kuma, in biyu suka kwanta tare, za su ji ɗumi. Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi shi kaɗai? 12Mutum ɗaya shi kaɗai za a iya rinjaye shi, amma biyu za su iya tsayayya. Igiya mai zare uku ba a tsinke ta da sauri.
Saurayi Mai Hikima da Sarki Wawa
13Saurayi matalauci mai hikima ya fi tsohon sarki wawa wanda ya kāsa jin gargaɗi. 14Mai yiwuwa saurayin ya fito daga kurkuku ya zama sarki, ko kuwa an haife shi matalauci a cikin mulkin nan. 15Na ga dukan masu rai da suke zirga-zirga a duniya suna bin saurayin, wanda zai gāji sarki. 16Yawan mutanen da suka gabace shi ba shi da iyaka. Duk da haka waɗanda suka zo daga baya ba su ji daɗinsa ba. Wannan ma abin wucewa ne, kamar bin iska.