Mafi Girma a Cikinsu
Kowace baiwa da suke gasa a kanta — harsuna, annabci, sani, bangaskiyar da take kawar da duwatsu, har ma bayar da kome — ba ta da amfani ba tare da ƙauna ba. Ƙauna tana da haƙuri, ba ta riƙe lissafin laifi, kuma tana dawwama fiye da baye-baye, waɗanda za su ƙare sa'ad da muka gani fuska da fuska.
13 1Idan ina magana da harsunan mutane da na mala'iku, amma ba ni da ƙauna, ni ganga mai ƙara ne kawai, ko kuge mai amo. 2Idan ina da baiwar annabci, na kuma fahimci dukan asirai da dukan sani, ina kuma da cikakkiyar bangaskiya har in iya motsa duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne. 3Idan na ba da dukan abin da nake da shi, na kuma ba da jikina domin in yi fahariya, amma ba ni da ƙauna, ba na amfana da kome ba.
4Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta fahariya, ba ta nuna girman kai. 5Ba ta rashin ladabi, ba ta neman nata kaɗai, ba ta saurin fushi, ba ta tuna laifofin da aka yi mata. 6Ƙauna ba ta farin ciki da mugunta, sai dai tana murna tare da gaskiya. 7Kullum tana kāriya, kullum tana amincewa, kullum tana bege, kullum tana jimrewa.
8Ƙauna ba ta taɓa kāsawa ba. Amma annabce-annabce za su ƙare, harsuna za su daina, sani kuma zai ƙare. 9Gama muna sani a sashe, muna kuma annabci a sashe, 10amma sa'ad da cikakke ya zo, sai abin da yake a sashe ya ɓace. 11Sa'ad da nake yaro, nakan yi magana kamar yaro, nakan yi tunani kamar yaro, nakan yi hankali kamar yaro. Amma da na zama babba, sai na bar halayen ƙuruciya. 12Gama yanzu muna ganin siffa marar fito-na-fito a cikin madubi; amma a lokacin za mu gani fuska da fuska. Yanzu ina sani a sashe; amma a lokacin zan sani sarai, kamar yadda aka san ni sarai. 13Yanzu fa waɗannan uku sun dawwama: bangaskiya, da bege, da ƙauna. Amma mafi girma a cikinsu ƙauna ce.