Baye-bayen da suke Gina Iyali
Harsuna ba tare da fassara ba suna gina mai magana kaɗai, saboda haka annabci ya fi: baƙon da ya shigo ya kamata a tona asirin zuciyarsa ya fāɗi yana yin sujada. Kome a cikin taron ana auna shi ko yana ginawa, a kuma yi shi bisa tsari, domin Ubanmu ba mai hargitsi ba ne.
14 1Ku biɗi ƙauna, ku kuma yi marmarin baye-bayen Ruhu, musamman ma ku yi annabci. 2Duk wanda yake magana da wani harshe, ba ga mutane yake magana ba, sai dai ga Ubanmu, domin ba wanda yake gane shi, yana faɗin asirai ne cikin Ruhu. 3Amma wanda yake annabci, ga mutane yake magana domin gina su, da ƙarfafa su, da ta'aziyya. 4Wanda yake magana da wani harshe yana gina kansa ne, amma wanda yake annabci yana gina ikkilisiya ne. 5Ina so dukanku ku yi magana da harsuna, amma gara ku yi annabci. Wanda yake annabci ya fi wanda yake magana da harsuna, sai dai in ya fassara, domin a gina ikkilisiya.
6To,'yan'uwa, in na zo wurinku ina magana da harsuna, wane amfani zan yi muku, in ban yi muku magana ta wahayi, ko ta sani, ko ta annabci, ko ta koyarwa ba? 7Haka ma abubuwa marasa rai da suke fitar da ƙara, ko sarewa ce ko garaya, in ba a bambanta karin waƙar ba, yaya za a san abin da ake kaɗawa? 8In kuma ƙaho ya busa busar da ba a fahimta ba, wa zai shirya don yaƙi? 9Haka ku ma, in harshenku bai faɗi kalma a fili ba, yaya za a san abin da ake faɗi? Za ku dai zama kuna magana ne cikin iska. 10Babu shakka akwai harsuna iri iri da yawa a duniya, kuma babu ko ɗaya da ba shi da ma'ana. 11To, in ban san ma'anar wannan ƙara ba, zan zama baƙo ga mai maganar, shi kuma mai maganar ya zama baƙo gare ni. 12Haka ku ma, da yake kuna marmarin baye-bayen Ruhu, sai ku nema ku yi fice cikin ƙarfafa ikkilisiya. 13Saboda haka, wanda yake magana da wani harshe, ya yi addu'a domin ya iya fassara shi. 14Domin in na yi addu'a da wani harshe, ruhuna ne yake addu'a, amma hankalina ba ya amfana.
15To, me zan yi? Zan yi addu'a da ruhuna, in kuma yi addu'a da hankalina. Zan yi waƙar yabo da ruhuna, in kuma yi waƙar yabo da hankalina. 16In ba haka ba, in kana yabo da ruhu kaɗai, yaya baƙon da yake zaune a wurin zai ce “Amin” ga godiyarka, da yake bai san abin da kake faɗi ba? 17Ko da kana ba da godiya yadda ya kamata, duk da haka ba a gina ɗayan ba. 18Ina gode wa Ubanmu domin ina magana da harsuna fiye da ku duka. 19Amma a cikin ikkilisiya, gara in faɗi kalmomi biyar da hankalina domin in koya wa waɗansu, da in faɗi kalmomi dubu goma da wani harshe.
20'Yan'uwa, kada ku yi tunani kamar yara. Game da mugunta ku zama jarirai, amma game da tunani ku zama balagaggu.
21An rubuta a cikin Shari'a cewa, “Da baƙin harsuna da leɓunan baƙi zan yi wa wannan jama'a magana, duk da haka ba za su saurare ni ba,” in ji Ubanmu.
22Saboda haka harsuna alama ce, ba ga masu bi ba, sai dai ga marasa bi. Annabci kuwa alama ce, ba ga marasa bi ba, sai dai ga masu bi. 23To, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da harsuna, waɗansu baƙi ko marasa bi kuwa suka shigo, ba za su ce kun haukace ba? 24Amma in duka suna annabci, sai wani marar bi ko baƙo ya shigo, duka za su kashe masa zuciya, duka kuma za su bincike shi, 25asiran zuciyarsa su tonu. Sa'an nan sai ya fāɗi rubda ciki, ya yi wa Ubanmu sujada, yana shaidawa cewa lalle Ubanmu yana tare da ku.
Sujada cikin Tsari da ya Dace
26To,'yan'uwa, me za mu ce? Sa'ad da kuka taru, kowa yana da waƙa, ko koyarwa, ko wahayi, ko harshe, ko fassara. Bari a yi dukan wannan domin gina juna. 27In wani yana magana da wani harshe, mutum biyu, ko mafi yawa uku, kowa a jere, sai wani kuma ya fassara. 28In kuma babu mai fassara, sai mai maganar ya yi shiru a cikin ikkilisiya, yana magana da kansa kaɗai da kuma Ubanmu. 29Bari annabawa biyu ko uku su yi magana, sauran kuma su auna da kyau abin da aka faɗa. 30In kuma wahayi ya zo wa wani da yake zaune a wurin, sai wanda yake magana da fari ya yi shiru. 31Gama dukanku kuna iya yin annabci ɗaya bayan ɗaya, domin kowa ya koya, kowa kuma ya sami ƙarfafa. 32Ruhohin annabawa kuma suna ƙarƙashin ikon annabawa. 33Gama Ubanmu ba Allah ne na rikici ba, sai dai na salama, yadda yake a dukan ikkilisiyoyin tsarkaka. 34Mata su yi shiru a cikin ikkilisiyoyi, domin ba a yardar musu su yi magana ba, sai dai su kasance ƙarƙashin iko, yadda Shari'a ma take faɗi. a a v34 Waɗansu rubuce-rubucen hannu sun sa ayoyi 34-35 bayan aya ta 40. 35In kuwa suna son su koyi wani abu, sai su tambayi mazansu a gida, gama abin kunya ne mace ta yi magana a cikin ikkilisiya. 36Ko daga wurinku ne maganar Ubanmu ta fara fitowa? Ko gare ku kaɗai ta zo? 37Duk wanda yake ganin kansa annabi ne, ko mai bin Ruhu, sai ya gane cewa abin da nake rubuta muku umarnin Ubangiji ne. 38Amma in wani bai kula da wannan ba, shi ma ba za a kula da shi ba.
39Saboda haka,'yan'uwana, ku yi marmarin yin annabci, kada kuma ku hana yin magana da harsuna. 40Amma bari a yi kome a kan tsari da kuma yadda ya dace.