Babu Abin da Yake Ɓoye ga Ubanmu
Gargaɗi game da munafunci da kwaɗayi, wanda wani manomi ya tabbatar, wanda ya gina manyan rumbuna a daren da zai mutu. Sa'an nan akasin haka: gwarare, hankaki da furannin bisa, da Ubanmu yana sane da abin da kuke bukata. An gaya wa bayi su kasance a shirye da farke, Yesu kuma ya ce ya kawo rarrabuwa.
12 1A sa'an nan, da dubban mutane suka taru suna tattake juna, sai Yesu ya fara magana da almajiransa da farko, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato munafunci. 2Babu abin da aka ɓoye da ba za a bayyana shi ba, babu kuma asirin da ba za a sani ba. 3Saboda haka duk abin da kuka faɗa cikin duhu za a ji shi cikin haske, abin da kuka yi raɗa a cikin ɗakuna na ɓoye kuma za a yi shelarsa daga kan rufin gidaje.
4“Ina gaya muku, abokaina, kada ku ji tsoron waɗanda suke kashe jiki, bayan haka kuma ba su da sauran abin da za su iya yi. 5Zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa, ku ji tsoron wanda, bayan ya kashe, yana da ikon jefa ku cikin jahannama. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa.
6Ba a sayar da gwarare biyar a kan ƙananan kuɗi biyu ba? Duk da haka ba a manta da ko ɗayansu a gaban Ubanmu ba. a a v6 Assariyon ƙaramin kuɗin tagulla ne mai ƙaramar daraja — biyu daga cikinsu sukan sayi gwarare biyar. 7Amma har gashin kanku duk an ƙididdige su. Kada ku ji tsoro, kun fi gwarare masu yawa daraja.
8“Ina kuma gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum shi ma zai shaida shi a gaban mala'ikun Ubanmu. 9Amma wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, za a yi mūsun saninsa a gaban mala'ikun Ubanmu. 10Duk wanda ya faɗi magana gāba da Ɗan Mutum za a gafarta masa, amma wanda ya yi saɓo gāba da Ruhu Mai Tsarki ba za a gafarta masa ba. 11Sa'ad da suka kawo ku a gaban majami'u, da masu mulki, da masu iko, kada ku damu yadda za ku kāre kanku ko abin da za ku faɗa, 12gama Ruhu Mai Tsarki zai koya muku a daidai wannan sa'a abin da ya kamata ku faɗa.”
Wawan da Ya Manta da Ubanmu
13Sai wani a cikin taron ya ce masa, “Malam, ka gaya wa ɗan'uwana yă raba gādo da ni.”
14Amma Yesu ya ce masa, “Kai mutum, wa ya naɗa ni alƙali ko mai sulhu a kanku?” 15Ya ce musu, “Ku yi hankali! Ku kiyaye kanku daga kowane irin kwaɗayi, domin rayuwar mutum ba ta dangana ga yawan abin da yake da shi ba.”
16Sai ya ba su wani misali, ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani mai kyau.
17Ya yi tunani a ransa, ‘Me zan yi? Ba ni da wurin da zan ajiye hatsina.’ 18Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi, zan rushe rumbunana, in gina waɗanda suka fi girma, in ajiye dukan hatsina da kayana a can.’ 19‘Zan kuma ce wa raina, “Kai rai, kana da tarin abu da aka ajiye na shekaru masu yawa, ka huta, ka ci, ka sha, ka ji daɗin rayuwa.”’
20Amma Ubanmu ya ce masa, ‘Kai wawa! A daren nan za a karɓi ranka daga gare ka. To, abin da ka shirya, na wa zai zama?’ 21Haka yake faruwa da duk wanda ya tara wa kansa dukiya amma ba shi da arziki ga Ubanmu.”
Ubanmu Ya San Abin da Kuke Bukata
22Sa'an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, wato abin da za ku ci, ko game da jikinku, wato abin da za ku sa. 23Gama rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24Ku dubi hankaki, ba sa shuka ko girbi, ba su da ɗaki ko rumbu, duk da haka Ubanmu yana ciyar da su. Ku fa kun fi tsuntsaye daraja ƙwarai! 25Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara ko sa'a ɗaya a rayuwarsa? 26In har ba za ku iya yin ƙaramin abu haka ba, don me kuke damuwa game da sauran? 27Ku lura yadda furanni suke girma, ba sa wahala, ba sa kaɗi. Duk da haka ina gaya muku, ko Sulemanu a cikin dukan darajarsa bai yi ado kamar ɗayansu ba. 28In haka Ubanmu yake tufatar da ciyawar jeji — wadda take nan yau, gobe kuma a jefa ta cikin murhu — balle fa ku, zai tufatar da ku, ku masu ƙarancin bangaskiya?
29Kada ku nemi abin da za ku ci ko abin da za ku sha, kada kuma ku damu. 30Gama dukan al'umman duniya suna neman waɗannan abubuwa, Ubanku kuwa ya san kuna bukatarsu. 31A maimakon haka, ku nemi Mulkin Ubanmu, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa.
32“Kada ku ji tsoro, ku ƙaramin garke, gama Ubanku ya ji daɗin ba ku mulki. 33Ku sayar da kayanku ku ba da sadaka ga matalauta. Ku yi wa kanku jakunkunan kuɗi marasa tsufa — dukiya marar ƙarewa a Sama, inda ɓarawo ba ya zuwa kusa, asu kuma ba ya ɓatarwa. 34Gama inda dukiyarku take, a can ne zuciyarku ma za ta kasance.
Ku Kasance a Shirye Sa'ad da Maigida Zai Dawo
35“Ku kasance a sanye da shiri don hidima, ku kuma bar fitilunku suna ci, 36kamar bayin da suke jiran dawowar maigidansu daga bikin aure, domin sa'ad da ya zo ya ƙwanƙwasa, nan da nan su buɗe masa ƙofa. 37Masu albarka ne bayin da maigida ya iske suna a faɗake sa'ad da ya zo. Lalle hakika, ina gaya muku, zai sa wa kansa shiri don hidima, yă zaunar da su a tebur, yă zo yă yi musu hidima. 38Ko ya zo da tsakar dare ko kafin gari ya waye, masu albarka ne bayin nan in ya iske su a shirye. 39Ku san wannan, da maigida ya san sa'ar da ɓarawo zai zo, da bai bar a fasa gidansa ba. 40Ku ma, dole ku kasance a shirye, gama Ɗan Mutum yana zuwa a sa'ar da ba ku zata ba.”
41Bitrus ya ce, “Ubangiji, ka faɗi wannan misali dominmu ne, ko domin kowa ne?”
42Ubangiji ya amsa ya ce, “Wane ne amintaccen wakili mai hikima, wanda maigida zai sa yă lura da bayin gidansa, domin yă riƙa ba su rabonsu a daidai lokaci? 43Mai albarka ne bawan nan da maigida ya iske yana yin haka sa'ad da ya dawo. 44Lalle hakika, ina gaya muku, zai sa shi yă lura da dukan dukiyarsa. 45Amma in bawan nan ya ce a ransa, ‘Maigidana ya yi jinkirin dawowa,’ sai ya fara dūkan bayi, maza da mata, yana ci, yana sha, yana kuma buguwa. 46Maigidan bawan nan zai zo a ranar da bai zata ba, a sa'ar da bai sani ba, yă yanka shi biyu, yă ba shi wuri a cikin marasa aminci. 47Bawan da ya san nufin maigidansa amma bai yi shiri ba, bai kuwa aikata shi ba, za a yi masa dūka mai yawa. 48Amma wanda bai sani ba, duk da haka ya yi abin da ya cancanci hukunci, za a yi masa dūka kaɗan. Duk wanda aka ba shi abu mai yawa, za a nemi mai yawa daga gare shi, wanda kuma aka danƙa wa abu mai yawa, za a nema a hannunsa fiye da haka.
Ɗa Yana Kawo Wuta, Ba Salama Ba
49“Na zo ne domin in jefa wuta a duniya, kuma da ma a ce ta riga ta kama! 50Amma ina da baftisma da zan sha, kuma yadda nake cikin ƙunci sai an cika ta! 51Kuna tsammani na zo ne domin in kawo salama a duniya? A'a, ina gaya muku, sai dai rabuwa. 52Daga yanzu za a sami mutum biyar a gida ɗaya a rarrabe — uku gāba da biyu, biyu kuma gāba da uku. 53Za su rabu — uba gāba da ɗa, ɗa kuma gāba da uba, uwa gāba da 'ya, 'ya kuma gāba da uwa, suruka gāba da matar ɗanta, matar ɗa kuma gāba da surukarta.”
54Ya kuma ce wa taron, “Sa'ad da kuka ga girgije yana tasowa daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Ruwa yana zuwa,’ sai kuwa haka ya kasance.
55Sa'ad da kuma iskar kudu ta hūra, sai ku ce, ‘Za a yi zafi,’ sai kuwa haka ya zama. 56Ku munafukai! Kun san yadda za ku karanta yanayin ƙasa da sama. Don me ba ku san yadda za ku karanta wannan zamani na yanzu ba?
57“Don me kuma ba ku shar'anta wa kanku abin da yake daidai ba? 58Sa'ad da kake tafiya tare da mai ƙararka zuwa gaban mai shari'a, ka yi ƙoƙari ku sasanta a hanya, in ba haka ba zai iya jā ka zuwa gaban alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, ɗan sanda kuma yă jefa ka cikin kurkuku. 59Ina gaya maka, ba za ka fito ba sai ka biya har kwabo na ƙarshe.”