Ku Tuba Kafin Lokaci Yă Ƙure
Da aka gaya masa game da kisan da Bilatus ya yi, Yesu ya ƙi tunanin cewa waɗanda aka kashe sun fi kowa zunubi, ya ce ku tuba. Itacen ɓaure marar 'ya'ya ya sami ƙarin shekara ɗaya. Ya 'yanta wata mace da ta tanƙware a ranar Asabar ta kuma ɗaukaka Ubanmu, ya yi gargaɗi cewa ƙofar ƙunƙunta ce, ya kuma yi kuka.
13 1A daidai lokacin nan, sai waɗansu mutane suka gaya masa game da mutanen Galili, waɗanda Bilatus ya gauraya jininsu da hadayunsu.
2Sai ya amsa musu ya ce, “Kuna tsammani waɗannan mutanen Galili sun fi dukan sauran mutanen Galili zunubi ne, da yake sun sha wahalar nan? 3A'a, ina gaya muku; sai dai in ba ku tuba ba, dukanku za ku hallaka haka ma. 4Ko kuwa waɗancan mutum goma sha takwas da suka mutu sa'ad da hasumiyar Silowam ta faɗo a kansu — kuna tsammani sun fi kowa da kowa a Urushalima laifi ne? 5A'a, ina gaya muku; sai dai in ba ku tuba ba, dukanku za ku hallaka haka nan.”
6Sa'an nan ya ba su wannan misali, “Wani mutum yana da itacen ɓaure da aka shuka a gonar inabinsa. Ya zo yana neman 'ya'ya a kansa, amma bai samu ba. 7Sai ya ce wa mai lambun, ‘Duba, shekara uku ke nan ina zuwa neman 'ya'ya a kan itacen ɓauren nan, amma ban samu ba. Ka sare shi — don me zai yi ta ɓata ƙasa a banza?’ 8Amma ya amsa masa ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ka ƙyale shi bana ma, sai na gina kewayensa na kuma zuba taki. 9Sa'an nan in ya ba da 'ya'ya a shekara mai zuwa, da kyau; in kuwa bai yi ba, sai ka sare shi.’”
An 'Yantar da Wata 'Ya a Ranar Asabaci
10To, yana koyarwa a wata majami'a a ranar Asabaci. 11A daidai lokacin nan, ga wata mace da wani ruhu ya raunana ta shekara goma sha takwas, tana tanƙware, ba za ta iya mikewa sam ba.
12Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, “Mace, an 'yantar da ke daga naƙasarki.”
13Ya ɗora hannuwansa a kanta, nan take kuwa ta miƙe ta kuma ɗaukaka Ubanmu.
14Amma shugaban majami'ar ya yi fushi domin Yesu ya warkar a ranar Asabaci, sai ya ce wa taron, “Akwai kwana shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo a warkar da ku a cikin kwanakin nan, ba a ranar Asabaci ba.”
15Sai Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Ku munafukai! Ashe, kowannenku ba ya kunce saniyarsa ko jakinsa daga wurin sa a ranar Asabaci yă fitar da shi yă kai shi shan ruwa? 16To, wannan 'yar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya daure shekara goma sha takwas, ba za a 'yantar da ita daga daurin nan a ranar Asabaci ba?”
17Yayinda yake faɗin waɗannan abubuwa, dukan maƙiyansa suka ji kunya, dukan taron kuwa suka yi farin ciki saboda dukan abubuwa masu ɗaukaka da yake yi.
Mulki Yakan Girma Kamar Iri
18Saboda haka ya ce, “Mulkin Ubanmu yana kama da me? Da me zan kwatanta shi? 19Yana kama da ƙwayar mastad da wani mutum ya ɗauka ya shuka a lambunsa, ta yi girma ta zama itace, har tsuntsayen sararin sama suka yi sheƙa a rassansa.”
20Ya kuma sāke cewa, “Da me zan kwatanta Mulkin Ubanmu? 21Yana kama da yisti da wata mace ta ɗauka ta ɓoye a cikin mudu uku na gari, har sai da dukansa ya kumbura.”
Ku Shiga ta Matsattsiyar Ƙofa
22Ya ci gaba da tafiyarsa ta cikin birane da ƙauyuka, yana koyarwa yana tafiya wajen Urushalima. 23Sai wani ya tambaye shi, “Ya Ubangiji, kaɗan ne waɗanda za a ceto?” Sai ya ce musu,
24“Ku yi ƙoƙari ƙwarai ku shiga ta matsattsiyar ƙofar — ina gaya muku, mutane da yawa za su yi ƙoƙarin shiga amma za su kāsa. 25Da zarar mai gidan ya tashi ya rufe ƙofar, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa, kuna cewa, ‘Ya Ubangiji, ka buɗe mana.’ Sai yă amsa yă ce, ‘Ban san inda kuka fito ba.’ 26Sa'an nan za ku fara cewa, ‘Mun ci mun kuma sha a gabanka; ka kuma yi koyarwa a titunanmu.’ 27Amma yă ce, ‘Ina gaya muku, ban san inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukanku masu aikata mugunta!’ 28Za a yi kuka da cizon haƙora, sa'ad da kuka ga Ibrahim da Is'haƙa da Yakubu da dukan annabawa a cikin Mulkin Ubanmu, alhali ku kuwa an jefar da ku waje. 29Mutane za su zo daga gabas da yamma, daga arewa da kudu, su zauna su ci abinci a cikin Mulkin Ubanmu. 30Lalle kuwa, waɗansu na ƙarshe ne waɗanda za su zama na farko, waɗansu kuma na farko ne waɗanda za su zama na ƙarshe.”
Yesu Ya Yi Kuka saboda Urushalima
31A daidai wannan sa'a, sai waɗansu Farisiyawa suka zo, suna gaya masa, “Ka fita, ka bar nan — Hiridus yana so yă kashe ka.”
32Sai ya ce musu, “Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, ga shi, ina fitar da aljanu ina kuma warkar da marasa lafiya yau da gobe, a rana ta uku kuwa in gama aikina. 33Duk da haka, dole ne in yi tafiya yau da gobe da jibi, da yake ba annabin da zai iya mutuwa a waje da Urushalima.
34Urushalima, Urushalima, mai kashe annabawa, mai jifan waɗanda aka aiko mata! Sau nawa na yi marmarin tara 'ya'yanki kamar yadda kaza takan tara 'ya'yanta a ƙarƙashin fikafikanta — amma kika ƙi! 35Ga shi, an bar miki gidanki a yashe. Ina gaya miki, ba za ki ƙara ganina ba sai kin ce, ‘Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubanmu!’”