Ƙawancen da Ba Nasa Ba Ne
Yahuda ya gudu zuwa Masar ba tare da ya tambayi Uban ba, ya kuma biya domin taimakon da ba zai iya taimako ba. Suna ce wa annabawa su faɗi abubuwa masu daɗi. Hanyar komawa gida natsuwa ce da dogara, wadda suka ƙi. Duk da haka Uban yana jira ya yi alheri, wata murya kuma tana cewa, bi ta nan.
30 1“Kaito ga 'ya'ya masu tawaye,” in ji Ubanmu, “waɗanda suke aiwatar da wani shiri, amma ba nawa ba, suke kuma ƙulla ƙawance, amma ba na Ruhuna ba, suna tara zunubi a kan zunubi; a a v1 Ubanmu ya kira mutanensa 'ya'ya masu tawaye' — 'ya'ya maza da mata da suke nasa, ba baƙi ba. Baƙin cikinsa a wannan babi baƙin ciki ne na Uba. 2waɗanda suka kama hanya zuwa Masar, ba tare da sun nemi shawarata ba, domin su nemi mafaka a cikin kariyar Fir'auna su kuma nemi matsuguni a inuwar Masar. 3Saboda haka kariyar Fir'auna za ta zama muku kunya, matsuguni kuma a inuwar Masar yă zama muku wulaƙanci. 4Gama ko da yake shugabannin Fir'auna suna a Zowan, manzanninsa kuma sun kai Hanes, 5kowa zai sha kunya saboda wani mutanen da ba za su iya taimakonsu ba, waɗanda ba sa kawo wani amfani ko riba, sai dai kunya da wulaƙanci.”
6“Saƙo game da namun jejin Negeb. Ta cikin ƙasa mai wahala da ƙunci, inda zakanya da zaki suke yawo, da kububuwa da maciji mai saurin harbi suke fako, suna ɗauke da dukiyoyinsu a bayan jakuna, da taskokinsu a tozon raƙuma, zuwa ga wani mutanen da ba za su iya taimakonsu ba. 7Taimakon Masar banza ne da wofi; saboda haka na kira ta ‘Dodon da Ba Ya Cutarwa.’
A Rubuta Shi Yă Zama Shaida
8“Yanzu ka tafi, ka rubuta shi a gabansu a kan allo ka kuma zāna shi a cikin littafi, domin yă zama don lokaci mai zuwa, 9Gama su mutane ne masu tawaye, 'ya'ya masu ha'inci, 'ya'ya da ba sa son su ji koyarwar Ubanmu. 10Suna ce wa masu duba, ‘Kada ku gani,’ suna kuma ce wa annabawa, ‘Kada ku yi mana annabcin abin da yake daidai; ku gaya mana abubuwa masu daɗi, ku yi annabcin ruɗi.
11Ku bar hanya, ku kauce daga turba, kada mu ƙara jin labarin Mai Tsarki na Isra'ila.’
12Saboda haka ga abin da Mai Tsarki na Isra'ila, Ubanmu, yake cewa: Domin kun ƙi wannan magana kuka dogara ga danniya da ha'inci kuka kuma jingina a kansu, 13saboda haka wannan laifi zai zama muku kamar tsagewar da take gab da faɗuwa, kumburi a cikin bango mai tsawo, wanda rushewarsa take zuwa ba zato, nan take. 14Fasuwarsa kamar fasuwar tulun mai ginin tukwane ne, wanda aka farfasa ba tausayi har a cikin gutsattsarinsa ba a sami ko gutsuri da za a kwashe wuta daga murhu ko a ɗiba ruwa daga rijiya.
15Gama ga abin da Uba Mai Iko Dukka, Mai Tsarki na Isra'ila, ya faɗa: A cikin komowa da hutu za ku sami ceto; a cikin natsuwa da dogara ne ƙarfinku zai kasance. Amma kun ƙi, 16kuka ce, ‘A'a! Za mu gudu a kan dawakai’—saboda haka za ku gudu; kuka kuma ce, ‘Za mu hau dawakai masu sauri’—saboda haka masu binku za su yi sauri.
17Dubu za su gudu saboda barazanar mutum ɗaya; saboda barazanar mutum biyar za ku gudu, har sai kun rage kamar sandan tuta a kan ƙwanƙolin dutse, kamar alama a kan tudu.
18Saboda haka Ubanmu yana jira domin yă yi alheri gare ku, saboda haka kuma yakan tashi domin yă nuna muku jinƙai. Gama shi Uba ne mai adalci; masu albarka ne duk waɗanda suke jiransa. b b v18 Ko bayan tawayen 'ya'yansa, Ubanmu ba ya tsayawa daga nesa — yana jira, yana sunkuyawa gare su, don ganin wata alama ta cewa za su komo gida. 19Mutane za su zauna a Sihiyona, a Urushalima; ba za ku ƙara yin kuka ba. Da jin karar kukanku lalle zai yi muku alheri; sa'ad da ya ji, zai amsa muku. 20Ko da yake Ubanmu ya ba ku burodin wahala da ruwan shan azaba, Malaminku ba zai ƙara ɓoyewa ba, amma idanunku za su ga Malaminku.
21Kunnuwanku za su ji magana a bayanku, ‘Ga hanya nan; ku bi ta,’ sa'ad da kuka juya dama ko hagu.
22Sa'an nan za ku ƙazantar da sassaƙaƙƙun gumakanku da aka dalaye da azurfa da gumakan ƙarfe da aka dalaye da zinariya. Za ku yar da su kamar tsummar al'ada ku ce, ‘Ku fita!’
23Zai aiko da ruwan sama domin irin da kuka shuka, da abinci daga amfanin ƙasa, mai yalwa da yawa. A ranar dabbobinku za su yi kiwo a wuraren kiwo masu faɗi. 24Shanu da jakunan da suke nome ƙasa za su ci ingantaccen abinci, wanda aka shiƙe da felu da cokali mai yatsu. 25A kan kowane dutse mai tsawo da tudu za a sami gudanan ruwa, a ranar babban kisa sa'ad da hasumiyoyi suka faɗi. 26Hasken wata zai zama kamar na rana, hasken rana kuma zai yi haske sau bakwai, kamar hasken kwana bakwai, sa'ad da Ubanmu ya ɗaure karyewar mutanensa ya kuma warkar da raunin da ya yi. 27Duba—sunan Ubanmu yana zuwa daga nesa, yana ƙuna da fushinsa, cikin hayaƙi mai kauri yana tashi; leɓunansa sun cika da hasala, harshensa kuma kamar wuta mai cinyewa ne. 28Numfashinsa kamar rigyawar ruwa ne mai ambaliya da yake kaiwa har wuya, domin yă tankaɗe al'ummai a cikin matankaɗin hallaka yă kuma sa linzami a muƙamuƙan mutanen da yake kai su ga ɓata. 29Za ku kasance da waƙa, kamar a daren da ake yin idi mai tsarki, da farin cikin zuciya, kamar sa'ad da mutum yake tafiya da karar sarewa domin yă je dutsen Ubanmu, zuwa ga Dutsen Isra'ila. 30Ubanmu kuma zai sa a ji muryarsa mai ɗaukaka ya kuma bayyana saukar dukan hannunsa, cikin zafin fushi da harshen wuta mai cinyewa, tare da ambaliyar ruwan sama da hadari da ƙanƙara. 31Gama da muryar Ubanmu za a ragargaza Assuriyawa, sa'ad da ya buge su da sandansa. 32Kowane bugu na sandan hukunci da Ubanmu zai yi musu zai zo tare da ganguna da molaye, yayinda yake yaƙe su da dukan hannunsa da ya ɗaga. 33Gama tun da daɗewa an shirya wurin ƙonawa; hakika, an shirya shi domin sarki, tarin wutarsa mai zurfi da faɗi, da wuta da itace a yalwace; numfashin Ubanmu, kamar rafin kibritu, yana ƙuna shi.