Kaiton Waɗanda Suke Dogara ga Masar
Dawakan Masar nama ne, ba ruhu ba; dogara gare su yakan kayar da mai taimako da wanda ake taimakawa tare. Uba zaki ne wanda ihun makiyaya ba ya iya korarsa, kuma kamar tsuntsaye ne masu shawagi bisa Urushalima. Assuriya ta fāɗi ta takobin da ba mutum ne yake riƙe da shi ba, mutane kuma suka zubar da gumakansu.
31 1Kaiton waɗanda suke gangarawa zuwa Masar neman taimako, waɗanda suke dogara ga dawakai, waɗanda suke amincewa da kekunan yaƙi saboda yawansu da kuma ga mahaya dawakai saboda suna da ƙarfi ƙwarai—amma ba sa dubawa ga Mai Tsarki na Isra'ila, Ubanmu, ba sa kuma nemansa. 2Duk da haka shi ma mai hikima ne, yana kuma kawo masifa; ba ya janye maganarsa. Zai tashi gāba da gidan masu aikata mugunta da kuma gāba da taimakon masu aikata laifi. 3Masarawa mutane ne, ba Allah ba; dawakansu nama ne, ba ruhu ba. Sa'ad da Ubanmu ya miƙa hannunsa, mai taimako zai yi tuntuɓe, wanda aka taimaka kuma zai fāɗi, dukansu kuwa za su ƙare tare.
4Gama ga abin da Ubanmu ya faɗa mini: Kamar yadda zaki ko ɗan zaki yake ruri a kan abin da ya kama—ko da an kira ƙungiyar makiyaya gāba da shi, ba ya tsorata saboda ihunsu ko ya firgita saboda surutunsu—haka Uban rundunonin Sama zai sauko don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da bisa tsayinsa. 5Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama, haka Uban rundunonin Sama zai kāre Urushalima; zai kāre ta yă kuma cece ta, zai wuce bisanta yă kuɓutar da ita.
6Ku komo wurin wanda mutanen Isra'ila suka juya masa baya ƙwarai. 7Gama a ranan nan kowa zai yar da gumakansa na azurfa da gumakansa na zinariya, waɗanda hannuwanku da kansu suka ƙera muku cikin zunubi.
8Sa'an nan Assuriya zai fāɗi ta wurin takobi wanda ba na mutum ba ne, takobi kuma wanda ba na mutane ba zai cinye shi. Zai gudu a gaban takobi, samarinsa kuma za a sa su aikin tilas. 9Kagaransa zai rushe saboda tsoro, sarakunansa kuma za su gudu da firgita daga tutar yaƙi, in ji Ubanmu, wanda wutarsa take a Sihiyona wanda kuma tanderunsa yake a Urushalima.