Sarkin da Yake Mulki da Adalci
Shugabannin da suke ba mutane mafaka kamar inuwar dutse a ƙasa mai gajiyarwa sun tsaya gāba da wawan da yake ƙarya game da Uba, yana kuma kwashe abincin mayunwaci daga farantinsa. Mata masu jin daɗin rai sun ji cewa girbi zai lalace. Fādar za ta zauna kufai har sai an zubo Ruhu, jeji kuma ya zama mai yalwar amfani.
32 1Ga shi, wani sarki zai yi mulki da adalci, kuma masu mulki za su yi shugabanci da gaskiya. 2Kowannensu zai zama kamar mafaka daga iska, wurin tsari daga hadari, kamar rafukan ruwa a busasshiyar ƙasa, kamar inuwar wani babban dutse a ƙasa mai gajiyarwa. 3Sa'an nan idanun masu gani ba za su rufe ba, kuma kunnuwan masu ji za su saurara. 4Zuciya mai garaje za ta fahimci sani, kuma harshe mai i'ina zai yi magana da sauri da kuma a fili. 5Ba za a ƙara kiran wawa da suna mai martaba ba, ba kuma za a ce mai sharri yana da daraja ba. 6Gama wawa yakan yi maganar wauta, zuciyarsa kuma tana ƙulla mugunta: domin yă aikata rashin tsoron Allah, yă faɗi ƙarya game da Ubanmu, yă bar mai yunwa da hannu wofi, yă kuma hana mai ƙishirwa ruwan sha. 7Makaman mai sharri mugaye ne; yana ƙulla makirci na mugunta domin yă hallaka matalauci da kalmomin ƙarya, ko da mabukaci yana kai ƙararsa da gaskiya. 8Amma mutum mai martaba yana shirya abubuwa masu martaba, kuma ta wurin abubuwa masu martaba yake tsayawa.
Ku Tashi, Ku 'Ya'ya Mata Marasa Kula
9Ku mata masu sakewa, ku tashi ku ji muryata; ku 'ya'ya mata marasa kula, ku saurari abin da nake faɗa.
10“Bayan shekara da ɗan lokaci kaɗan za ku yi rawar jiki, ku mata marasa kula, gama girbin inabi zai gaza, kuma ba za a yi tarawa ba. 11Ku yi rawar jiki, ku masu sakewa; ku girgiza, ku marasa kula! Ku tuɓe kanku tsirara ku kuma ɗaura tufafin makoki a kugunku. 12Ku bugi ƙirjinku saboda gonaki masu daɗi, saboda kuringar inabi mai ba da 'ya'ya, 13saboda ƙasar mutanena, inda ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya suke tsirowa; hakika, saboda dukan gidajen farin ciki a birni mai annashuwa. 14Gama za a yashe fada, a watsar da birni mai hayaniya; tudu da hasumiyar tsaro za su zama kufai har abada, wurin annashuwa ga jakunan daji, wurin kiwo ga garkuna, 15sai an zubo Ruhun Ubanmu a kanmu daga sama, jeji kuma ya zama gona mai amfani, gona mai amfani kuma a ɗauke ta kamar kurmi. 16Sa'an nan gaskiya za ta zauna a jeji, adalci kuma zai dawwama a gona mai amfani. 17Aikin adalci zai zama salama, sakamakon adalci kuma, natsuwa da tsaro har abada. 18Mutanena za su zauna a gida mai salama, a wuraren zama masu tsaro, a wuraren hutawa marasa damuwa. 19Ko da ƙanƙara ta rushe kurmi, aka kuma ragargaza birni ƙaƙaf, 20masu albarka ne ku da kuke shuka kusa da dukan ruwaye, ku da kuke sakin saniya da jaki su yi yawo cikin 'yanci.”