Dina
Wani basaraken wurin ya kama Dina ya yi mata fyaɗe, sa'an nan yana so ya aure ta. 'Yan'uwanta suka mayar da martani da salama ta ƙarya: suka nemi a yi wa mazan kaciya, sa'an nan suka kashe kowane namiji a birnin sa'ad da suke cikin zafi. Abin da kawai Yakubu ya koka a kai shi ne haɗarin da ya same shi kansa.
34 1Dina, 'yar da Liya ta haifa wa Yakubu, ta fita don ta ga 'yan matan ƙasar. 2Shekem ɗan Hamor Bahibe, sarkin ƙasar, ya gan ta, ya kama ta, ya kwana da ita, ya kuma wulaƙanta ta. 3Zuciyarsa ta manne wa Dina 'yar Yakubu; ya ƙaunaci yarinyar, ya kuma yi mata magana mai sanyaya zuciya. 4Sai Shekem ya ce wa mahaifinsa Hamor, “Ka nemo mini yarinyar nan ta zama matata.”
5Yakubu ya ji cewa Shekem ya ƙazantar da 'yarsa Dina, amma 'ya'yansa suna tare da dabbobinsa a jeji, saboda haka Yakubu bai ce kome ba sai da suka dawo. 6Sai Hamor, mahaifin Shekem, ya fito wurin Yakubu don yă yi magana da shi. 7'Ya'yan Yakubu suka dawo daga jeji. Da suka ji haka, sai mutanen suka ji zafi ƙwarai, suka kuma yi fushi sosai, domin Shekem ya yi abin kunya a Isra'ila, da ya kwana da 'yar Yakubu, abin da bai kamata a yi ba. 8Hamor ya yi magana da su, ya ce, “Ɗana Shekem yana marmarin 'yarku ƙwarai. Ina roƙonku, ku ba shi ita ta zama matarsa. 9Ku yi auratayya da mu; ku ba mu 'ya'yanku mata, ku kuma ɗauki 'ya'yanmu mata wa kanku. 10Ku zauna tare da mu; ƙasar a buɗe take gare ku. Ku zauna, ku yi ciniki, ku kuma mallaki kadarori a cikinta.”
11Shekem ya ce wa mahaifinta da 'yan'uwanta, “Bari in sami tagomashi a idanunku; duk abin da kuka ce mini, zan ba ku. 12Ku nemi duk wani sadaki da kyauta, ko da yawansu, zan biya. Sai dai ku ba ni yarinyar ta zama matata.”
13'Ya'yan Yakubu suka amsa wa Shekem da mahaifinsa Hamor da yaudara, domin Shekem ya ƙazantar da 'yar'uwarsu Dina. 14Suka ce musu, “Ba za mu iya yin wannan ba, mu ba da 'yar'uwarmu ga mutumin da ba a yi masa kaciya ba; wannan abin kunya ne gare mu. 15Za mu yarda da wannan ne kaɗai, idan kun zama kamarmu, wato a yi wa kowane namijinku kaciya. 16Sa'an nan za mu ba ku 'ya'yanmu mata, mu kuma ɗauki naku wa kanmu; za mu zauna tare da ku, mu zama jama'a ɗaya. 17Amma in ba ku saurare mu ba, ba ku kuma yi kaciya ba, za mu ɗauki 'yarmu, mu tafi.”
18Maganarsu ta gamshi Hamor da ɗansa Shekem. 19Saurayin bai yi jinkirin aikata haka ba, don yana jin daɗin 'yar Yakubu. Shi ne kuma aka fi girmamawa a gidan mahaifinsa. 20Sai Hamor da ɗansa Shekem suka zo ƙofar birninsu, suka yi magana da mutanen birninsu, suka ce, 21“Waɗannan mutane suna zaman lafiya da mu. Bari su zauna a ƙasar, su yi ciniki a cikinta, ai ƙasar tana da fāɗi sosai dominsu. Za mu ɗauki 'ya'yansu mata su zama matanmu, mu kuma ba su namu. 22Sai dai a kan wannan sharaɗi mutanen za su yarda su zauna tare da mu mu zama jama'a ɗaya, wato a yi wa kowane namiji a cikinmu kaciya, kamar yadda aka yi musu. 23Ashe, garkunansu da dukiyarsu da dukan dabbobinsu ba za su zama namu ba? Bari dai mu yarda da su, za su kuwa zauna tare da mu.”
24Dukan waɗanda suke fita ta ƙofar birninsa suka saurari Hamor da ɗansa Shekem, aka kuma yi wa kowane namiji kaciya, dukan waɗanda suke fita ta ƙofar birninsa. 25A rana ta uku, tun suna cikin zafi, sai biyu daga cikin 'ya'yan Yakubu, Saminu da Lawi, 'yan'uwan Dina, kowanne ya ɗauki takobinsa, suka auka wa birnin da bai yi zato ba, suka karkashe kowane namiji. 26Suka kashe Hamor da ɗansa Shekem da takobi, suka ɗauko Dina daga gidan Shekem, suka tafi. 27'Ya'yan Yakubu suka auka wa waɗanda aka kashe, suka washe birnin, domin mutanen can sun ƙazantar da 'yar'uwarsu. 28Suka ɗauki garkunansu na tumaki, da na shanu, da jakunansu, da dukan abin da yake cikin birni da kuma a jeji. 29Suka kwashe dukan dukiyarsu, da dukan 'ya'yansu, suka kuma kame matansu, suka washe dukan abin da yake cikin gidaje. 30Yakubu ya ce wa Saminu da Lawi, “Kun jawo mini wahala, kun sa na zama abin ƙyama ga mazaunan ƙasar nan, wato Kan'aniyawa da Ferizziyawa. Ni kuwa mutanena kaɗan ne; in suka haɗa kai a kaina, za su auka mini, in kuma hallaka, ni da gidana.”
31Amma suka ce, “Ashe, ya kamata yă yi da 'yar'uwarmu kamar karuwa?”