Musa da Haruna a Gaban Fir'auna
Musa da Haruna suka roƙi Fir'auna izinin idi a jeji, ya ce musu bai san wannan Allah ba. Aka hana ciyawa amma aka bar yawan tubalin, aka dūki shugabannin aiki, Isra'ila kuwa suka ɗora wa Musa laifi. Musa ya juya ya tambayi Ubanmu don me ma ya aiko shi.
5 1Bayan haka Musa da Haruna suka tafi wurin Fir'auna suka ce, “Ga abin da Ubanmu na Isra'ila ya ce: Ka bar mutanena su tafi su yi mini biki a jeji.”
2Fir'auna ya ce, “Wane ne Allah, da zan yi biyayya ga muryarsa in bar Isra'ila su tafi? Ban san Allah ba, ba kuwa zan bar Isra'ila su tafi ba.”
3Suka ce, “Ubanmu ya same mu. Bari mu yi tafiya ta kwana uku zuwa cikin jeji mu yi hadaya ga Ubanmu, in ba haka ba zai iya buge mu da annoba ko takobi.”
4Amma sarkin Masar ya ce musu, “Musa da Haruna, don me kuke janye mutane daga aikinsu? Ku koma ga aikinku!” 5Fir'auna ya ce, “Duba, mutanen ƙasar yanzu sun yi yawa, kuna kuma so ku sa su daina aiki!”
6A ranan nan Fir'auna ya ba da umarni ga masu gadin bayi da shugabannin da suke kan mutane, ya ce, 7“Kada ku ƙara ba wa mutane ciyawa don yin tubali kamar dā. Sai su tafi su tattara ciyawa da kansu.
8Ku nema musu tubali daidai yawan da suke yi dā; kada ku rage shi. Ragwaye ne su; shi ya sa suke kuka suna cewa, ‘Bari mu je mu yi hadaya ga Allahnmu.’ 9Ku nawaita wa mutanen aiki, domin su ci gaba da shi su ƙyale ƙarairayi.”
10Masu gadin bayi da shugabanni suka fita suka gaya wa mutane, “Fir'auna ya ce, ‘Ba zan ƙara ba ku ciyawa ba.’ 11Ku tafi ku nemo wa kanku ciyawa duk inda kuka same ta—amma ba za a rage aikinku ko kaɗan ba.’” 12Saboda haka mutane suka bazu ko'ina a cikin dukan ƙasar Masar don su tattara tattaka a maimakon ciyawa. 13Masu gadin bayi suka dinga matsa musu suna cewa, “Ku gama aikinku na kullum, kamar lokacin da kuke da ciyawa.” 14Aka dūki shugabannin Isra'ilawa, waɗanda masu gadin bayi na Fir'auna suka naɗa a kansu, aka tambaye su, “Don me ba ku cika adadin tubalinku na jiya da na yau ba, kamar dā?”
15Sai shugabannin Isra'ilawa suka zo suka yi kuka ga Fir'auna, suka ce, “Don me kake yi wa bayinka haka? 16Ba a ba wa bayinka ciyawa ba, duk da haka suna ce mana, ‘Ku yi tubali!’ Duba, ana dūkan bayinka, amma laifin mutanenka ne.”
17Fir'auna ya ce, “Ragwaye! Ragwaye ne ku! Shi ya sa kuke cewa, ‘Bari mu je mu yi hadaya ga Allah.’ 18Yanzu ku tafi, ku yi aiki. Ba za a ba ku ciyawa ba, duk da haka dole ku ba da cikakken adadin tubalinku.”
19Shugabannin Isra'ilawa suka ga suna cikin wahala sa'ad da aka ce musu, “Kada ku rage adadin tubalinku na kullum.” 20Da suka bar Fir'auna, sai suka iske Musa da Haruna suna jiransu domin su sadu da su, 21suka ce musu, “Bari Ubanmu ya dube ku ya yi muku shari'a, gama kun mai da mu abin ƙyama ga Fir'auna da fādawansa, kuka sa takobi a hannunsu domin su kashe mu.”
22Sai Musa ya koma wurin Ubanmu ya ce, “Ya Ubana Mai Iko Dukka, don me ka kawo wa mutanen nan wahala? Don me ka taɓa aiko ni?
23Tun da na tafi wurin Fir'auna don in yi magana da sunanka, ya cuci mutanen nan, kai kuwa ba ka ceci mutanenka ko kaɗan ba.”