Tafiya Zuwa Urushalima
Kowace tasha tana kawo gargaɗi kada ya ci gaba, wani annabi kuma ya ɗaure hannuwansa da ɗamarar Bulus. Bulus ya ce ya shirya ya mutu a can. A Urushalima, taron jama'a a haikali, suna zaton ya shigar da Bahelene ciki, suka kusa kashe shi da duka kafin sojoji su fitar da shi.
21 1Bayan da muka rabu da su, sai muka shiga jirgin ruwa muka miƙe zuwa Kos kai tsaye, washegari kuma muka tafi Rhodes, daga can kuma muka tafi Batara. 2Da muka sami wani jirgin ruwa mai tsallakawa zuwa Funisiya, sai muka shiga shi muka tashi. 3Da muka hangi Kubrus, sai muka bar ta a hannun haguwanmu, muka tuƙa zuwa Suriya, muka sauka a Taya, inda jirgin zai saukar da kayansa. 4Muka sami almajirai a can, muka zauna kwana bakwai. Ta wurin Ruhu Mai Tsarki suka yi ta gaya wa Bulus kada yă taka ƙafarsa a Urushalima. 5Sa'ad da lokacinmu a can ya cika, sai muka tashi muka ci gaba da tafiya, dukansu tare da matansu da 'ya'yansu suna tafiya tare da mu har bayan birnin. Muka durƙusa a bakin teku muka yi addu'a, 6muka kuma yi bankwana da juna. Sa'an nan muka shiga jirgin ruwa, su kuma suka koma gida.
7Da muka gama tafiyarmu ta jirgin ruwa daga Taya, sai muka iso Butolemais, muka gai da 'yan'uwa, muka zauna kwana ɗaya tare da su.
8Washegari muka tashi zuwa Kaisariya, muka shiga gidan Filibus mai bishara, ɗaya daga cikin bakwai ɗin, muka zauna tare da shi. 9Yana da 'ya'ya mata huɗu da ba su yi aure ba, waɗanda suke annabci. 10Yayinda muke zaune a can kwanaki masu yawa, sai wani annabi mai suna Agabus ya sauko daga Yahudiya.
11Ya zo wurinmu, ya ɗauki ɗamarar Bulus, ya ɗaure ƙafafunsa da hannuwansa, ya ce, “Ga abin da Ruhu Mai Tsarki ya ce: Yahudawan da suke a Urushalima za su ɗaure mai wannan ɗamara haka, sa'an nan su miƙa shi ga hannun Al'ummai.”
12Da muka ji haka, sai mu da mutanen wurin muka roƙi Bulus kada yă haura zuwa Urushalima. 13Bulus ya amsa ya ce, “Me ya sa kuke kuka kuna ɓata mini zuciya? Na shirya ba kawai a ɗaure ni ba, har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.” 14Da yake bai yarda a lallashe shi ba, sai muka yi shiru muka ce, “Bari a aikata nufin Ubangiji.”
15Bayan waɗannan kwanaki, sai muka yi shiri muka haura zuwa Urushalima. 16Waɗansu almajirai daga Kaisariya suka kuma tafi tare da mu, suka kai mu wurin wani mai suna Manason, mutumin Kubrus, almajiri tun farko, domin mu sauka a wurinsa.
17Sa'ad da muka iso Urushalima, sai 'yan'uwa suka karɓe mu da farin ciki. 18Washegari Bulus ya tafi tare da mu don ganin Yaƙub, dukan dattawa kuma suna nan. 19Ya gaishe su, sa'an nan ya ba su labarin, ɗaya bayan ɗaya, abin da Ubanmu ya aikata a cikin Al'ummai ta wurin hidimarsa. 20Da suka ji haka, sai suka yabi Ubanmu, sa'an nan suka ce masa, “Ka gani, ɗan'uwa, dubban Yahudawa nawa ne suka gaskata, dukansu kuma suna himma sosai ga shari'a. 21An gaya musu cewa kana koya wa dukan Yahudawan da suke cikin al'ummai su yashe Musa, kana gaya musu kada su yi wa 'ya'yansu kaciya ko su bi al'adunmu. 22To, me za mu yi? Babu shakka za su ji cewa ka zo. 23Saboda haka ka yi abin da muke gaya maka. Muna da mutane huɗu da suke ƙarƙashin wani alkawari. a a v23 Waɗannan mutane sun ɗauki alkawarin Banazare — wani alkawarin bautar Allah na ɗan lokaci da yake ƙarewa da aske kai da kuma miƙa hadaya a haikali. 24Ka ɗauki waɗannan mutane, ka tsarkake kanka tare da su, ka kuma biya kuɗin da za su kashe domin su aske kawunansu. Sa'an nan kowa zai san cewa labaran da ake yaɗawa game da kai ƙarya ne, da kuma cewa kai kanka kana kiyaye shari'a. 25Amma game da Al'ummai da suka gaskata, mun riga mun rubuta shawararmu: su guji abincin da aka miƙa wa gumaka, da jini, da naman dabbar da aka shaƙe, da kuma fasikanci.”
26Saboda haka Bulus ya ɗauki mutanen, washegari kuma, bayan ya tsarkake kansa tare da su, sai ya shiga haikali, yana sanar da lokacin da kwanakin tsarkakewar za su ƙare da kuma lokacin da za a miƙa hadaya domin kowannensu.
An Kama Bulus a Haikali
27Da kwana bakwai ɗin suna gab da ƙarewa, sai waɗansu Yahudawa daga Asiya suka gan shi a haikali, suka tunzura dukan taron, suka kama shi, 28suna ihu, suna cewa, “Ya mutanen Isra'ila, ku taimaka! Wannan shi ne mutumin da yake koya wa kowa a ko'ina gāba da mutanenmu, da shari'a, da kuma wannan wuri. Har ma ya kawo Hellenawa cikin haikali, ya ƙazantar da wannan wuri mai tsarki.” 29Gama a dā sun ga Tarofimus mutumin Afisa tare da Bulus a birnin, suka ɗauka cewa Bulus ya kawo shi cikin haikali.
30Sai dukan birnin ya ruɗe; mutane suka ruga wuri ɗaya, suka kama Bulus, suka ja shi daga haikali, nan da nan kuma aka rufe ƙofofi. 31Yayinda suke ƙoƙarin kashe shi, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar sojoji cewa dukan Urushalima na cikin hargitsi. 32Nan da nan ya ɗauki sojoji da shugabannin ɗari-ɗari, ya ruga da gudu zuwa gare su. Da suka ga shugaban sojoji da sojojin, sai taron suka daina dūkan Bulus. 33Shugaban sojoji ya zo, ya kama shi, ya umarta a ɗaure shi da sarƙa biyu, sa'an nan ya tambaya ko shi wane ne da kuma abin da ya aikata. 34A cikin taron waɗansu suna ihun wani abu, waɗansu kuma wani. Da ya kāsa gane gaskiyar saboda hayaniyar, sai ya umarta a kawo Bulus cikin barikin sojoji. 35Sa'ad da Bulus ya kai bakin matakalai, sai dole sojoji su ɗauke shi saboda tashin hankalin taron, 36gama taron mutanen suna ta binsa, suna ihu, suna cewa, “A kawar da shi!”
Bulus Ya Yi Magana da Taron
37Da ana gab da shigar da Bulus cikin barikin, sai ya tambayi shugaban sojoji, ya ce, “Na iya gaya maka wani abu?” Shi kuma ya amsa ya ce, “Ashe kana jin Hellenanci?”
38Ashe, ba kai ne mutumin Masar nan da ya tā da tawaye a dā ya kuma jagoranci mayaƙa masu kisan kai dubu huɗu zuwa jeji ba?
39Bulus ya amsa ya ce, “Ni Bayahude ne, daga Tarsus a ƙasar Kilikiya, ɗan birni wanda ba ƙaramin birni ba ne. Ina roƙonka, ka bar ni in yi magana da mutanen.”
40Da aka ba shi izini, sai Bulus ya tsaya a bakin matakalai, ya yi wa mutanen alama da hannunsa. Sa'ad da aka yi tsit ƙwarai, sai ya yi musu magana da Ibrananci, ya ce: