Mai Shuka Ya Fita Yă Yi Shuka
Daga cikin jirgin ruwa Yesu ya ba da labarai game da mulkin Ubansa waɗanda suke ɓoyewa kamar yadda suke bayyanawa: ƙasa iri huɗu, ciyawa da aka bari da gangan ta yi girma har lokacin girbi, ƙwayar mastad, yisti da aka ɓoye, dukiyar da ta cancanci a sayar da kome saboda ita. Sa'an nan mutanen garinsu suka ji haushinsa, kuma ba a yi abu da yawa a can ba.
13 1A ranar nan Yesu ya fita daga gidan, ya zauna a bakin teku. 2Taro mai yawa ya taru kewaye da shi, sai ya shiga jirgin ruwa ya zauna, yayin da dukan taron suka tsaya a bakin teku.
3Ya kuma gaya musu abubuwa masu yawa da misalai, yana cewa, “Ga shi, wani mai shuka ya fita yă yi shuka. 4Yayin da yake shuka, waɗansu iri suka faɗa a gefen hanya, sai tsuntsaye suka zo suka cinye su. 5Waɗansu iri kuwa suka faɗa a ƙasa mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, suka tsira da sauri don ƙasar ba ta da zurfi. 6Da rana ta fito, sai tsire-tsiren suka ƙone; da yake ba su da saiwa, sai suka yanƙwane. 7Waɗansu iri kuma suka faɗa cikin ƙaya, sai ƙayayen suka yi girma suka shaƙe su. 8Waɗansu iri kuwa suka faɗa a ƙasa mai kyau, suka ba da hatsi: waɗansu riɓi ɗari, waɗansu sittin, waɗansu kuma talatin. 9Duk mai kunnuwa, yă ji.”
10Sai almajiran suka zo wurinsa suka tambaye shi, “Don me kake yi musu magana da misalai?”
11Ya ce, “An ba ku ikon sanin asiran Mulkin Ubanmu; su kuwa ba a ba su ba. 12Duk mai abu za a ƙara masa har yă samu a yalwace; amma wanda ba shi da kome, ko abin da yake da shi ma za a karɓe masa. 13Shi ya sa nake yi musu magana da misalai, don suna kallo amma ba sa gani, suna saurare amma ba sa ji ba sa kuma ganewa. 14A kansu annabcin Ishaya ya cika, cewa, ‘Za ku yi ta ji amma ba za ku taɓa ganewa ba; za ku yi ta kallo amma ba za ku taɓa gani ba.’ 15Gama zuciyar mutanen nan ta taurare; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu—in ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su gane da zuciyarsu, su juyo, in kuwa warkar da su.’
16Amma idanunku masu albarka ne, gama suna gani, haka ma kunnuwanku, gama suna ji. 17Lalle hakika, ina gaya muku, annabawa da masu adalci da yawa sun yi marmarin ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba; su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.
18Saboda haka, ku saurari misalin mai shuka. 19Duk wanda ya ji maganar Mulki bai kuwa gane ta ba—sai mugun nan yă zo yă ƙwace abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da aka shuka a gefen hanya. 20Irin da aka shuka a ƙasa mai duwatsu kuwa, shi ne wanda yake jin maganar, nan da nan yă karɓe ta da farin ciki, 21amma da yake ba shi da saiwa a cikinsa, ba ya daɗewa; sa'ad da wahala ko tsanani ya zo saboda maganar, nan da nan sai yă kauce. 22Wanda aka shuka a cikin ƙaya kuwa, shi ne mai jin maganar, amma damuwar wannan zamani da ruɗin dukiya sukan shaƙe ta, har ta kāsa ba da amfani. 23Amma irin da aka shuka a ƙasa mai kyau, shi ne mai jin maganar yă kuma gane ta. Yakan ba da amfani—riɓi ɗari, ko sittin, ko talatin na abin da aka shuka.”
Alkama da Ciyawa a Gona
24Ya kuma ba su wani misali, yana cewa, “Mulkin Ubanmu yana kama da wani mutum da ya shuka iri mai kyau a gonarsa. 25Amma yayin da kowa yake barci, sai maƙiyinsa ya zo, ya shuka ciyawa a cikin alkama, ya tafi. 26Da alkama ta tsira ta ba da hatsi, sai ciyawar ma ta bayyana. 27Sai bayin mai gonar suka zo suka ce, ‘Mai gida, ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? To, daga ina ciyawar ta fito?’
28Ya amsa ya ce, ‘Maƙiyi ne ya yi wannan.’ Sai bayin suka tambaye shi, ‘To, kana so mu je mu tumɓuke su?’
29‘A'a,’ ya ce, ‘gama yayin da kuke cire ciyawar, mai yiwuwa ku tumɓuke alkama tare da ita. 30Ku bar su duka su yi girma tare har lokacin girbi. A lokacin girbi zan ce wa masu girbi, Ku fara tara ciyawar, ku ɗaɗɗaure ta dami-dami domin a ƙone; sa'an nan ku tara alkama a cikin rumbuna.’”
Ƙwayar Mustad Ta Zama Itace
31Ya kuma ba su wani misali, yana cewa, “Mulkin Ubanmu yana kama da ƙwayar mustad da wani mutum ya ɗauka ya shuka a gonarsa. 32Ko da yake ita ce mafi ƙanƙanta a cikin dukan iri, sa'ad da ta yi girma takan zama mafi girma a cikin tsire-tsiren lambu, har ta zama itace, inda tsuntsaye sukan zo su yi sheƙa a rassanta.”
Mulki Yana Aiki kamar Yisti Ɓoyayye
33Ya kuma ba su wani misali, yana cewa, “Mulkin Ubanmu yana kama da yisti da wata mace ta ɗauka ta kwaɓa a cikin gari kimanin fam ashirin da biyar, har ya game dukan garin.”
34Dukan waɗannan abubuwa Yesu ya faɗa wa taron da misalai; bai kuwa gaya musu kome ba sai da misali.
35Wannan ya cika abin da aka faɗa ta bakin annabi, cewa, “Zan buɗe bakina da misalai; zan furta abubuwan da aka ɓoye tun halittar duniya.”
Uba Yana Rarraba Alkama da Ciyawa
36Sa'an nan ya bar taron ya shiga gida. Sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, “Ka bayyana mana misalin ciyawar da ke cikin gona.”
37Ya amsa ya ce, “Mai shuka irin nan mai kyau shi ne Ɗan Mutum. 38Gonar kuwa ita ce duniya. Iri mai kyau kuwa su ne 'ya'yan Mulki; ciyawar kuma su ne 'ya'yan mugun nan. 39Maƙiyin da ya shuka su kuwa shi ne Iblis; girbin kuwa shi ne ƙarshen zamani; masu girbin kuwa su ne mala'iku. 40Kamar yadda ake tara ciyawa a ƙone ta da wuta, haka zai kasance a ƙarshen zamani. 41Ɗan Mutum zai aiki mala'ikunsa su fid da dukan abin da yake jawo zunubi da dukan masu aikata mugunta daga mulkinsa. 42Za su jefa su cikin matoya mai cin wuta, inda ake kuka da cizon haƙora. 43Sa'an nan masu adalci za su haskaka kamar rana a cikin Mulkin Ubansu. Mai kunnuwa, yă ji.”
Mulki Ya Fi Kome Daraja
44Mulkin Ubanmu yana kama da dukiyar da aka ɓoye a gona. Wani mutum ya same ta, ya sāke ɓoye ta, sa'an nan da farin ciki ya sayar da dukan abin da yake da shi, ya sayi gonar.
45“Har wa yau, Mulkin Ubanmu yana kama da wani ɗan kasuwa mai neman lu'ulu'u masu kyau. 46Da ya sami lu'ulu'u guda mai tsada ƙwarai, sai ya je ya sayar da dukan abin da yake da shi, ya saye shi.
Taru Yana Kama Kowane Iri
47Har wa yau, Mulkin Ubanmu yana kama da taru da aka jefa a tafki, ya tattara kifi na kowane iri. 48Da ya cika, sai masunta suka jā shi zuwa gaɓa, suka zauna, suka tattara kifi masu kyau a cikin kwanduna, suka zubar da marasa kyau. 49Haka zai kasance a ƙarshen zamani, mala'iku za su fito su ware mugaye daga cikin masu adalci, 50su kuma jefa su cikin matoya mai cin wuta, inda za su yi kuka suna cizon haƙora.”
51“Kun gane dukan waɗannan abubuwa?” Suka ce, “I.”
52Ya ce musu, “Saboda haka duk malamin shari'a da aka horar domin Mulkin Ubanmu yana kama da mai gida wanda yakan fito da dukiya sababbi da tsofaffi daga ɗakin ajiyarsa.”
An Ƙi Yesu a Garinsa
53Da Yesu ya gama waɗannan misalai, sai ya tashi daga wurin.
54Da ya komo garinsu, ya yi musu koyarwa a majami'arsu, har suka yi mamaki suna cewa, “Daga ina wannan mutum ya sami wannan hikima da waɗannan manyan ayyuka? 55Wannan ba ɗan masassaƙin ba ne? Ba Maryamu ce sunan mahaifiyarsa ba, 'yan'uwansa kuwa Yaƙubu, da Yusuf, da Siman, da Yahuda? 56'yan'uwansa mata duka kuwa ba a nan suke tare da mu ba? To, daga ina wannan mutum ya sami dukan waɗannan abubuwa?”
57Sai suka yi tuntuɓe game da shi. Amma Yesu ya ce musu, “Ana girmama annabi a ko'ina, sai dai a garinsa da kuma a cikin gidansa.”
58Bai kuwa yi ayyukan al'ajabi da yawa a wurin ba, saboda rashin bangaskiyarsu.