Wane ne Ya 'Yantar da Jakin Jeji?
Tambayoyin suna ci gaba ta cikin namomin jeji da ba sa bukatar kulawar mutum: awakin dutse masu haihuwa su kaɗai, jakin jeji da yake raina birni, jimina da take manta da ƙwayayenta, doki da yake yi wa tsoro dariya, gaggafa a kan ƙwanƙolin dutsensa. Babu ɗayansu da yake biyan bukatar Ayuba.
39 1“Ko ka san lokacin da awakin dutse suke haihuwa? Kana kula da bareyi sa'ad da suke haihuwa? 2Ko za ka iya ƙidaya watannin da suke ɗauke da 'ya'yansu? Ka san lokacin da suke haihuwa? 3Sukan tsugunna su haihu; zafin naƙudarsu kuma ya ƙare. 4'Ya'yansu sukan yi ƙarfi a fili; sukan tafi, ba sa kuma dawowa.
5“Wane ne ya 'yantar da jakin jeji? Wane ne ya kunce igiyoyin jaki mai sauri, 6wanda na ba shi jeji yă zama masa gida, na kuma ba shi ƙasar gishiri tă zama mazauninsa? 7Yana reni surutun birni, ba ya kuma jin ihun mai korarsa. 8Yana yawo a duwatsu neman wurin kiwonsa, yana neman kowane abu kore.
9“Ko ɓaunar jeji yana niyyar yă bauta maka? Ko zai kwana a bakin kwaminka? 10Ko za ka iya ɗaure ɓaunar jeji da igiyoyi a layin noma? Ko zai yi noma a kwaruruka a bayanka? 11Ko za ka dogara gare shi domin ƙarfinsa mai girma ne? Ko za ka danƙa masa aikinka? 12Ko za ka amince masa yă dawo maka da hatsinka, yă kuma tara shi a masussukarka?
13“Fikafikan jimina suna bugawa da farin ciki, amma ko gashi da fuka-fukansu kamar na shamuwa ne? 14Takan bar ƙwanta a ƙasa, ta kuma bar su su yi ɗumi a cikin ƙura, 15tana mantawa cewa ƙafa za tă iya murƙushe su, ko kuma naman jeji yă tattake su. 16Takan nuna wa 'ya'yanta tsanani, kamar ba nata ba ne; ba ta damu ba ko wahalarta ta zama a banza, 17domin na sa ta manta da hikima, ban kuma ba ta rabo a cikin ganewa ba. 18Duk da haka, sa'ad da ta tashi gudu, takan yi wa doki da mahayinsa dariya.
19“Ko kai ne kake ba wa doki ƙarfinsa? Ko kai ne kake rufe wuyansa da geza mai kaɗawa? 20Ko kai ne kake sa shi yă yi tsalle kamar fāra? Ƙarar hancinsa mai alfahari tana sa razana. 21Yana tono ƙasa da ƙafarsa a kwari, yana farin ciki da ƙarfinsa; yakan ruga zuwa fagen yaƙi. 22Yakan yi wa tsoro dariya, ba ya jin razana; ba ya kuma ja da baya daga takobi. 23Kwarin kibau yana ƙara a gefensa, da māshi mai walƙiya da kuma zogi. 24Da zafin kwaɗayi mai tsananta, yakan haɗiye ƙasa; ba ya iya tsayawa cik sa'ad da ƙaho ya busa. 25Da busar ƙaho, yakan ce, ‘Ahaa!’ Yana jin ƙanshin yaƙi daga nesa, tare da tsawar shugabannin yaƙi da sowar yaƙi.
26“Ko ta wurin ganewarka ne shirwa take tashi sama ta kuma baje fikafikanta wajen kudu? 27Ko bisa umarninka ne gaggafa take firiya ta kuma yi sheƙarta a can sama? 28Tana zama a kan tsauni ta kuma yi gidanta a can, a kan dutsen tsauni, kagararta. 29Daga can take neman abincinta; idanunta na hange shi daga nesa. 30'Ya'yanta suna shan jini, kuma duk inda waɗanda aka kashe suke, nan take.”