Ruhuna Ya Karye
Ruhunsa ya karye, kabari kuma yana kama da gadon da aka shimfiɗa. Ya tambaya wa zai tsaya masa lamuni, tun da babu ko aboki ɗaya da yake da hikimar bayarwa. In dole ne ya kira rami ubansa, tsutsa kuma uwarsa, ina begensa yake?
17 1“Ruhuna ya karye, kwanakina sun ƙare, kabari yana shirye domina. 2Hakika masu ba'a sun kewaye ni, idanuna kuma ba sa kawar da kai daga tsokanarsu.
3“Ka sa mini jingina a wurinka; wa dabam zai ba da kalmarsa yă zama lamunina? 4Gama ka rufe zukatansu ga fahimta; saboda haka ba za ka bar su su yi nasara ba. 5Wanda ya ci amanar abokansa domin ribar kansa—idanun 'ya'yansa za su dushe.
6“Ya mai da ni abin ba'a a cikin mutane, wani wanda ake tofa masa miyau a fuska. 7Idona ya dushe saboda baƙin ciki, dukan gaɓoɓina kuma suna kama da inuwa. 8Masu adalci sun firgita da wannan, marar laifi kuma ya tasar wa marar tsoron Allah. 9Duk da haka mai adalci yana riƙe da hanyarsa, mai tsabtar hannu kuma yana ƙara ƙarfi gaba gaba.
10“Amma ku dawo, dukanku, ku zo yanzu—ban sami ko mutum guda mai hikima a cikinku ba. 11Kwanakina sun wuce, shirye-shiryena sun karye, tare da su kuma sha'awoyin zuciyata. 12Sun mai da dare rana; ‘haske,’ suka ce, ‘ya kusa’—a gaban duhu. 13Idan ina sa zuciya ga kabari yă zama gidana, idan na shimfiɗa gadona cikin duhu, 14idan na ce wa rami, ‘Kai ne mahaifina,’ da kuma wa tsutsa, ‘Mahaifiyata’ da ‘'Yar'uwata,’ 15to ina begena yake? Wa zai iya ganin wani bege domina? 16Zai gangara zuwa ƙofofin kabari ne? Za mu sauka tare cikin ƙura ne?”