Bildad Ya Sāke Magana
Bildad ya ji haushin a ɗauke su kamar shanu, ya amsa da shiryayyen jawabi game da ƙarshen mugaye: an kashe fitilarsa, tarko a diddigensa, babu zuriyar da ta ragu da rai. Kowane hoto yana faɗa a kan mutumin da ya gama binne 'ya'yansa ke nan.
18 1Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa ya ce, 2“Har yaushe za ka yi ta neman kalmomi? Ka yi hankali, sa'an nan za mu iya magana. 3Don me ake ɗaukarmu kamar dabbobi, ana kirgamu a matsayin wawaye a gabanka? 4Kai da kake yayyage kanka cikin fushinka—ya kamata a yashe duniya saboda kai, ko a matsar da dutse daga wurinsa? 5Hakika, an kashe hasken mugu, harshen wutarsa kuma ya dushe. 6Haske ya yi duhu a tentinsa, fitilar da ke samansa kuma ta mutu. 7An datse ƙarfin takawansa, dabarunsa kuma sun kā da shi. 8Ƙafafunsa ne suka tura shi cikin taru, yana kuma tafiya kai tsaye cikin ragarsa. 9Tarko ya kama shi a diddige; mataku ya riƙe shi sosai. 10An ɓoye masa igiyar tarko a ƙasa, an kuma sa masa tarko a kan hanyarsa. 11Abubuwan razana suna tsorata shi ta kowane gefe, suna kuma binsa daga baya. 12Yunwa ta cinye ƙarfinsa, masifa kuma tana a shirye don faɗuwarsa. 13Tana cinye sassan fatarsa; ɗan farin mutuwa yana cinye gaɓoɓinsa. a a v13 “Ɗan farin mutuwa” kalmar waƙa ce da take nufin wata cuta mai kisa, mai sa mutum ya raunana — wakilin mutuwa mafi muni. 14An ciro shi daga amincin tentinsa, an kuma kai shi gaban sarkin razana. 15Wuta ta zauna a tentinsa, wanda ba nasa ba ne; an kuma barbaza kibiritu mai ci a kan gidansa. 16Saiwoyinsa sun bushe a ƙasa, rassansa kuma sun yanƙwane a sama. 17Tunawa da shi ya ɓace daga duniya, ba shi kuma da suna a tituna. 18An kore shi daga haske zuwa cikin duhu, an kuma fitar da shi daga duniya. 19Ba ya barin ɗa ko jika a cikin mutanensa, babu mai tsira a inda ya taɓa zama. 20Mazaunan yamma sun firgita game da abin da ya faɗa masa, mazaunan gabas kuma razana ta kama su. 21Hakika, haka ƙarshen gidajen mugaye yake, wurin mutumin da bai san Allah ba.”