Yanzu a bugun takarda

Ayuba 16 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Masu Ta'aziyya Marasa Amfani

Ayuba ya kira su masu ta'aziyya na wahala, ya ce shi ma zai iya yin jawabai, da a ce an musanya matsayinsu. Ya kwatanta Allah kamar jarumin yaƙi wanda ya kama shi a wuya ya kafa shi abin harbi. Duk da haka ya nace cewa akwai mai shaida masa a sama.

Babi na 16.

Sai Ayuba ya amsa ya ce, “Na ji abubuwa da yawa irin waɗannan; dukanku masu ta'aziyya marasa amfani ne. Maganganunku na iska ba su da iyaka ne? Me ya tsokane ku har kuke ci gaba da amsa? Ni ma zan iya magana kamar ku, in kuna wurina; zan iya tara kalmomi a kanku, in kuma kaɗa muku kai. Amma da zan ƙarfafa ku da bakina, ta'aziyyar leɓunana kuma za ta sauƙaƙa muku zafi. In na yi magana, zafina ba ya sauƙi; in kuma na yi shiru, me zai rabu da ni? Lalle yanzu Allah ya gajiyar da ni; ka hallaka dukan jama'ata. Ka tsuke ni, wannan kuma ya zama shaida; ramewata ta tashi gāba da ni, tana ba da shaida a fuskata. Fushinsa ya yayyage ni, ya kuma auka mini; ya ciji haƙoransa a kaina; maƙiyina ya zura mini ido. Mutane sun buɗe bakunansu a kaina; sun mare ni a kumatu da reni; sun haɗa kai su yaƙe ni. Allah ya ba da ni ga marasa adalci, ya kuma jefa ni cikin hannun mugaye. Ina cikin kwanciyar hankali, sai ya ragargaza ni; ya kama ni a wuya ya kuma farfasa ni; ya mai da ni abin harbinsa. Maharbansa sun kewaye ni; ya tsage ƙodata ba tausayi, ya kuma zuba maɗacina a ƙasa. Yana ragargaza ni da buga bayan buga; yana auka mini kamar jarumi. Na ɗinka tufafin makoki a kan fatata, na kuma binne goshina a ƙura. Fuskata ta yi ja saboda kuka, duhu mai yawa kuma ya rufe fatar idanuna, ko da yake babu zalunci a hannuwana, addu'ata kuma tsarkakakkiya ce. Ya ke ƙasa, kada ki rufe jinina, kada kuma kukata ta sami wurin hutawa. Ko yanzu ma, shaidata tana cikin Sama, mai kāre ni kuma yana can bisa. Abokaina suna mini ba'a; idona yana zubar da hawaye ga Allah, don yă yi roƙo saboda mutum a gaban Allah, kamar yadda ɗan adam yake roƙo saboda maƙwabcinsa. Gama 'yan shekaru kaɗan za su wuce, sa'an nan zan tafi hanyar da ba a dawowa.”