Timoti ya Shiga Aikin
Ubanmu ya kira su ta wahayin wani mutumin Makidoniya. Lidiya ta buɗe gidanta; wata baiwa mai duba ta rasa ruhunta, iyayengijinta kuma suka rasa kuɗin shigarsu. Bayan an yi musu duka aka ɗaure su da sarƙoƙi, Bulus da Sila suka raira waƙa da tsakar dare, girgizar ƙasa ta buɗe ƙofofi, aka kuma yi wa mai gadin kurkukun baftisma.
16 1Bulus ya ci gaba zuwa Darbe da Listira. A can akwai wani almajiri mai suna Timoti, ɗan wata mace Bayahudiya mai bi, amma mahaifinsa Baheleni ne. 2'Yan'uwa a Listira da Ikoniyum suna yabonsa. 3Bulus yana so yă tafi tare da shi, saboda haka ya ɗauke shi ya yi masa kaciya, saboda Yahudawan waɗannan wurare, gama duk sun san mahaifinsa Baheleni ne. 4Sa'ad da suke ratsa garuruwan, suka ba su ƙa'idodin da manzanni da dattawa a Urushalima suka kafa, domin su kiyaye su. 5Saboda haka ikkilisiyoyi suka ƙarfafa cikin bangaskiya, suka kuma riƙa ƙaruwa a yawansu kullum.
Uba ya Kira su zuwa Makidoniya
6Suka ratsa yankin Firijiya da Galatiya, da yake Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin maganar a Asiya. 7Da suka isa Misiya, suka yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai bar su ba. 8Saboda haka suka wuce Misiya, suka gangara zuwa Taruwasa. 9Da dare Bulus ya ga wahayi: wani mutumin Makidoniya ya tsaya yana roƙonsa, “Ka ƙetare zuwa Makidoniya ka taimake mu.” 10Da ya ga wahayin, nan da nan muka nemi mu tashi zuwa Makidoniya, muka tabbata Ubanmu ya kira mu domin mu yi musu bishara.
Lidiya ta Buɗe Zuciyarta a Filibi
11Saboda haka muka shiga jirgin ruwa daga Taruwasa, muka miƙe zuwa Samotaresi, kashegari kuma zuwa Niyafolis, 12daga can kuma zuwa Filibi, babban birnin wannan yankin Makidoniya, mallakar Roma. Muka zauna a can kwanaki da dama.
13A ranar Asabar muka fita waje da ƙofar gari zuwa wani kogi, muna tsammani akwai wurin addu'a a can. Muka zauna muka yi magana da matan da suka taru a wurin. 14Wata mace mai suna Lidiya, daga Tiyatira, mai sayar da shunayyar tufa, mai bautar Ubanmu, tana sauraro. Ubangiji ya buɗe zuciyarta ga maganar Bulus. 15Da aka yi mata baftisma ita da iyalinta, sai ta roƙe mu, “In kun ɗauke ni mai aminci ga Ubangiji, ku zo gidana ku sauka.” Ta kuma rinjaye mu.
An Daure su saboda Bishara
16Yayinda muke tafiya wurin addu'a, sai muka sadu da wata baiwa mai aljanin duba; takan sami wa masu ita riba mai yawa ta wurin duba. 17Ta bi Bulus da mu, tana ihu, “Waɗannan mutane bayin Allah Maɗaukaki ne, suna sanar da ku hanyar ceto.” 18Ta yi haka kwanaki da yawa. Bulus ya ɓata rai ƙwarai, sai ya juya ya ce wa aljanin, “Na umarce ka da sunan Yesu Almasihu, ka fito daga gare ta.” Nan take ya fito.
19Da masu ita suka ga begen ribarsu ya ɓace, sai suka kama Bulus da Sila, suka ja su zuwa kasuwa a gaban masu mulki. 20Suka kawo su wurin alƙalai, suka ce, “Waɗannan mutane Yahudawa ne, suna tada hankalin birninmu. 21Suna yaɗa al'adun da bai dace mu Romawa mu karɓa ko mu aikata ba.”
22Taron suka haɗu suka fāɗa musu, alƙalai kuma suka tsage tufafin Bulus da Sila, suka ba da umarni a yi musu dūka da sanduna. 23Bayan sun yi musu dūka kam, sai suka jefa su cikin kurkuku, suka umarci mai gadin kurkuku yă tsare su sosai. 24Da ya sami wannan umarni, sai ya kulle su a ɗakin ciki, ya kuma sa ƙafafunsu a turu.
25Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu'a suna raira waƙoƙin yabo ga Ubanmu, 'yan kurkuku kuma suna sauraronsu. 26Ba zato ba tsammani sai wata girgizar ƙasa mai ƙarfi ta girgiza harsashen kurkukun; nan take dukan ƙofofi suka buɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka kunce. 27Mai gadin kurkuku ya farka, ya ga ƙofofin kurkuku a buɗe, sai ya zāre takobinsa yana nufin yă kashe kansa, yana tsammani 'yan kurkuku sun gudu. 28Amma Bulus ya yi ihu, “Kada ka cuci kanka, gama dukanmu muna nan!”
29Mai gadin kurkuku ya nemi fitilu, ya ruga ciki, ya kuma faɗi yana rawar jiki a gaban Bulus da Sila. 30Sa'an nan ya fito da su waje ya ce, “Ya shugabanni, me zan yi don in sami ceto?”
31Suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka kuwa sami ceto, kai da iyalinka.” 32Suka yi masa maganar Ubangiji, shi da duk waɗanda suke gidansa. 33A wannan sa'a ta dare, ya ɗauke su ya wanke musu raunukansu; sa'an nan nan take aka yi masa baftisma shi da dukan iyalinsa. 34Ya kawo su gidansa, ya shimfiɗa musu abinci, ya kuma yi farin ciki ƙwarai tare da dukan iyalinsa saboda sun gaskata da Ubanmu.
35Amma da safiya ta yi, sai alƙalai suka aiki 'yan sanda, suna cewa, “Ku saki waɗannan mutane.”
36Mai gadin kurkuku ya gaya wa Bulus, “Alƙalai sun aiko da umarni a sake ku. Yanzu ku fito, ku tafi lafiya.”
37Amma Bulus ya ce musu, “Sun yi mana dūka a bainar jama'a, ba tare da shari'a ba, mu da muke 'yan ƙasar Roma, suka kuma jefa mu cikin kurkuku. Yanzu suna so su fitar da mu a ɓoye? A'a! Su kansu su zo su fito da mu.”
38'Yan sanda suka kai wa alƙalai waɗannan kalmomi, suka kuma ji tsoro da suka ji su 'yan ƙasar Roma ne. 39Suka zo suka nemi gafara, suka fito da su, suka kuma roƙe su su bar birnin. 40Saboda haka suka bar kurkuku suka tafi gidan Lidiya. A can suka ga 'yan'uwa, suka ƙarfafa su, sa'an nan suka tafi.