Ba a Iya Dakatar da Hasken Uba
Fitilar zinariya da itatuwan zaitun biyu ke ciyarwa ta amsa karayar zuciyar Zarubabel game da ƙaramin haikali da ba a gama ba. Maganar Ubanmu gare shi: ba ta wurin iko ba, ba kuma ta wurin ƙarfi ba, amma ta wurin Ruhuna. Hannuwan da suka kafa harsashin za su gama shi; kada kowa ya raina ƙananan abubuwa.
4 1Sai mala'ikan da yake magana da ni ya dawo, ya tashe ni, kamar yadda akan tashe mutum daga barci. 2Ya tambaye ni, “Me kake gani?” Na ce, “Ina ga alkukin fitila na zinariya, da kwano a bisansa, da fitilu bakwai, da bututu bakwai ga kowace fitila a bisa.
3Itatuwan zaitun biyu suna tsaye kusa da shi, ɗaya a dama ta kwanon, ɗayan kuma a hagunsa.”
4Sai na ce wa mala'ikan da yake magana da ni, “Mene ne waɗannan, ranka ya daɗe?”
5Sai mala'ikan da yake magana da ni ya ce, “Ba ka san abin da waɗannan suke ba?” Na ce, “A'a, ranka ya daɗe.”
6Ya ce mini, “Ga maganar da Ubanmu ya yi wa Zerubabel, Ba da ƙarfi ba, ba kuma da iko ba, sai dai ta wurin Ruhuna, in ji Uban rundunonin Sama. 7Wane ne kai, babban dutse? A gaban Zerubabel za ka zama fili. Zai fitar da dutsen kan gini yana ihu, ‘Alheri, alheri gare shi!’
8Sai maganar Ubanmu ta zo mini, cewa,
9Hannuwan Zerubabel ne suka kafa harsashin gidan nan; hannuwansa kuma za su gama shi. Sa'an nan za ku sani Uban rundunonin Sama ne ya aiko ni gare ku. 10Wa ya rena ranar ƙananan abubuwa? Za su yi murna, sa'ad da suka ga igiyar awo a hannun Zerubabel. Waɗannan bakwai idanun Ubanmu ne, waɗanda suke kewaya duniya duka.”
11Sai na tambaye shi, “Mene ne itatuwan zaitun biyun nan da suke dama da hagu na alkukin fitila?” 12Na sāke tambaya, “Mene ne rassan zaitun biyun nan da suke kusa da bututun zinariya biyun da suke zuba man zinariya?”
13Ya ce mini, “Ba ka san abin da waɗannan suke ba?” Na ce, “A'a, ranka ya daɗe.”
14Ya ce, “Waɗannan su ne shafaffu biyu da suke tsaye kusa da Ubangijin dukan duniya.”