Samson Ya Ɗauke Ƙofofin Garin Gaza
Samson ya ɗauke ƙofofin Gaza, sa'an nan ya ƙaunaci Delila, wadda aka biya ta don ta gano asirinsa. Bayan ƙarya uku ya faɗa mata dukan zuciyarsa, ya farka da aske kansa, bai kuwa san Ubanmu ya rabu da shi ba. Makaho a injin niƙa, gashinsa ya sāke tsirowa, ya kuma roƙi ƙarfi kuma.
16 1Samson ya tafi Gaza, a can kuwa ya ga wata karuwa, ya kuma kwana da ita. 2Da mutanen Gaza suka ji, “Samson ya zo nan,” sai suka kewaye wurin, suna jiransa dukan dare a ƙofar gari. Suka yi tsit dukan dare, suna cewa, “Da gari ya waye za mu kashe shi.” 3Samson ya kwanta a can har tsakar dare. Da tsakar dare ya tashi, ya kama ƙofofin ƙofar gari da madogaransu biyu, ya tumɓuke su tare da sandan ƙullewa, ya ɗora su a kafaɗunsa, ya kuma ɗauke su zuwa kan tudun da yake fuskantar Hebron.
4Bayan haka ya ƙaunaci wata mace a Kwarin Sorek, wadda sunanta Delila. 5Sai shugabannin Filistiyawa suka zo wurinta suka ce, “Ki rarrashe shi ki gane inda babban ƙarfinsa yake, da yadda za mu iya rinjayarsa mu daure shi domin mu ƙasƙantar da shi. Kowannenmu zai ba ki kuɗin azurfa dubu ɗaya da ɗari.”
6Delila ta ce wa Samson, “Gaya mini inda babban ƙarfinka yake, da yadda za a iya daure ka a ƙasƙantar da kai.”
7Samson ya ce mata, “In an daure ni da sabbin igiyoyin baka bakwai, waɗanda ba su bushe ba tukuna, zan raunana in zama kamar kowane mutum.”
8Sai shugabannin Filistiyawa suka kawo mata sabbin igiyoyin baka bakwai, waɗanda ba su bushe ba tukuna, ta kuma daure shi da su. 9Ta kuwa sa mutane a ɓoye a cikin ɗaki. Ta ce masa, “Filistiyawa sun auko maka, Samson!” Amma ya tsintsinke igiyoyin baka kamar yadda zaren lilin yakan tsinke sa'ad da ya taɓa wuta. Ta haka ba a gano asirin ƙarfinsa ba.
10Delila ta ce wa Samson, “Ka yi mini ba'a ka kuma gaya mini ƙarya. Yanzu ka gaya mini yadda za a iya daure ka.”
11Ya ce mata, “In an daure ni ƙankan da sababbin igiyoyi waɗanda ba a taɓa amfani da su ba, zan raunana, kamar kowane mutum.”
12Delila ta ɗauki sababbin igiyoyi ta daure shi da su, tana cewa, “Samson, Filistiyawa sun auko maka!” Mutane kuwa suna a ɓoye a cikin ɗaki. Amma ya tsintsinke igiyoyin daga hannuwansa kamar zare.
13Delila ta ce wa Samson, “Ka yi mini ba'a ka kuma yi mini ƙarya dukan wannan lokaci. Gaya mini yadda za a iya daure ka.” Ya ce mata, “In kika saƙa kitso bakwai na kaina cikin yadin masaƙa kika kuma kafa shi da ƙarfi, zan raunana kamar kowane mutum.”
14Ta kafa shi da ƙusa ta kuma ce masa, “Samson, Filistiyawa sun auko maka!” Amma ya farka daga barcinsa ya zāre ƙusar, da masaƙar, da yadin.
15Ta ce, “Yaya za ka ce ‘Ina ƙaunarki’ alhali zuciyarka ba ta tare da ni? Sau uku ke nan ka yi mini ba'a ba ka kuma gaya mini inda babban ƙarfinka yake ba.”
16Da ta matsa masa ƙwarai da kalmominta kullum, tana ta matsa masa, sai ya gaji ƙwarai har ya yi marmarin ya mutu. 17Sai ya gaya mata dukan zuciyarsa, “Ba reza da ta taɓa kaina ba, gama Banazare ne ni na Ubanmu tun daga cikin mahaifiyata. In an aske ni, ƙarfina zai rabu da ni, in kuma raunana, kamar kowane mutum.”
18Da Delila ta ga ya gaya mata dukan zuciyarsa, sai ta aika a kira shugabannin Filistiyawa, “Ku sāke zuwa sau ɗaya kuma, gama ya gaya mini dukan zuciyarsa.” Sai suka zo wurinta da azurfar a hannuwansu. 19Ta sa shi barci a kan cinyoyinta, ta kira wani mutum, ta sa shi ya aske kitso bakwai na kansa. Ta kuma fara ƙasƙantar da shi, ƙarfinsa kuwa ya rabu da shi. 20Ta ce, “Filistiyawa sun auko maka, Samson!” Ya farka daga barcinsa yana tsammani, “Zan fita kamar dā in kuɓutar da kaina.” Amma bai san Ubanmu ya rabu da shi ba.
21Filistiyawa suka kama shi, suka ƙwaƙule masa idanu, suka kuma kawo shi Gaza. Suka daure shi da ƙuƙumman tagulla, ya kuma yi niƙa a kurkuku. 22Amma gashin kansa ya fara sāke tsirowa bayan an aske shi.
Uba Ya Sāke Ƙarfafa Samson Sau Ɗaya Kuma
23Sai shugabannin Filistiyawa suka taru domin su miƙa babbar hadaya ga Dagon allahnsu, su kuma yi biki, suna cewa, “Allahnmu ya bashe Samson maƙiyinmu a hannunmu.” 24Da mutane suka gan shi, suka yabi allahnsu, suna cewa, “Allahnmu ya bashe maƙiyinmu a hannunmu, wanda ya lalatar da ƙasarmu ya kuma ƙara yawan waɗanda ya kashe.”
25Da zukatansu suka yi farin ciki, sai suka ce, “A kira Samson yă nishaɗantar da mu.” Sai suka fito da Samson daga kurkuku, ya kuma nishaɗantar da su. Suka tsai da shi tsakanin ginshiƙai. 26Samson ya ce wa yaron da yake riƙe da hannunsa, “Bar ni in taɓa ginshiƙan da gidan yake kafe a kai, domin in jingina a kansu.” 27Gidan kuwa cike yake da maza da mata; dukan shugabannin Filistiyawa suna can, a kan rufin kuma wajen maza da mata dubu uku suna kallon Samson yana nishaɗi. 28Sai Samson ya kira ga Ubanmu, “Ya Uba Mai Iko Duka, ka tuna da ni, ina roƙonka. Ka ƙarfafa ni sau ɗaya kawai yanzu, domin da bugu ɗaya in yi wa Filistiyawa adalci saboda idanuna biyu.” 29Samson ya kama ginshiƙai biyu na tsakiya waɗanda suke riƙe da gidan, ya kuma jingina a kansu, hannunsa na dama a kan ɗaya, na hagu kuma a kan ɗaya. 30Samson ya ce, “Bar in mutu tare da Filistiyawa.” Ya tura da dukan ƙarfinsa, sai gidan ya faɗo a kan shugabanni da dukan mutanen da suke cikinsa. Ta haka ya kashe mutane da yawa a mutuwarsa fiye da waɗanda ya kashe a lokacin ransa.
31'Yan'uwansa da dukan gidan mahaifinsa suka gangaro, suka ɗauke shi, suka kuma kawo shi sama, suka binne shi tsakanin Zora da Eshtawol a kabarin mahaifinsa Manowa. Ya yi wa Isra'ila shari'a shekara ashirin.