Ayuba Ya Amsa
Ayuba ya yarda cewa Allah ya fi ƙarfin a yi gardama da shi, matsalar kuwa ke nan. Ba wanda zai iya kiran shi zuwa ɗakin shari'a, ko bakin marar aibi ma zai hukunta shi. Ayuba ya ce Allah yana hallaka marar aibi da mugu duka, yana kuma marmarin wani mai shiga tsakani da zai ɗora hannu a kan su biyu.
9 1Sai Ayuba ya amsa ya ce, 2“Hakika na sani cewa haka yake. Amma yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? 3Idan mutum ya so yă yi gardama da shi, ba zai iya amsa masa sau ɗaya cikin dubu ba. 4Shi mai hikima ne a zuciya, mai iko kuma a ƙarfi—wane ne ya taɓa yi masa tawaye ya kuma fita lafiya? 5Yakan kawar da duwatsu kafin su sani, yana juya su a cikin fushinsa. 6Yakan girgiza duniya daga wurinta, ginshiƙanta kuma suna rawa. 7Yakan umarci rana, ba kuwa ta fitowa; yakan rufe taurari. 8Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai, yana kuma tattaka raƙuman ruwan teku. 9Shi ne ya yi taurarin Beyar, da Oriyon, da Fileyadis, da ƙungiyoyin taurari na sararin kudu. 10Yakan aikata manyan abubuwa waɗanda ba a iya ganewa, da abubuwan banmamaki waɗanda suka wuce ƙidaya. 11Ga shi—yakan wuce ni, ban kuwa gan shi ba; yakan yi gaba, amma ban gane shi ba. 12Idan ya ƙwace, wa zai iya mayar da shi? Wa zai ce masa, ‘Me kake yi?’ 13Allah ba zai janye fushinsa ba; a ƙarƙashinsa mataimakan Rahab, dodon teku, suka durƙushe a ragargaje. a a v13 Rahab a nan ba matar Yariko ba ce, sai dai tsohon suna ne na dodon teku mai hargitsi — kwatancin waƙa na kowane iko da yake gāba da Allah. 14Balle ni, yaya zan amsa masa, ko in zaɓi kalmomina don in yi gardama da shi? 15Ko da ina da gaskiya, ba zan iya amsa masa ba; sai dai in roƙi alƙalina jinƙai. 16Da na kira shi, ya kuwa amsa mini, da ban gaskata cewa yana sauraron muryata ba. 17Gama yakan ragargaza ni da hadari, yana kuma ƙara mini raunuka ba dalili. 18Ba ya bar ni in sami numfashi, sai dai yă cika ni da ɗaci. 19In batun ƙarfi ne, shi ne mai iko! In kuwa batun shari'a ne, wa zai iya kiran shi zuwa shari'a? 20Ko da ina da gaskiya, bakina zai hukunta ni; ko da ba ni da laifi, zai nuna ni mai karkata. 21Ba ni da laifi; ban damu da kaina kuma ba; na ƙi raina. 22Duk ɗaya ne; saboda haka na ce, yakan hallaka marar laifi da mugu duka. 23Sa'ad da masifa ba zato ta kawo mutuwa, yakan yi dariyar baƙin cikin marar laifi. 24An ba da duniya ga mugaye; yakan rufe idanun alƙalanta. In ba shi ba ne, to wa ke yi? 25Kwanakina sun fi mai gudu sauri; suna gudu, ba sa ganin wani alheri. 26Suna shuɗewa kamar jiragen ruwa na kyauro, kamar gaggafa mai sheƙowa a kan ganimarta. 27In na ce, ‘Zan manta da gunagunina, zan kawar da ɓacin fuskata, in yi farin ciki,’ 28Ina tsoron dukan zafuffukana, gama na sani ba za ka ɗauke ni marar laifi ba. 29Za a hukunta ni; don me zan wahalar da kaina a banza? 30Ko da na wanke kaina da ƙanƙara na kuma tsabtace hannuwana da sabulu, 31duk da haka za ka jefa ni cikin rami, tufafina kuma su yi ƙyamata. 32Gama shi ba mutum ba ne kamar ni, da zan amsa masa, da za mu tafi shari'a tare. 33Babu matsakanci a tsakanin mu, wanda zai iya ɗora hannunsa a kanmu biyu. b b v33 Ayuba yana marmarin wani wanda zai iya tsayawa tsakaninsa da Allah — matsakanci da zai iya ɗora hannu a kan dukansu. Wannan marmari ya sami amsa a cikin Yesu, matsakanci guda tsakanin Allah da mutane (1 Timoti 2:5). 34Bari yă ɗauke sandarsa daga gare ni, kada kuma tsoronsa yă sāke firgita ni. 35Sa'an nan zan yi magana ba tare da tsoronsa ba; amma a yadda yake, ban sami 'yancin yin haka ba.”