Sha'awarsa Tana Gare Ni
Mutumin yana yabonta tun daga ƙafafunta masu takalmi har gashinta, yana jin daɗinta a fili. Ba ta kau da yabon ba. Ta ce sha'awar ta juna ce, kuma tata ce, sa'an nan ta fitar da shi zuwa gonakin inabi da ƙauyuka, inda ta ajiye masa 'ya'yan itace.
7 1Kai, ƙafafunki suna da kyau cikin takalma, ya 'yar sarauta! Lanƙwasar cinyoyinki kamar kayan ado suke, aikin hannuwan gwani. 2Cibiyarki kwano ne mai zagaye wanda ba ya taɓa rasa ruwan inabi gauraye. Cikinki tarin alkama ne wanda aka kewaye da furannin lili. 3Mamanki biyu kamar 'yan barewa biyu suke, tagwayen barewa. 4Wuyanki kamar hasumiya ta hauren giwa yake. Idanunki tafkuna ne a Heshbon, kusa da ƙofar Bat-rabbim. Hancinki kamar hasumiyar Lebanon yake, mai fuskantar Damascus. 5Kanki a bisanki kamar dutsen Karmel yake, gashin kanki mai sassauƙa kamar shunayya yake; an ɗaure sarki a cikin kitsonsa. 6Kai, yadda kike da kyau, yadda kuma kike da daɗi, ke, ƙaunatacciyata, da dukan annashuwarki! 7Tsayinki kamar itacen dabino yake, mamanki kuma kamar tarin 'ya'yansa. 8Na ce, “Zan hau itacen dabino in kama 'ya'yansa.” Bari mamanki su zama kamar tarin 'ya'yan inabi, ƙamshin numfashinki kuma kamar na tuffa, 9bakinki kuma kamar ruwan inabi mafi kyau yake. Yana gudu sumul domin ƙaunataccena, yana shaƙuwa a hankali bisa leɓuna da haƙora.
10Ni ta ƙaunataccena ce, sha'awarsa kuma tana gare ni. 11Zo, ƙaunataccena, bari mu fita zuwa gonaki mu kwana a ƙauyuka. 12Bari mu tashi da sassafe zuwa gonakin inabi mu ga ko itatuwan inabi sun toho, ko furanni sun buɗe, ko kuma rumman ya yi fure. A can zan ba ka ƙaunata. 13'Ya'yan mandireki suna ba da ƙamshinsu, bisa ƙofofinmu kuma akwai dukan 'ya'ya mafi kyau, sababbi da tsoffi, waɗanda na ajiye maka, ƙaunataccena. a a v13 Mandireki tsirrai ne masu ƙamshi, waɗanda a zamanin dā aka yi imani sosai cewa suna tā da sha'awar ƙauna suna kuma ƙara haihuwa.