Yesu Ya Kira Almajiransa na Farko
Bitrus ya yi kamun kifi dukan dare bai kama kome ba, sa'an nan bisa ga maganar Yesu ya jawo kifi mai yawa har ya roƙe shi ya rabu da shi. Aka taɓa wani mutum mai kuturta. Aka saukar da wani shanyayye ta rufin gida, aka gafarta masa ta wurin ikon Ubanmu, abin da ya ɓata wa malaman Attaura rai. Lawi ya bar wurin karɓar haraji.
5 1Wata rana, sa'ad da taron mutane suke matsawa kewaye da shi domin su ji maganar Ubanmu, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Janisaret. a a v1 Tafkin Janisaret wani suna ne na Tekun Galili. 2Ya ga kwale-kwale biyu tsaye a bakin tafkin; masuntan kuwa sun fito daga cikinsu, suna wanke tarunansu. 3Sai ya shiga ɗaya daga cikin kwale-kwalen, wato na Siman, ya roƙe shi yă tura shi kaɗan daga gaɓar ruwa. Sa'an nan ya zauna, yana koya wa taron daga cikin kwalen.
4Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, “Tura kwalen zuwa inda ruwa ya yi zurfi, ku kuma zura tarunanku domin kamun kifi.”
5Siman ya amsa ya ce, “Ya Shugaba, mun yi aiki dukan dare, ba mu kama kome ba. Amma bisa ga maganarka, zan zura tarunan.” 6Da suka yi haka, sai suka kama kifi mai yawa ƙwarai har tarunansu suka fara yagewa. 7Sai suka yi alama wa abokan aikinsu da ke cikin ɗaya kwalen su zo su taimaka. Suka kuwa zo, suka cika kwale-kwalen biyu har suka fara nutsewa. 8Da Siman Bitrus ya ga haka, sai ya fāɗi a gwiwoyin Yesu ya ce, “Ka rabu da ni, Ubangiji, gama ni mai zunubi ne!” 9Gama mamaki ya kama shi da dukan waɗanda suke tare da shi saboda yawan kifin da suka kama,
10haka kuma Yaƙub da Yohanna, 'ya'yan Zabadi, abokan aikin Siman. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro; daga yanzu za ka riƙa kamun mutane.”
11Sai suka jā kwale-kwalensu zuwa gaɓar ruwa, suka bar kome, suka bi shi.
An Tsarkake Wani Mutum
12Wata rana sa'ad da Yesu yake cikin wani gari, sai ga wani mutum cike da muguwar cutar fata a jikinsa. Da ya ga Yesu, sai ya fāɗi rubda ciki ya roƙe shi ya ce, “Ya Ubangiji, in kana so, kana iya tsarkake ni.”
13Sai Yesu ya mīƙa hannunsa, ya taɓa shi, ya ce, “Ina so. Ka tsarkaka.” Nan da nan cutar fatan ta rabu da shi.
14Yesu ya umarce shi kada yă gaya wa kowa, “Amma ka tafi, ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayar da Musa ya umarta saboda tsarkakewarka, yă zama shaida ga mutane.”
15Amma labarinsa ya ƙara bazuwa; taron mutane masu yawa suka taru domin su ji shi, su kuma sami warkarwa daga cututtukansu. 16Amma Yesu yakan janye zuwa wuraren da ba kowa domin yă yi addu'a.
Ikon Uba na Gafarta Zunubai
17Wata rana sa'ad da yake koyarwa, waɗansu Farisiyawa da malaman shari'a suna zaune, waɗanda suka zo daga kowane ƙauye na Galili, da kuma daga Yahudiya da Urushalima. Ikon Ubanmu kuwa yana tare da shi domin yă warkar da marasa lafiya. 18A daidai lokacin, sai ga waɗansu mutane ɗauke da wani shanyayye a kan tabarma, suna ƙoƙari su kawo shi ciki su sa shi a gaban Yesu. 19Da suka kāsa samun hanyar shigar da shi saboda taron, sai suka hau kan rufin gida, suka saukar da shi tare da tabarmarsa ta cikin rufin, zuwa tsakiyar jama'a, a gaban Yesu kai tsaye.
20Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Aboki, an gafarta maka zunubanka.”
21Sai malaman dokoki da Farisiyawa suka fara muhawara, suna cewa, “Wane ne wannan mutum mai saɓon Allah? Wa ya isa yă gafarta zunubai sai Allah shi kaɗai?”
22Da Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya amsa musu ya ce, “Don me kuke tunani a zukatanku? 23Wanne ne mafi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya’? 24Amma domin ku san Ɗan Mutum yana da iko a duniya na gafarta zunubai,” —sai ya ce wa shanyayyen— “ina gaya maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.”
25Nan da nan sai ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da ya kwanta a kai, ya tafi gida yana ɗaukaka Ubanmu. 26Mamaki ya kama dukansu, suka ɗaukaka Ubanmu, cike da tsoro, suna cewa, “Yau mun ga abubuwan al'ajabi.”
Yesu Ya Kira Lawi
27Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji mai suna Lawi zaune a wurin karɓar haraji. Sai ya ce masa, “Bi ni.”
28Sai Lawi ya tashi, ya bar kome, ya bi shi. 29Sa'an nan Lawi ya shirya wa Yesu babban biki a gidansa, taro mai yawa na masu karɓar haraji da waɗansu kuma suna zaune suna cin abinci tare da su. 30Amma Farisiyawa da malaman dokokinsu suka yi gunaguni ga almajiransa, suna cewa, “Don me kuke ci kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubai?”
31Yesu ya amsa musu ya ce, “Masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. 32Ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubai su tuba.”
Tambaya game da Azumi
33Sai suka ce masa, “Almajiran Yohanna sukan yi azumi sau da yawa suna kuma addu'a, haka ma almajiran Farisiyawa, amma naka suna ci suna sha.”
34Yesu ya ce, “Ko za ku iya sa abokan ango su yi azumi tun yana tare da su? 35Amma kwanaki za su zo sa'ad da za a ɗauke ango daga gare su, a lokacin nan ne kuwa za su yi azumi a waɗannan kwanaki.”
36Ya kuma ba su wani misali ya ce, “Ba wanda yakan yage ɓalle daga sabuwar riga yă dinka a kan tsohuwa. In ba haka ba, zai yage sabuwar, ɓallen sabuwar kuma ba zai dāce da tsohuwar ba. 37Ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna; in ba haka ba, sabon ruwan inabin zai farfashe salkunan, yă zube, salkunan kuma su lalace. 38A'a, dole a zuba sabon ruwan inabi a cikin sababbin salkuna. 39Ba kuwa wanda bayan ya sha tsohon ruwan inabi yake son sabo, gama yakan ce, ‘Tsohon ya fi kyau.’”