Kwaɗi Suka Mamaye Ƙasar
Kwaɗi sun cika murhu da gadaje, Fir'auna kuma ya ce gobe ne lokacin samun sauƙi, sa'an nan ya taurare zuciyarsa da zarar ya samu. Ƙura ta zama kwarkwata waɗanda masu sihiri ba su iya kwaikwayo ba. Da ƙudaje kuma Ubanmu ya ja layi, ya kiyaye Goshen ba tare da su ba, domin Masar ta san ƙasar wane ne.
8 1Sai Ubanmu ya ce wa Musa, “Ka tafi wurin Fir'auna ka ce masa, ‘Ga abin da Ubanmu ya ce, Ka bar mutanena su tafi, “domin su bauta mini.’”” 2Amma in ka ƙi ka bar su su tafi, zan addabi dukan ƙasarka da kwaɗi. 3Kogin Nilu zai yi cike da kwaɗi, waɗanda za su hau su shiga gidanka, da ɗakin kwananka, da kan gadonka, da gidajen bayinka da na mutanenka, da cikin murhunanka, da cikin kwanonin kullunka. 4Kwaɗin za su hau a kanka, da a kan mutanenka, da a kan dukan bayinka.’ 5Sai Ubanmu ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka miƙa hannunka da sandarka a kan koguna, da rafuffuka, da tafkuna, “ka fito da kwaɗi a kan ƙasar Masar.’””
6Haruna ya miƙa hannunsa a kan ruwayen Masar, sai kwaɗi suka hau suka rufe ƙasar Masar. 7Amma masu sihiri suka yi haka ma da sihirinsu, suka fito da kwaɗi a kan ƙasar Masar.
8Sai Fir'auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Ku roƙi Allah yă kawar da kwaɗin nan daga wurina da mutanena, ni kuwa zan bar mutanen su tafi su yi hadaya ga Allah.”
9Musa ya ce wa Fir'auna, “Daraja taka ce—ka kanka ka ƙayyade lokacin, a yaushe zan yi maka addu'a, da bayinka, da mutanenka, domin a kawar da kwaɗin daga gare ka da gidajenka, su rage a Kogin Nilu kaɗai?”
10“Gobe,” ya ce. Musa ya amsa ya ce, “Kamar yadda ka faɗa, saboda ka san babu wani kamar Ubanmu.
11Kwaɗin za su rabu da kai, da gidajenka, da bayinka, da mutanenka, su rage a Kogin Nilu kaɗai.”
12Musa da Haruna suka bar Fir'auna, Musa kuwa ya yi kuka ga Ubanmu game da kwaɗin da Ubanmu ya kawo wa Fir'auna. 13Ubanmu kuwa ya yi yadda Musa ya roƙa. Kwaɗin suka mutu a cikin gidaje, da harabobi, da gonaki. 14Suka tara su tsibi-tsibi, sai ƙasar ta yi wari. 15Amma da Fir'auna ya ga an sami sauƙi, sai ya taurare zuciyarsa, ya ƙi ya saurare su, yadda Ubanmu ya faɗa.
Ƙwarƙwata Daga Ƙura
16Sai Ubanmu ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, Ka miƙa sandarka ka buga ƙurar ƙasa, “za tă zama ƙwarƙwata a cikin dukan ƙasar Masar.””
17Suka yi haka. Haruna ya miƙa hannunsa da sandarsa ya buga ƙurar ƙasa, sai ƙwarƙwata ta kama mutane da dabbobi. Dukan ƙurar ƙasa ta zama ƙwarƙwata a cikin dukan ƙasar Masar. 18Masu sihiri kuwa suka yi ƙoƙari da sihirinsu domin su fito da ƙwarƙwata, amma suka kāsa. Ƙwarƙwata ta rufe mutane da dabbobi. 19Sai masu sihirin suka ce wa Fir'auna, “Wannan yatsan Allah ne.” Amma zuciyar Fir'auna ta taurare; ya ƙi ya saurare su, yadda Ubanmu ya faɗa.
An Ware Ƙasar Goshen
20Sai Ubanmu ya ce wa Musa, “Ka tashi da sassafe ka tsaya a gaban Fir'auna sa'ad da yake fita zuwa ruwa. Ka ce masa, ‘Ga abin da Ubanmu ya ce, Ka bar mutanena su tafi, domin su bauta mini.
21“In ba ka bar mutanena su tafi ba, zan aiko da ƙudaje a kanka, da a kan bayinka, da mutanenka, da gidajenka. Gidajen Masarawa za su cika da ƙudaje, har ma da ƙasar da suke tsaye a kanta. 22A ranar nan zan keɓe ƙasar Goshen, inda mutanena suke zama, domin kada ƙudaje su kasance a can, domin ka san cewa ni, Ubanka, ina cikin ƙasar. 23Zan bambanta tsakanin mutanena da mutanenka. Gobe wannan alama za tă faru.’”
24Ubanmu kuwa ya yi haka. Kukkumi masu yawa na ƙudaje suka cika gidan Fir'auna da gidajen bayinsa; a cikin dukan ƙasar Masar kuwa, ƙasar ta lalace saboda ƙudajen.
25Sai Fir'auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Ku tafi, ku yi hadaya ga Allahnku a cikin ƙasar nan.”
26Amma Musa ya ce, “Ba daidai ba ne mu yi haka—gama abin da muke yi wa Ubanmu hadaya, abin ƙyama ne ga Masarawa. In muka yanka abin da yake abin ƙyama a gare su a idanunsu, ba za su jajjefe mu da duwatsu ba? 27Dole mu yi tafiyar kwana uku zuwa cikin jeji mu yi hadaya ga Ubanmu, yadda ya umarce mu.”
28Sai Fir'auna ya ce, “Zan bar ku ku tafi ku yi hadaya ga Ubangiji Allahnku a cikin jeji—sai dai kada ku yi nisa sosai. Ku yi mini addu'a.”
29Sai Musa ya ce, “Da zarar na rabu da kai, zan roƙi Ubanmu, gobe kuwa ƙudajen za su rabu da Fir'auna, da bayinsa, da mutanensa. Sai dai kada Fir'auna yă sāke yin ha'inci ta wurin ƙin barin mutanen su tafi su yi hadaya ga Ubanmu.” 30Sai Musa ya fita daga wurin Fir'auna ya roƙi Ubanmu. 31Ubanmu kuwa ya yi yadda Musa ya roƙa, ya kawar da ƙudajen daga wurin Fir'auna, da bayinsa, da mutanensa—babu ko ɗaya da ya rage. 32Amma Fir'auna ya sāke taurare zuciyarsa a wannan lokaci kuma, bai kuwa bar mutanen su tafi ba.