An Naɗa Musa da Haruna
Aka sa Musa ya zama kamar Allah ga Fir'auna, Haruna kuma annabinsa. Da maganar Ubanmu sandan Haruna ya zama maciji ya haɗiye sandunan masu sihiri. Sa'an nan Kogin Nilu, ran Masar, ya zama jini; kifaye suka mutu kogin kuma ya yi wari. Masu sihiri suka kwaikwaya, Fir'auna kuwa bai motsu ba.
7 1Ubanmu ya ce wa Musa, “Ga shi, na mai da kai kamar Allah ga Fir'auna, kuma Haruna ɗan'uwanka zai zama annabinka. 2Za ka faɗa duk abin da na umarce ka; Haruna ɗan'uwanka kuwa zai gaya wa Fir'auna yă saki Isra'ilawa su fita daga ƙasarsa. 3Amma zan taurare zuciyar Fir'auna, in kuma ninka alamuna da al'ajubana a ƙasar Masar. 4Fir'auna ba zai saurare ku ba, saboda haka zan sa hannuna a kan Masar, in fitar da rundunonina—mutanena, zuriyar Isra'ila—daga ƙasar Masar ta wurin manyan hukunce-hukunce. 5Masarawa kuwa za su sani ni ne Uba sa'ad da na miƙa hannuna a kan Masar, na kuma fitar da mutanen Isra'ila daga cikinsu.”
6Musa da Haruna suka yi haka; suka yi daidai kamar yadda Ubanmu ya umarce su. 7Musa yana da shekara tamanin, Haruna kuwa yana da shekara tamanin da uku, sa'ad da suka yi magana da Fir'auna.
8Sai Ubanmu ya ce wa Musa da Haruna,
9sa'ad da Fir'auna ya ce muku, “Ku nuna wani abin al'ajabi,” sai ka ce wa Haruna, “Ɗauki sandanka, ka jefar da shi a gaban Fir'auna, “zai kuwa zama maciji.””
10Musa da Haruna suka tafi wurin Fir'auna suka yi kamar yadda Ubanmu ya umarta. Haruna ya jefar da sandansa a gaban Fir'auna da fādawansa, sai ya zama maciji. 11Sai Fir'auna shi ma ya kirawo masu hikima da masu sihiri, bokayen Masar kuwa suka yi haka da sihirinsu na asiri. 12Kowannensu ya jefar da sandansa, suka zama macizai. Amma sandan Haruna ya haɗiye sandunansu. 13Zuciyar Fir'auna ta taurare; bai saurare su ba, kamar yadda Ubanmu ya faɗa.
Kogin Nilu Ya Zama Jini
14Sai Ubanmu ya ce wa Musa, “Zuciyar Fir'auna ta taurare; ya ƙi yă bar mutane su tafi. 15Ka tafi wurin Fir'auna da safe sa'ad da yake fitowa zuwa ruwa. Ka tsaya a bakin Kogin Nilu don ka same shi, ka kuma riƙe sandan da ya zama maciji a hannunka. 16Ka ce masa, Ubanmu na Ibraniyawa ya aiko ni gare ka, yana cewa, “Ka saki mutanena su tafi su bauta mini a jeji.” Duk da haka har yanzu ba ka saurara ba. 17Ga abin da Ubanmu ya ce, “Ta wurin wannan za ka san ni ne Uba, ga shi, da sandan da yake a hannuna zan bugi ruwan Kogin Nilu, zai kuwa zama jini. 18Kifin da yake cikin Kogin Nilu za su mutu, Kogin Nilu kuwa zai yi wari, Masarawa kuwa ba za su iya shan ruwa daga Kogin Nilu ba.”’” 19Ubanmu ya ce wa Musa, “Ka gaya wa Haruna, Ɗauki sandanka ka miƙa hannunka a kan ruwayen Masar—a kan kogunansu, da magudanai, da tafkuna, da dukan tafkunan ajiyarsu—za su kuwa zama jini. Jini zai cika dukan Masar, har cikin kwanonin itace da na dutse.”
20Musa da Haruna suka yi kamar yadda Ubanmu ya umarta. A gaban Fir'auna da fādawansa, Haruna ya ɗaga sandan ya bugi ruwan Kogin Nilu, dukan ruwansa kuwa ya zama jini. 21Kifin da yake cikin Kogin Nilu suka mutu, Kogin Nilu ya yi wari, Masarawa kuwa ba su iya shan ruwa daga Kogin Nilu ba. Jini kuwa ya kasance a dukan ƙasar Masar. 22Amma bokayen Masar suka yi haka da sihirinsu na asiri. Saboda haka zuciyar Fir'auna ta ci gaba da taurin; bai saurare su ba, kamar yadda Ubanmu ya faɗa. 23Fir'auna ya juya ya shiga gidansa, bai kuwa mai da hankali ko ga wannan ba. 24Dukan Masarawa suka haƙa rijiyoyi kewaye da Kogin Nilu don neman ruwan sha, domin ba su iya shan ruwan Kogin Nilu ba. 25Kwana bakwai cikakku suka wuce bayan Ubanmu ya bugi Kogin Nilu.