Isra'ila Ta Roƙi A Saukaƙa Mata Nauyin Karkiya
Isra'ila ta roƙi Rehobowam ya saukaƙa karkiyar mahaifinsa; ya bi shawarar abokansa ya kuma yi alkawarin kunamai a maimakon haka. Kabilu goma suka tafi suka naɗa Yerobowam sarki — aikin Ubanmu ne kansa — sa'an nan shi ya yi maruƙan zinariya biyu a Betel da Dan don kada kowa ya koma Urushalima.
12 1Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra'ila sun zo Shekem domin su naɗa shi sarki. 2Sa'ad da Yerobowam ɗan Nebat ya ji haka — shi kuwa yana Masar har yanzu, inda ya gudu daga Sarki Sulemanu, ya kuma zauna a can. 3Sai suka aika aka kirawo shi. Yerobowam da dukan taron Isra'ila suka zo suka ce wa Rehobowam, 4“Mahaifinka ya mai da karkiyarmu da wuya. Yanzu ka saukaƙa mana wahalar aiki mai wuya da karkiya mai nauyi da mahaifinka ya ɗora mana, mu kuwa za mu bauta maka.”
5Ya ce musu, “Ku tafi har kwana uku, sa'an nan ku dawo wurina.” Sai mutanen suka tafi.
6Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawan da suka yi wa mahaifinsa Sulemanu hidima tun yana da rai. Ya ce, “Yaya kuke ba ni shawara in amsa wa mutanen nan?”
7Suka amsa suka ce, “In ka bauta wa mutanen nan yau, ka amsa musu da alheri, za su zama bayinka har abada.”
8Amma ya ƙi shawarar dattawan, sai ya nemi shawarar samarin da suka girma tare da shi suke kuma yin masa hidima. 9Ya tambaye su, “Mene ne shawararku? Yaya za mu amsa wa mutanen nan da suka ce mini, ‘Ka saukaƙa mana karkiyar da mahaifinka ya ɗora mana’?”
10Samarin da suka girma tare da shi suka amsa suka ce, “Ga mutanen nan da suka ce maka, ‘Mahaifinka ya mai da karkiyarmu da nauyi, amma kai ka saukaƙa mana ita,’ ka gaya musu haka, ‘Ƙaramin yatsana ya fi kugun mahaifina kauri.’ 11Mahaifina ya ɗora muku karkiya mai nauyi; ni kuwa zan ƙara mata nauyi. Mahaifina ya hore ku da bulala; ni kuwa zan hore ku da kunamai.”
12Bayan kwana uku Yerobowam da dukan mutanen suka dawo wurin Rehobowam, kamar yadda sarki ya ce, “Ku dawo wurina bayan kwana uku.” 13Sarkin ya amsa wa mutanen da kakkausar magana. Ya ƙi shawarar da dattawan suka ba shi, 14ya kuma yi musu magana kamar yadda samarin suka ba da shawara, “Mahaifina ya mai da karkiyarku da nauyi; ni kuwa zan ƙara mata nauyi. Mahaifina ya hore ku da bulala; ni kuwa zan hore ku da kunamai.”
15Saboda haka sarkin bai saurari mutanen ba, gama wannan juyin al'amura daga wurin Ubanmu ne, domin a cika maganar da Ubanmu ya yi ta bakin Ahiya mutumin Shilo wa Yerobowam ɗan Nebat.
16Da dukan Isra'ila suka ga sarki ya ƙi ya saurare su, sai suka amsa masa suka ce, “Wane rabo muke da shi a wurin Dawuda? Ba mu da gādo a wurin ɗan Yesse! Zuwa tentunanku, ya Isra'ila! Yanzu ka lura da gidanka, Dawuda!” Sai Isra'ila suka tafi gida zuwa tentunansu.
17Amma Rehobowam ya ci gaba da mulki a kan Isra'ilawan da suke zaune a garuruwan Yahuda. 18Sarki Rehobowam ya aiki Adoram, wanda yake kula da aikin dole, amma dukan Isra'ila suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sai Sarki Rehobowam ya hanzarta ya hau karusarsa ya gudu zuwa Urushalima. 19Ta haka Isra'ila take cikin tawaye ga gidan Dawuda har yă zuwa yau.
20Da dukan Isra'ila suka ji Yerobowam ya dawo, sai suka kirawo shi zuwa taron suka naɗa shi sarki a kan dukan Isra'ila. Kabilar Yahuda kaɗai ce ta bi gidan Dawuda.
21Da Rehobowam ya isa Urushalima, sai ya tara dukan gidan Yahuda da kabilar Benyamin — zaɓaɓɓun mayaƙa dubu ɗari da tamanin — domin su yaƙi gidan Isra'ila su mai da mulkin ga Rehobowam ɗan Sulemanu.
22Amma maganar Ubanmu ta zo wa Shemaya, mutumin Ubanmu, cewa,
23“Ka gaya wa Rehobowam ɗan Sulemanu, sarkin Yahuda, da dukan gidan Yahuda da na Benyamin, da sauran mutanen, cewa,
24“Ga abin da Ubanmu ya ce, Kada ku haura ku yaƙi 'yan'uwanku, Isra'ilawa. Kowannenku yă koma gida, gama wannan daga wurina ne.” Sai suka yi biyayya ga maganarsa suka koma gida, kamar yadda ya faɗa.
Yerobowam Ya Gina Gumaka a Betel da Dan
25Yerobowam ya gina Shekem a ƙasar tudun Ifraimu, ya kuma zauna a can. Daga nan ya fita ya gina Fenuwel. 26Yerobowam ya yi tunani a zuciyarsa, “Yanzu mulki zai iya komawa ga gidan Dawuda. 27In mutanen nan suka haura domin su miƙa hadaya a gidan Ubanmu da yake Urushalima, zukatansu za su juyo ga ubangijinsu, Rehobowam sarkin Yahuda. Za su kashe ni su koma ga Rehobowam sarkin Yahuda.” 28Bayan ya nemi shawara, sai sarkin ya ƙera 'yan maruƙa biyu na zinariya. Ya ce wa mutanen, “Haurawa zuwa Urushalima ya fi ƙarfinku. Ga allolinku, ya Isra'ila, waɗanda suka fisshe ku daga ƙasar Masar.” 29Ya kafa ɗaya a Betel, ɗayan kuma a Dan. 30Wannan ya zama zunubi, gama mutanen suka riƙa zuwa su yi sujada a gaban ɗaya har zuwa Dan. 31Yerobowam ya gina gidajen tsafi a kan tuddai, ya kuma naɗa firistoci daga kowane irin mutane, waɗanda ba Lawiyawa ba. 32Yerobowam ya kafa wani idi a rana ta goma sha biyar ga watan takwas, kamar idin Yahuda, ya kuma miƙa hadayu a bisa bagadin. Haka ya yi a Betel, yana miƙa hadaya ga 'yan maruƙan da ya ƙera, a can kuma ya naɗa firistoci domin gidajen tsafin da ya gina a kan tuddai. 33A rana ta goma sha biyar ga watan takwas — wata da shi da kansa ya ƙaga — ya haura zuwa bagadin da ya gina a Betel, ya kafa wani idi domin Isra'ilawa, ya kuma haura zuwa bagadin domin ya ƙona turare.