Tsarin Ubanmu domin Aure
Amsa tambayoyin da suka rubuto game da aure: miji da mata kowannensu yana bin ɗayan hakkin jikinsa, kada mai bi ya rabu da abokin aurensa marar bi wanda yake so ya zauna, kuma saboda wahalar wannan lokaci zama yadda kake yana da kyau. Ko yaya yanayinka yake, ka zauna a cikinsa tare da Ubanmu.
7 1To, game da abin da kuka rubuto, cewa, “Yana da kyau mutum kada yă taɓa mace.” 2Amma domin a guji fasikanci, kowane namiji yă kasance da matarsa, kowace mace kuma tă kasance da mijinta. 3Miji yă ba wa matarsa hakkinta, haka kuma mace tă ba wa mijinta nasa. 4Mace ba ta da iko a kan jikinta, sai mijinta; haka kuma miji ba shi da iko a kan jikinsa, sai matarsa. 5Kada ku hana wa juna, sai dai in kun yarda da juna na ɗan lokaci, domin ku himmantu ga addu'a; sa'an nan ku sāke haɗuwa, don kada Shaiɗan yă jarabce ku ta dalilin rashinku na kamun kai. 6Ina faɗin wannan ne a matsayin izini, ba a matsayin umarni ba. 7Ina so dai kowa yă zama kamar yadda nake. Amma kowa yana da baiwarsa daga wurin Ubanmu, wani ta haka, wani kuma ta haka. 8Ga marasa aure da gwauraye kuwa ina gaya musu, yana da kyau a gare su su kasance kamar yadda nake. 9Amma in ba za su iya kamun kai ba, to, su yi aure, gama ya fi kyau a yi aure da a sha azabar sha'awa. 10Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da umarni, ba ni ba, amma Ubangiji, cewa, kada mace tă rabu da mijinta. 11Amma in ta rabu, sai tă kasance babu aure, ko kuwa tă sāke sulhu da mijinta, kuma kada miji yă saki matarsa.
12Ga sauran kuwa ina cewa (ni, ba Ubangiji ba), in wani ɗan'uwa yana da mata marar bi, ita kuma tana yarda tă zauna tare da shi, to, kada yă sake ta. 13In kuma wata mace tana da miji marar bi, shi kuma yana yarda yă zauna tare da ita, to, kada tă saki mijin. 14Gama ana tsarkake miji marar bi ta wurin matarsa, ana kuma tsarkake mace marar bi ta wurin ɗan'uwa. In ba haka ba, da 'ya'yanku marasa tsarki ne, amma yanzu suna da tsarki. 15In kuwa wanda ba mai bi ba ya rabu, to, bari yă rabu; a irin wannan hali, ɗan'uwa ko 'yar'uwa ba a daure shi ba. Ubanmu ya kira ku ga zaman lafiya. 16Yaya za ki sani, ke mace, ko za ki ceci mijinki? Ko kuma yaya za ka sani, kai miji, ko za ka ceci matarka?
17Sai dai kowa yă yi rayuwa yadda Ubangiji ya ba shi rabo, yadda Ubanmu ya kira shi. Haka nake ba da umarni a dukan ikkilisiyoyi. 18An yi wa wani kaciya sa'ad da aka kira shi? Kada yă koma ba kaciya ba. An kira wani babu kaciya? Kada yă yi kaciya. 19Kaciya ba kome ba ce, rashin kaciya kuma ba kome ba ne, amma kiyaye umarnan Ubanmu, shi ne abin da yake da muhimmanci. 20Kowa sai yă kasance a halin da yake ciki sa'ad da aka kira shi. 21An kira ka kana bawa? Kada yă dame ka. Amma in za ka iya samun 'yanci, to, ka yi amfani da shi. 22Gama bawan da aka kira cikin Ubangiji, shi 'yantacce ne na Ubangiji; haka kuma 'yantacce da aka kira, shi bawan Almasihu ne. 23An saye ku da tsada, kada ku zama bayin mutane. 24'Yan'uwa, kowane hali kowa yake ciki sa'ad da aka kira shi, sai yă kasance a nan tare da Ubanmu.
25Game da marasa aure kuwa, ba ni da umarni daga wurin Ubangiji, amma ina ba da shawarata a matsayin wanda jinƙan Ubangiji ya mai da shi amintacce. 26Ina tsammani yana da kyau, saboda wahalar da ake ciki yanzu, mutum yă kasance yadda yake. 27An daure ka ga mata? Kada ka nemi a sake ka. Ba ka da mata? Kada ka nemi mata. 28Amma in ka yi aure, ba ka yi zunubi ba; in kuma budurwa ta yi aure, ba ta yi zunubi ba. Sai dai irin waɗannan mutane za su sha wahala a cikin jiki, ni kuwa ina so in kiyaye ku daga wannan. 29Abin da nake nufi ke nan, 'yan'uwa, lokacin da aka ƙayyade ya ragu. Daga yanzu, bari masu mata su zama kamar ba su da su, 30masu kuka kuma kamar ba su yin kuka, masu farin ciki kuma kamar ba su cikin farin ciki, masu saye kuma kamar ba su da kome, 31masu amfani da duniya kuma kamar ba su shagaltu da ita ba, gama fasalin wannan duniya na yanzu yana shuɗewa.
32Ina so ku rabu da damuwa. Mutumin da ba shi da aure yana lura da al'amuran Ubangiji, yadda zai gamshi Ubangiji. 33Amma mutumin da yake da aure yana lura da al'amuran duniya, yadda zai gamshi matarsa, 34shi kuwa a rarrabe yake. Mace marar aure ko budurwa tana lura da al'amuran Ubangiji, domin tă zama mai tsarki a jiki da ruhu; amma mace mai aure tana lura da al'amuran duniya, yadda za tă gamshi mijinta. 35Ina faɗin wannan ne domin amfaninku, ba domin in sa muku takunkumi ba, sai dai domin halin da ya dace da kuma mai da hankali ga Ubangiji ba tare da shagala ba.
36In wani yana tsammani yana yin abin da bai dace ba ga budurwar da ya yi alkawarin aure, sha'awarsa kuma tana da ƙarfi, ya kuma kamata haka yă faru, to, bari yă yi yadda yake so, bari su yi aure, ba zunubi ba ne. 37Amma duk wanda ya tsaya ƙarƙam a zuciyarsa, ba a tilasta masa ba, yana kuma da iko a kan nufinsa, ya kuma yanke shawara a zuciyarsa yă riƙe budurwarsa, ya yi daidai. 38Saboda haka wanda ya auri budurwarsa ya yi daidai; wanda kuwa bai aure ta ba ya fi yin daidai.
39An daure mace ga mijinta muddin yana da rai; in kuwa ya mutu, tana da 'yanci tă auri duk wanda take so, sai dai cikin Ubangiji kaɗai. 40Amma za tă fi jin daɗi, a ganina, in ta kasance yadda take. Ina kuma tsammani ni ma ina da Ruhun Ubanmu.