Kai Ƙarar 'Yan'uwa Gaban Marasa Bi
Masu bi suna jan juna zuwa kotunan arna — wannan kanta ta riga ta zama kasawa; gara a zalunce ka. Sa'an nan aka gwada take-takensu na 'yanci da zunubin jima'i: jikunansu gaɓoɓin Almasihu ne da haikalin Ruhu, an saye su da tamani, saboda haka ku ɗaukaka Ubanmu cikin jiki.
6 1Sa'ad da waninku yana da gardama da wani, ya kuskura yă kai ƙara gaban marasa adalci domin a yi shari'a, ba gaban mutanen Allah ba? 2Ba ku sani ba cewa tsarkaka za su yi wa duniya shari'a? In za ku yi wa duniya shari'a, ashe ba ku isa ku yanke ƙananan ƙararraki ba? 3Ba ku sani ba cewa za mu yi wa mala'iku shari'a? Balle fa al'amuran wannan rayuwa! 4Saboda haka, in kuna da irin waɗannan gardandami, kukan naɗa waɗanda ba su da wani matsayi a ikkilisiya su zama alƙalai? 5Ina faɗin haka ne domin in kunyata ku. Babu wani mai hikima a cikinku da zai iya yin shari'a tsakanin 'yan'uwa masu bi? 6A maimakon haka, ɗan'uwa yakan kai ɗan'uwansa kotu, har ma a gaban marasa bi! 7Yin ƙararraki da juna shan kashi ne ƙaƙaf gare ku tun farko. Me ya sa ba za ku bari a yi muku zalunci ba? Me ya sa ba za ku bari a cuce ku ba? 8A maimakon haka, ku kanku kukan yi zalunci kuna kuma cuta, har ma ga 'yan'uwanku.
9Ko ba ku sani ba cewa marasa adalci ba za su gāji Mulkin Ubanmu ba? Kada a ruɗe ku: ba masu fasikanci, ba masu bautar gumaka, ba mazinata, ba karuwan maza, ba kuma maza masu kwana da maza, 10ba ɓarayi, ba masu kwaɗayi, ba mashaya, ba masu zagi, ba mazambata, da za su gāji Mulkin Ubanmu ba. 11Haka waɗansunku suka kasance. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, an kuma baratar da ku da sunan Ubangiji Yesu Almasihu da kuma ta Ruhun Ubanmu.
12“Ina da 'yanci in yi kome”—amma ba kome ne yake da amfani ba. “Ina da 'yanci in yi kome”—amma ba zan bar kome yă mallake ni ba. 13“Abinci domin ciki ne, ciki kuma domin abinci”—Ubanmu kuwa zai hallaka dukansu. Amma jiki ba domin fasikanci ba ne—domin Ubangiji ne, Ubangiji kuma domin jiki. 14Ubanmu kuwa, wanda ya tā da Ubangiji, zai tā da mu ma ta ikonsa. 15Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Almasihu ne? To, in ɗauki gaɓoɓin Almasihu in mai da su gaɓoɓin karuwa? Sam, ba zai taɓa yiwuwa ba! 16Ko ba ku sani ba cewa duk wanda ya haɗa kansa da karuwa ya zama jiki ɗaya da ita? Gama Nassi ya ce, “Su biyun za su zama nama ɗaya.” 17Amma duk wanda ya haɗa kansa da Ubangiji, ruhu ɗaya ne da shi.
18Ku guji fasikanci. Kowane irin zunubi da mutum yake yi yana waje da jiki ne, amma mai fasikanci yana yin zunubi a kan jikinsa ne. 19Ko ba ku sani ba cewa jikinku haikalin Ruhu Mai Tsarki ne wanda yake cikinku, wanda kuka samu daga wurin Ubanmu? Ku ba naku ba ne, 20gama an saye ku da tsada. Saboda haka ku ɗaukaka Ubanmu cikin jikinku.