Ƙauna Ta Fi Sani
Masu bi za su iya cin naman da aka miƙa wa gumaka? Gunki ba kome ba ne, kuma akwai Uba ɗaya wanda daga gare shi ne dukan abubuwa suke. Amma sani yakan kumbura mutum yayin da ƙauna take ginawa: idan cinsa zai hallaka ɗan'uwan da Almasihu ya mutu dominsa, Bulus ba zai ƙara cin nama ba har abada.
8 1Game da abincin da aka miƙa wa gumaka: mun san dukanmu muna da sani. Sani yana sa girman kai, amma ƙauna tana ginawa. 2Idan wani yana tsammani ya san wani abu, to tukuna bai sani yadda ya kamata ya sani ba. 3Amma idan wani yana ƙaunar Ubanmu, to Ubanmu ya san shi.
4Game da cin abincin da aka miƙa wa gumaka: mun san gunki ba kome ba ne a duniya, kuma babu wani Uba sai guda. 5Gama ko da akwai abubuwan da ake kira alloli, a sama ko a ƙasa—hakika kuwa akwai “alloli” masu yawa da “iyayengiji” masu yawa. 6Duk da haka a gare mu, akwai Allah guda ɗaya, wato Ubanmu, dukan abubuwa daga gare shi suke kuma muna raye dominsa; akwai kuma Ubangiji guda ɗaya, wato Yesu Almasihu, dukan abubuwa ta wurinsa suke kuma muna raye ta wurinsa. a a v6 A nan Bulus ya jera Uba da Ɗa gefe da gefe: Allah guda ɗaya shi ne Ubanmu, tushen dukan abubuwa, Ubangiji guda ɗaya kuwa shi ne Yesu, wanda ta wurinsa aka halicci dukan abubuwa.
7Amma ba kowa ne yake da wannan sani ba. Waɗansu, waɗanda har yanzu suka saba da gumaka, suna cin wannan abinci kamar an miƙa shi wa gunki da gaske, lamirinsu kuwa mai rauni ya ƙazantu. 8Abinci ba ya kusantar da mu ga Ubanmu. Ba za mu zama a baya ba in ba mu ci ba, ba kuwa za mu zama a gaba ba in mun ci. 9Amma ku yi hankali kada wannan 'yancinku yă zama sanadin tuntuɓe ga masu rauni. 10Idan wani ya gan ka kai mai sani kana ci a cikin haikalin gunki, ashe lamirinsa mai rauni ba zai sami ƙarfin hali yă ci abincin da aka miƙa wa gumaka ba? 11Ta haka saboda saninka, wannan mai rauni ya hallaka—ɗan'uwan nan da Almasihu ya mutu dominsa. 12Sa'ad da kuke yin wannan irin zunubi ga 'yan'uwanku, kuna kuma cutar da lamirinsu mai rauni, kuna yin zunubi ne ga Almasihu. 13Saboda haka, in abinci zai sa ɗan'uwana yă yi tuntuɓe, ba zan ƙara cin nama ba har abada, don kada in sa ɗan'uwana yă yi tuntuɓe.