Ana Neman Sabuwar Sarauniya
Da Bashti ta tafi, aka tattara 'yan mata zuwa gidan matan sarki bisa doka. Mordekai, wanda ya rene 'yar kawunsa marainiya Esta, ya ce mata ta ɓoye cewa ita Bayahudiya ce. Ta sami kambi, kuma aka rubuta labarinsa game da ƙulla kisan sarki a littafin tarihin sarauta.
2 1Bayan haka, sa'ad da fushin Sarki Zerzes ya huce, sai ya tuna da Bashti, da abin da ta yi, da kuma hukuncin da aka yanke mata. 2Sai masu yi wa sarki hidima suka ce, “A nemo wa sarki budurwai kyawawa masu ƙuruciya. 3Sarki yă naɗa shugabanni a kowace lardi ta mulkinsa, domin su tattara kowace budurwa kyakkyawa zuwa katangar birnin Shusha, cikin gidan mata a ƙarƙashin Hegai, bābān sarki mai tsaron mata, su kuma yi musu shirye-shiryen kwalliya. 4Budurwar da ta gamshi sarki, ita ce tă zama sarauniya a maimakon Bashti.” Wannan ya gamshi sarki, sai ya yi haka.
5A katangar birnin Shusha, akwai wani Bayahude mai suna Mordekai, ɗan Yayir, ɗan Shimeyi, ɗan Kish, daga kabilar Benyamin, 6wanda aka kwaso shi daga Urushalima tare da kamammun da aka kwaso tare da Yekoniya sarkin Yahuda, wanda Nebukadnezzar sarkin Babila ya kwashe zuwa bauta. 7Yana renon Hadassa, wato Esta, 'yar baffansa, wadda ba ta da uba ko uwa. Budurwar kuwa kyakkyawa ce da kyakkyawar siffa; sa'ad da mahaifinta da mahaifiyarta suka mutu, sai Mordekai ya ɗauke ta a matsayin 'yarsa.
8Sa'ad da aka ji umarnin sarki da dokarsa, aka kuma tara budurwai da yawa zuwa katangar birnin Shusha a ƙarƙashin kulawar Hegai, sai aka kai Esta ita ma fadar sarki, a ƙarƙashin kulawar Hegai, mai tsaron mata. 9Budurwar ta gamshe shi, ta kuma sami tagomashi a wurinsa, saboda haka ya yi maza ya yi mata shirye-shiryen kwalliya da rabon abinci, ya kuma ba ta zaɓaɓɓun 'yan mata bakwai daga fadar sarki, ya kuma mayar da ita da kuyanginta zuwa wuri mafi kyau na gidan mata. 10Esta ba ta bayyana mutanenta ko danginta ba, domin Mordekai ya umarce ta kada tă yi haka. 11Kowace rana Mordekai yakan yi kai da kawowa a gaban filin gidan mata, domin yă san yadda Esta take da kuma abin da yake faruwa da ita.
12Lokacin kowace budurwa na shiga wurin Sarki Zerzes yakan zo bayan watanni goma sha biyu na shirye-shiryen kwalliya da ake buƙata: wata shida da man mur, wata shida kuma da turare da kayan shafe-shafe. 13Ga yadda kowace budurwa take shiga wurin sarki: duk abin da ta nema, ana ba ta shi domin tă tafi da shi daga gidan mata zuwa fadar sarki. 14Takan shiga da yamma, da safe kuma takan koma gidan mata na biyu a ƙarƙashin Shashgaz, bābān sarki mai tsaron ƙwarƙwarai. Ba za tă sāke komawa wurin sarki ba sai in ya ji daɗinta, ya kuma kira ta da suna.
15Sa'ad da lokacin Esta ya yi na shiga wurin sarki—ita 'yar Abihayil, baffan Mordekai, wanda ya ɗauke ta a matsayin 'yarsa—ba tă nemi kome ba sai abin da Hegai, bābān sarki mai tsaron mata, ya shawarce ta. Esta kuwa ta sami tagomashi a wurin duk wanda ya gan ta.
16Aka kai Esta wurin Sarki Zerzes a fadarsa ta sarauta, a wata na goma, wato watan Tebet, a shekara ta bakwai ta mulkinsa. a a v16 Tebet shi ne wata na goma a kalandar Yahudawa, kusan tsakanin Disamba da Janairu.
17Sarki ya ƙaunaci Esta fiye da dukan sauran mata; ta kuma sami tagomashi da yarda a wurinsa fiye da dukan budurwai. Saboda haka ya sa rawanin sarauta a kanta, ya kuma naɗa ta sarauniya a maimakon Bashti.
18Sarki ya yi babban biki domin dukan shugabanninsa da fadawansa—bikin Esta. Ya kuma yi shelar hutu a larduna, ya ba da kyautai da karimcin sarauta.
19To, sa'ad da aka sāke tara budurwai sau na biyu, Mordekai yana zaune a ƙofar sarki. 20Esta ba ta bayyana mutanenta ko danginta ba, yadda Mordekai ya umarce ta; ta kuma yi masa biyayya kamar yadda take yi sa'ad da yake renonta.
Mordekai Ya Tona Maƙarƙashiya a Kan Sarki
21A kwanakin nan, yayin da Mordekai yake zaune a ƙofar sarki, sai Bigtana da Teresh, bābannin sarki guda biyu masu tsaron ƙofa, suka yi fushi, suka ƙulla maƙarƙashiyar kashe Sarki Zerzes. 22Amma Mordekai ya sami labarin maƙarƙashiyar, sai ya gaya wa Sarauniya Esta, ita kuwa ta sanar da sarki a cikin sunan Mordekai. 23Aka bincika al'amarin, aka tabbatar gaskiya ne, sai aka rataye su biyun a kan gungume. Aka kuma rubuta wannan a cikin littafin tarihi a gaban sarki.