Bulus Ya Fuskanci Tuhume-tuhume a Gaban Festus
Sabon gwamna ya gaji ƙarar, sai tsohon shirin yi masa kwanto ya dawo. Maimakon a aika shi Urushalima, Bulus ya ɗaukaka ƙara zuwa wurin Kaisar, Festas kuma ya amince. A asirce Festas ya yarda cewa jayayyar game da wani mataccen mutum ce mai suna Yesu wanda Bulus ya nace yana da rai.
25 1Bayan Festus ya iso lardin kwana uku, sai ya haura zuwa Urushalima daga Kaisariya. 2A can manyan firistoci da shugabannin Yahudawa suka kawo ƙararsu a kan Bulus, suka yi ta roƙonsa, 3suna neman a yi musu alheri a kansa—wato yă kirawo Bulus zuwa Urushalima. Sun kuwa yi kwanton ɓauna domin su kashe shi a kan hanya. 4Festus ya amsa cewa ana tsare Bulus a Kaisariya, shi kuma ba da daɗewa ba zai tafi can. 5“Saboda haka,” ya ce, “bari waɗanda suke da iko a cikinku su gangara tare da ni su kuma kawo ƙara a kan mutumin, in har akwai wani laifi a gare shi.”
6Festus bai kwana da su fiye da kwana takwas ko goma ba, sa'an nan ya gangara zuwa Kaisariya. Kashegari sai ya zauna a kujerar shari'a, ya umarta a kawo Bulus. 7Da Bulus ya iso, sai Yahudawan da suka zo daga Urushalima suka kewaye shi, suna kawo tuhume-tuhume masu yawa da masu nauyi waɗanda ba su iya tabbatarwa ba. 8Bulus ya amsa don kāre kansa ya ce, “Ban yi wani laifi ba, ko ga shari'ar Yahudawa, ko ga haikali, ko kuma ga Kaisar.”
9Amma Festus, saboda yana so yă gamshi Yahudawa, sai ya tambayi Bulus ya ce, “Ko za ka yarda ka haura zuwa Urushalima a yi maka shari'a a can a gabana a kan waɗannan tuhume-tuhume?”
10Bulus ya ce, “A gaban kujerar shari'ar Kaisar nake tsaye, inda ya kamata a yi mini shari'a. Ban yi wa Yahudawa wani laifi ba, kamar yadda kai kanka ka sani sarai. 11In har na yi laifi, na yi wani abin da ya cancanci mutuwa, ba zan ƙi mutuwa ba. Amma in tuhume-tuhumen da waɗannan mutane suke yi mini ba su da tushe, ba mai iya ba da ni gare su. Ina ɗaukaka ƙara zuwa ga Kaisar.”
12Bayan ya tattauna da majalisarsa, sai Festus ya amsa ya ce, “Ka ɗaukaka ƙara zuwa ga Kaisar; to, zuwa ga Kaisar za ka tafi.”
13Bayan kwanaki kaɗan, sai Sarki Agaribas da Barniki suka zo Kaisariya, suka gai da Festus. 14Da yake sun jima kwanaki da yawa a can, sai Festus ya kawo batun Bulus a gaban sarki ya ce, “Akwai wani mutum da Felis ya bar shi a nan a tsare. 15Sa'ad da nake Urushalima, sai manyan firistoci da dattawan Yahudawa suka kawo ƙara a kansa, suna neman in yanke masa hukunci. 16Na gaya musu ba al'adar Romawa ba ce a ba da wani kafin wanda ake tuhuma yă fuskanci masu tuhumarsa ido da ido, yă kuma sami zarafin kāre kansa game da ƙarar. 17Saboda haka da suka taru a nan, ban yi wani jinkiri ba—kashegari na zauna a kujerar shari'a, na umarta a kawo mutumin. 18Da masu tuhumarsa suka tashi tsaye, ba su kawo ko ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen laifuka da nake tsammani ba. 19A maimakon haka, suna da waɗansu gardama da shi game da addininsu da kuma wani mamaci mai suna Yesu, wanda Bulus ya ci gaba da cewa yana da rai. 20Da yake ban san yadda zan bincika wannan ba, sai na tambaye shi ko yana so yă tafi Urushalima a yi masa shari'a a can a kan waɗannan tuhume-tuhume. 21Amma da yake Bulus ya ɗaukaka ƙara a ci gaba da tsare shi don a jira hukuncin Sarkin sarakuna, sai na umarta a tsare shi har sai da zan iya aika shi wurin Kaisar.”
22Sai Agaribas ya ce wa Festus, “Ni ma ina so in ji mutumin da kaina.” Festus ya ce, “Gobe za ka ji shi.”
Bulus Ya Tsaya a Gaban Agaribas da Barniki
23Kashegari sai Agaribas da Barniki suka zo da irin ɗaukaka mai girma, suka shiga babban ɗakin tare da shugabannin soja da kuma manyan mutanen birnin. A kan umarnin Festus, sai aka kawo Bulus. 24Festus ya ce, “Sarki Agaribas, da dukanku da kuke nan tare da mu—ga mutumin nan da kuke gani. Dukan jama'ar Yahudawa sun kawo mini ƙara game da shi, a Urushalima da kuma a nan, suna ihu cewa bai kamata yă ƙara rayuwa ba. 25Amma da yake ban sami wani abin da ya cancanci mutuwa a gare shi ba, shi kuma da kansa ya ɗaukaka ƙara zuwa ga Sarkin sarakuna, sai na yanke shawara in aika shi. 26Ba ni da wani tabbataccen abin da zan rubuta wa ubangijina game da shi, saboda haka na kawo shi a gabanku duka, musamman ma a gabanka, Sarki Agaribas, domin bayan wannan bincike in sami abin da zan rubuta. 27Gama a ganina bai dace ba a aika da wani ɗan sarƙa ba tare da an nuna tuhume-tuhumen da ake yi masa ba.”